← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 70 OF 121

chapter 73

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Yayi shiru daga bisani yace khadija tace na am Yayana " yace kinsan bazanso abunda zai cutardake bako??? Tagyada kanta yanisa tundakike bakisan labarin mahaifiyar muba

Babu Wanda tasanar mawa kisani bayanni kinada wani yayan"" dasauri tadago tace Yaya kuma a ina?? Yanisa mu uku mahaifiyar mu tahaifa

Nima naji wannan ne lokacinda zamubar garin mahaifinmu tanasanarda wani malami alokacin ban fuskanci labarin sosaiba bayan nagirma nasake komawa yola

Da mamaki takalleshi duk da inayaro banwani sha wahalar gane gidansaba Amman da tambaya da yake malamine sainayi dace tunda nasan unguwar awajen gwaggo hasana na tambaya

Nasameshi yatsufa sosai baima ganeniba saida nayimasa bayani yanisa kwana na daya agarin hargidan mahaifinnawa natafi Amman baigane niba

Naso sosai nasan inda Dan uwana yake duk Wanda natambaya saiyace babu faruq agidan malamin shine yasanardani labarinda mahaifiyarmu tasanar dashi

Yanisa anan yakwashe komai yafada mata"" duk irin wahalarda tasha dayanda malamin yacemasa asirine akai mata komai baiboye mataba

Yanakai karshen labarin khadija tafasheda kuka baiyi kokarin hanataba saida tayi mai isarta dankanta tashare hawayenta

Yace wannan dalilinne yasaka banaso ki auri maimata Dan bazanso kema hakan tafaru dakeba"" khadija tadago jajayen idanunta takalleshi tace nagane Yayana Amman inaso kasani babu Wanda zaiwuce kaddararsa

Kataba tunanin za ahaifeni???? Duk da kiyayyarda mahaifinmu yakeyiwa mamana dayake akwai rabon saina shigo duniya gashi anhaifeni

Ya muktar kaddarata rubutacciyace bakada ikon sauyata inhar Allah yarubuto nima zansha wahala babu makawa hanawarka bazai kareni dakomaiba""

Kataba tunanin zan iya auren marar matar dagabaya yasake aurowata wacce zatayi nasanin fitana gidan??? Shifa Allah ba aimasa wayo baka isah ka karkare abunda yake arubuceba tunfil azal

Baikamata kayiwa kowacce mace kallon hakaba Dan idanharkayi tonima wani mai irin hangenka dawannan zai kalleni

Kasani ba arasa nakwarai acikin al ummah komai lalacewar zamani zakasamu akwai nagartattuñ mutane acikinsu

Tanisa abunda kawai yakamata kayi kace Allah yakare maka kanwarka daga fadawa hannun irin wadan nan azzaluman matan"" kuma kabawa kanwarka makami wato ilimin Islam Wanda kowayake takama dashi

Dashi zata iyah kare kanta Allah yashiga tsakaninta damiyagun mutane kumani bana zargin mom wlh baruwanta halinsu daya da labila

Idanhar tanada wani mugun hali da awajen yarta zamugani Dan duk Wanda yatsotsi nono bazai yarba kamar yanda naji anafada

Nikuwa nace wannan zancen burr ne inji tusa saunawa uwa take haihuwar Yaya Amman babu Wanda yagadota wani lokacin maishegen fada saita haifi salihar yarinya

Wani lokacin saliha saita haifi masifaffiya danhaka masucewa waisu bazasu auri yayan masifaffuba bawai halin uwar zaku dubaba nayar dankowa da halinsa

Muktar yanisa yana kallon agogon hannunsa yace dare yayi kikwanta kihuta"" kai tagyadamasa tace nagode kaima kasamu kakwanta nasan jiya bakai barciba

Murmushi yasaki maidan sautii yace ya akai kikasan banyi barciba??? Itama murmushin tayi tace gashinan inagani a idanuwanka

Yamike yadauko mata maganinta yace aikece kikajamun kinfita kina kuka badole hankalina yatashiba""" tace ayimun afuwa duk laifin nan dai nawane baice komaiba yabata maganin tasha yayi mata saida safe yakoma dakinsa yadade yaana nazarin maganganunta kafin yayi alwala yana sanarda Allah yazabawa kanwarsa abunda yafizama alkhairi arayuwarta
Washe gari dasafe yana dakinta zaune suna firah saiga wayarta tasoma ringing jikinta yasoma rawa dantasan shine jiya silent tasaka wayar bayan fitar muktar tadauko wajen miss call ashirin tayi mamaki sosai"" saitacireta silent saiyanzu gashi yakirah

Tanakallon wayar tana kallon yayanta yalurah da itah saiyashare yace wayar waye take ringing tsuru tayi alamun rashin gaskiya tace dama dama wayar sahibace tamanta da itah

Dakagan yanda take magana. Kasan batada gaskiya yayi murmushi yace tokidauka kice batakusa dawayar mana"" tadan sosa kanta tace ah ah kawai barta idan yagaji zaidaina kirah kowaye

Wayar hartakatse akasake kirah muktar yamika hannu yadauko wayar yaduba hubbina yaga anrubuta yadaga ido yakalleta saita done kanta yace kinganima inaganin kamar saurayintane yake kirah

Shirudai tayi batace komaiba hartakusa katsewa yadauka tareda sallama dayan bangaren aka amsa "" yace barka dasafiya yace yauwa Dan Allah Khadija nake nema

Muktar yadaga kai sukasake yin ido hudu tasosa kanta kamar wacce zatayi kuka"" yace togata nan tafe yakashe wayar baiko kalletaba yafita rike dawayar

Jikin khadija Yakama rawa tace yaunabani mekuma yakawoshi yanxu??? Saileken kofa takeyi""
Muktar da murmushi kwance afuskarsa yakarasa wajenda Usman yake tundaga nesa yaga matukar kamarda sukeyi da labila kuma tamkarma bai isah haihuwartaba""

Shima yana ganinsa yasaki fara a kafin yakawo inda yake haryasameshi yabashiy hannu suka gaisa "" daganan suka karasa kusa da motarsa

Suka sake gaisawa yace yan america saukar yaushe bayan malam yacemun bakanan"" sosai Usman yayiwa muktar kwarjini a ido Sam yakasa daga idonsa sama yakalleshi""

Yace shekaranjiya nazo"" yace toya hanya inafatar dai lafiya?? Yace ah lafiya kawune yakirani yasanardani sakonka

Usman yatari nunfashinsa yace Allah yasadai yayan namu ya amince"??? Wata kunyace ta sake kama muktar yace ah gaskiya lokacinda naji Sam banyi Na am ba dalilinda yasaka nataso aranar kenan

Nazone daniyar natafi da itah dankawai nace banyardaba saiyarinya tazubemun balafiya jiyama saida tasha allurah Usman yace subhanalillahi yayanmu meyasa zakaimana haka

Muktar yace dad inada nawa dalilin saboda nayi alkawarin Kanwata bazata auri Wanda yakeda mataba saboda shine silar dayasa mukarasa mahaifiyar mu yanisa

Amman sapna tayimun gamsasshen bayani kuma nayarda dahakan yanzu danaganka yasake nisawa yadago yakalli Usman kamar zaiyi kuka yace wlh inason Kanwata sosai itace kawai take debemun kewar mahaifiyarmu

Banaso tashiga tashin hankali da matsatsin rayuwa" yasanne kansa nidama banda natauyemata hakkinta bazantaba bari tayi aureba

Danba zanso wani yacutarda itaba"" Usman yamurmusa yadafa kafadarsa yace nagane abunda kakenufi kuma nagamsu nayimaka alkawarin babu abunda zaisameta inasonta sosai bawai son wasaba dasanina kaima kasan bazantaba bari wani yacutarda itah ba

Muktar yanisa shikenan Allah yazaba mana abunda yafizama alkhairi usman yace Ameen"" muktar yace bari nakiramaka itah

Yayi maganar yanashirin juyawa Usman yasake basa hannu suka gaisa sannan yawuce aransa yanacewa ashedai baban labila haka yake bashida girman kai""

Usman kanshi yaga saukin kan muktar"" yanashiga gidan innah tace wai inakaje naga khadija sai tsautsauniya take"" murmushi yayi yace innah dadyn labila ne yazo"" yayi maganar yana shiga dakin yace kishirya yana jiranki ya ajemata wayar akan dago harzaifita tace Yayana tsayawa yayi batareda yajiyoba tace nidai banason fita bakafadamashi gobe zamutafi dakaiba

Adarare takeyin maganar yajuyo dafuskarsa wajenta dauke da murmushi yace inazanje dake kiyitamun kuka ainalurah soyayyarku hartayi nisako

Tace wlh ah ah ya muktar yace hakane shiyasa naga kinyi serving din numbersa da hubbina

Kafin tace wlh banice nasaba yace karkibata masa lokaci yanajiranki Amman karkidade yawuce abunsa"" murmushi tayi mayafinta kawai tadauko tasaka tasa talkamanta tafito tana leke waiko zataga ya muktar innakuwa sai dariya takemata

Tafito dasauri tafita"" tunda yahangota yasoma aikomata dawani kyakkyawan murmushi Wanda itakanta bazata iyah daukarsaba akarancin shekarunta jitayima kamar kafafuwanta suna hardemata tuni tasanne kanta kasa


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 70 · 0% Book details