← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 117 OF 121

Chapter 016

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Idanuwanta biyu har akayi kiran asuba tanaji Usman yana buga mata kofa tatashi tayi sallah "" tacemasa to mikewa tayi takunna wutar dakin ganin kurajen minini ajikinta tasoma binsu dakallo "" gabanta yana faduwa dole takoma wajen bokan nan tunkafin abun nan yayi nisa yakareshi ""

Nikam nace kinmanta kincemasa Wanda bayida makari sai mutuwa?? Dama ance idan zakagina ramin mugunta kaginashi gajere dankoda kai kafada zaiyimaka saukin fita

Wanka tasakeyi saboda kaikayin tasaka kaya masudan tsayi duka sunrufemata jiki tayanda babu Wanda zaiganie

Karamin hijab tasaka saboda wadanda suke awuyanta"" tana zaune sai sake sake takeyi har haske yafito Usman ne yashigo dakin da sallama ta amsa tana dago kanta

Kusa da itah yazauna race masà inakwana" yace lafiya qalau kintashi lafiya?? Aranta tace bakalauba shegiyar matarka tanason ganin bayana"" 🙄

Afili kuma tace qalau saidai kewarka"" murmushi yasaki cikin jindadi yace kitaso mukarya Dan khadija Niger zataje wajen dangin mahaifiyarta"

Tace waidama ita Yar Niger ce??? Yace ah kishiryamun kayana kafin nakaita airport Dan nima tafiyace takamanie mutanenda nafadamaki sunzo company jiya tosune sukahada mana zama a America akalla zanyi sati acen

Lubabatu tace shikenan suka tashi suka sauka kasa sunsamu su khadija harsun soma karyawa tazuba masu sannan tacigaba daci

Duk da zumudi baibarta taci dayawaba"" tana gamawa labila tatayata suka dauko kayan labila taso tabita suje tare Amman gobe zasufara jarabawa shiyasa kawai bazata bitaba harbakin mota lubabatu tarakasu tanayiwa su anwar adawo lafiya

Abunda zaibaku mamaki su anwar basayarda lubabatu tadaukesu dazaran tadaukesu saisukama ihu dole sai an karbesu hakan yasakama tadaina daukarsu

Khadija tace shegiyar kiuya kamar wadanda akexizo lubabatu saidai tace hmm kawai saida motarsu tabar gidan sannan takoma cikin gida
.

Sunje adaidai kuwa suna isah akagama komai khadija takude jirgi su labila sunatsaye hargirjinsu yadaga nikam nace khadija dakarfin hali yara uku kuma babu mairike mata kodaya

Amman tunda tasaka ranta datafiyar aisaitayi tanason ganin kaleed ne sosai ""
Karfe biyu jirginsu yasauka" Niger tana saukowa tasoma kalle kalle inama zataga mutumen jitayi anyimata sallama"" ta amsa dafara a yace madam nine Wanda akace zankaiki gidan

Tace okay anwar dayake hannunta nadama yakarba"" tanagoye da sapna husna kuma tana rike gahannunta nahagu motarsa yabude tashiga yasaka Kayanta bayan motar tareyake dawani da alamu driver sane sukashiga motar yatayar

Sukahau hanya"" sunatafiya khadija kam sai kalle kalle takeyi " harsuka kaigidan sarautar mutumen yace wajenwa kikazo???

Tace sunanta Hauwa u yace shikenan fita yayi yayiwa maidagin bayani akasheka akasanarda sarki yanada baki daga Nigeria sunzo wajen hajiya babbane""

Yace ayisauri ashigo dasu nantake fadawa sukayimasu iso sarkin Wanda yake kan kagarar dazaran kadubeshi kaga khadija saikace shine yahaifeta dankamar tasuma tabaci yana ganinta yamike yasaki fara a

Yanayimata lale marhabin"" anwar yakarba yana kallo yacewa fadawa yau manyan bakine dasu danhaka zaigana da bakinsa kaitsaye cikin gidan yawuce dasu wajen matansa sukuma wadanda suka rakota yace akaisu falon baki akarramasu

Sosai khadija tashiga mamaki ya akai yasanda zuwanta babban gidan sarautar cike yake damanyan ginuka ko ina Kaduba bayine gasunan sunata aiyuka

Kaitsaye turakar Fulani yanufa itace uwargida "" itama tanaganinsu tatashi daga kishin gidenda take tace wanakegani kamar khadija??

Maimartaba yakalleta da murmushi akan fuskarsa yace itace ina hajiya?? Tace yanzun nan takoma bangarenta saimuje cen kawai tamike ta umurci sauran bayin dasu sanarda Amarya gabadaya suka rankaya dakin hajiya

Duka yaran khadijar andaukesu anwar yana hannun mai martaba husna tana hannun Fulani sapna Amarya takarbeta

Ita haryanzu mamakine kwance akan fuskarta sunashiga tayi arba da dattijuwar data taimaka mata lokacinda take nakudarsu Husaini

Itama tana ganinta tasaki fara a"" dasauri khadija taruga tarungumeta saikuma tafashe dakuka"" tashafa bayanta tace menene nakuka aikindawo cikin yan uwanki

Cikin kuka tace dama Ashe kece kikahaifi mamana meyasa bakifadamun hakanba lokacinda muke cikin dajin zaune???

Tadago da itah tana murmushi tace khadija kenan ba maimunatu tasanardakeba abunda yasaka banfadamakiba nasan idan kikaji zakiji haushina saboda duk nice silar shigarku wannan damuwar

Saiga hawaye sunabin fuskarta Fulani da mai martaba suka zauna tareda Amarya""

Khadija tasharemata hawaye tana girgiza kai tace kokadan bakece silar damuwar muba kowa naduniya bayawuce kaddararsa

Kaddararmuce tazo dahakan"" Hauwa u tafashe dakuka tace inada laifi sosai gashi asanadin rashin bin iyayena nayisanadin da yata Tarasa ranta bazantaba gafartawa kainaba wannan bakincikin dashinake kwana naketashi

Najamaki gashike bakisan dadin uwaba kowayanaso yatashi tareda mahaifiyarsa itah tarayu babuni kekuma kinrayu babu itah mezaisa bazanyi kukaba kaichoni hauwa

Nina San har abada bazandaina kukan nanba"" khadija tace dangirman Allah kidaina cewa hakan babufa Wanda ya isah yakaucewa kaddararsa


Kinmanta da Allah yadauke ummana yabarmun Yayana Wanda yakesona fiyedakomai yazamemun uwa uba

Bantaba kukan maraiciba harnakanji araina abunda yakemun komai uwama bazata samu hakanba

Yayimun abunda babu Wanda zaiyimun sannan Allah yahadanie da labila wacce takesona fiyeda kanta ""saikuma yasake hadani da Miji nagari"maisona duk wannan gatane da""Allah yayimun"aiwan nan kadai ya isah ingodemasa "" Hauwa ta share hawayenta tace hakane Amman nikam inaji ajikina bankyautaba gashi naja kinrabuda yayanki yan kananu lokacinda yadace kirungumesu sunyi nisa dake

Khadija tayi dariya tace kuma Allah saiyasake bani wasu tayi maganar tana kallonsu anwar sai lokacin Hauwa tagansu daibayan daya take kallonsu baki bude tace yara uku kikasake Haifa??

Kai masha Allah "" Allah abun godiya mikomunshi Muhammad inganie tayi maganar tana kallon mai martaba yatashi yakarasa gabanta yaduka sannan yamika mata

Tace barakallah kyakkyawa dashi shiru tayi tace kuganemun nikuwa kamar nasan maiwan nan fuskar??? Fulani tace nikaina hakan nakerayawa araina

Maimartaba yace narigaku azuciya tunsanda sukashigo naraya hakan" Amarya tace waiku bakugane dawa yake kamaba?? Ai ina ganinsa naga kamannin sultan""

Maimaitaba yace wanne sultan din??? Tace nagidan Yaya Husaini mana"" Hauwa tace hakane Kuwa wlh sunyi kama da kaleed ikon Allah kunga yanda akeyin kama

Khadija tana saurarensu saiyanzu tayi magana tace aidole suyi kama mana tunda kaninsane"babansu daya

Gabadaya suka kalleta da mamaki sukace taya zasuzama uba daya kuma bayan ba ubansu dayaba???

Khadija Tanisa tace abunda yakawoni kasar nan kenan akan maganar kaleed din tanisa mahaifin kaleed shine mijinda nake aure

Idanuwanta suka kawo kwalla tacigaba matar uba wacce takeneman ganin bayana itace tarabashi da mahaifiyarsa aka kasheta sannan shima tasaka akasheshi saita fashe dakuka

Tundanake arayuwata bantaba ganin mace marar imaniba irin lubabatu gabadaya jikinsu yayi sanyi tasoma basu labari duk yanda aljana maimunatu tasanarda itah


Aisha✍🏼
[3/30, 6:14 AM] YAYA HAYAT: ☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 117 · 0% Book details