← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 17 OF 121

chapter 20

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Jikinta sairawa yakeyi tanatsaye takasayin komai jira kawai takeyi taji yakushin berayen domin tunda take aduniya bata taba ganin beranda yayi girman koda Dan kaza ba banlantana kuma akuya

Shiru taji tsayin mintuna ahankali tasoma bude idonta bataga komaiba tawaiga ko ina bakomai ahankali tasaukarda karamar ajiyar zuciya"" tayiyu bakomai bane kawai kallonda tayi dazune kaset din horo shine takejin tsoro"""

Batareda wani kokonton tunanin taba takarasa dakin kawaidai saitaji jikinta yayimata ba dadi"" fitowa tayi takoma bangaren Usman tayi wanka tayi sallah""" sannan tayi kwalliya duk da bawata kwalliyace tayiba Dan jikinta jitakeyi tamkar anlikidamata shegen duka""

Bayan tagama shiryawa cikin kananun kaya Riga da sket""" masu karamin hannu"" tadauko Karamin hijab fari tasaka"" yar karamar fuskarta tafito tayimata kyau"" saukowa tayi kasa wajenda tabar"" kaleed""

Yana zaune kasa kusa dashi wadansu kadan karune manya"" masu katon kai kowanne daya girmansa yakai girman tsarii idanuwansa jajir tamkardai nawadan cen berayen""" cikin daga murya tace kaleed bar wajen nan""" tanarufe baki wadan nan manyan kadangarun suka soma keta wata muguwar dariyaa "" wacce ta karade dukan falon"" shikuwa kaleed sam baijitaba saiwasa yakeyi dasu yana dariya""" jikin ameena yasoma bariii tasoma ja baya ganin suna nufo inda take "" daidai shigowar Usman"" aidagudu taruga tafada jikinsa taboye fuskarta""

Cikin firgici yayarda jakar hannunsa yana tambayarta lafiya meenal?? Menene yafaru"" dahannunta ta nunamasa wajen kaleed shikuwa kaleed maganar babansa ce tasaka yadago kansa dasauri yadauko Dan kadan garensa naroba mai batir yarugo yana oyoyo papa"" jikin mahaifinsa yashige Usman yashafo kansa da hannu guda

Sannan yamaida kallonsa wajen ameena yace please meenal kidago kikalleni nigabadaya kintayarmun da hankali""

Shiru yaji batace komaiba yasake girgizata saiyaga ta langwabe dasauri yature kaleed gefe yadagota illaikuwa AMEENA tadade dasomewa""" Cikin sauri yakarasa jikin kujerah ya kwantarda itah"" dasauri yadebo ruwa yazo yaballe murfin robar yasoma yayyafamata""

Tasaukarda ajiyar zuciya ahankali tabude idonta zunbur tamike tasake kankameshi tafashe dakuka """ jikinsa yajawota murya araunane yace waimenene meenal Dan Allah kisanardani kinsan halinda zanshiga idan inaganin kukanki???

Har abada bazanso kizubarda hawayeba muddin inaraye Dan Allah kidaure kisanarsani menene dalilin kukanki ???
Cikin muryar kuka tace Yaya kadangaru naketa gani masu magana"" akusa da kaleed

Usman yakalli kaleed shima kaleed din shiyake kallo Wanda tunda mamarsa tafadi yakuramasu ido yana makale da kadan garensa naroba

Usman yayi murmushi yace meenal kadangaren robar kikewa kuka?? Inakin saba ganinshi dashi sai alokacin tadago daga jikin Usman cikin tsoro tsoro takalli kadangaren

Tsayin mintuna tamaida kallonta wajen Usman tace wadanda naganifa manyane kuma suna dariya"" kaleed yayi charab yace mom nan ake karamasu gilma"" yamatsa wata yar kunama saigashi yayi tsayi yanadaga kansa tamkar kadangaren gaske"""

Usman yace tokingani dama bakisan haka yakeba"" idan tsoronsa kikeji kibari na konashi damacen kece kikasiyomasa danni banason ire iren wadan nan

Dakinsa duka kincikashi da Teddy waiduk kayan wasane bakisan gunki bane kike ajewa badole saida wadan nan zaiyi wasaba kwanaki inaganifa harda macijin roba kika siyomasa"""

Ameena tasaukarda gajeruwar ajiyar zuciya tace wlh natsorata Yayana"" tashi muje kayi wanka kakwaso gajiya"" karan hancinta yalakuta yace bayan kintayarmun da hankali

Ninadaukama nine na aikatamaki wani gungumen laifii harna tanadi kalar hukuncinda zanyiwa kaina"""

Murmushi tasake taboye fuskarta cikin jikinshi tace rufamun asiri wanne laifi zakamun nikuwa aduniya Wanda zaisakani kuka"?? Nayi kuka lokacinda nake marainiya tunranarda na aureka bakinciki baisake tunkaroniba Wanda zaisa kabatamun rai hartakaini gayinkuka

Inaji araina nagamayin kukan bakinciki aduniya Allah yasharemun hawayena yahadani da nagartaccen namiji Wanda kowacce mace zatayi gurin samun abokin rayuwa kamarka

Ina mai addua kowacce mace tasamu miji mai kwatankwacin halayenka""" ido yakwalo yace daina zigani hakamana

Kinsa nafarajina asama ina shawagiii karkisa kaina yafasu dayawa""
Tayi dariya gaskiya nafada baban kaleed Dari bisa daribakada makusa duka dabi unka irinna nagartattun mutanene

Yaja hancinta yace kamaryanda kike nagartacciya ba kisani nayarda dakefiye dayandà nayarda dakaina kyawawan halayenki sune sukesakani karasonki

Babu shakka ke yar ajannace"" cikin zolaya tace idan kadagamuñ kafarkaba""" yayi dariya yace aituni nadage kafar wlh meenal da aljanna ahannuna take dakuwa kullum sainabaki itah sama dasau goma

Murmushi tayi tamike dagajikinsa yadago yana kallonta zaiyimagana tadorah Dan yatsanta saman labbansà tace ka Adana kalamanka. Harsaimun kwanta yanzu katashi muje kayi wanka kaci abinci kafin nan lokacin sallah yayi saikaje masallaci
.
Yamike yana murmushi yace tomuje Amarya dariya tasaki tajindàdin sunanda yakirata dashi sosai tanajin dadin yakiratà dasuñan

Tayigaba yanabayanta zuwa bangarensa tahadamasà ruwan wanka wadanda sukasha turareñ wanka masu kamshi

Tataimaka masa yarage kayan jikinsa yashiga toilet din"" tarufemasa kofa yana zolayarta waibazata tayashi wankanba saboda yadebo gajiya


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 17 · 0% Book details