← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 53 OF 121

Chapter 56

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Kasace mata komai yayi saboda kunyarda yaji"" mikewa tayi kawai tana murmushi tawuce abunta""

Bangaren khadija kuwa tanashiga daki tafada akan gado tadafe saitin zuciyarta inda yake harbawa tamkar kirjinta ne zaifaso zuciyar tafito

Tanacewa لاهولاولاقوت الابل لله kasa samun natsuwa tayi duk da jero adduarda takeyi bataji wani sauyiba azuciyarta "" tagumi tayi yayinda tashiga wata duniyar daban murmushi tasaki afili batasan sanda bakinta yafurta gaskiya kyakkyawane

Daidai shigowar labila tace baban nawa?? Kunyace takama khadija tace nifa badawata manufa nafadaba ina nufin yanada kyau Ashe shikika biyo ba ummaba"""

Nantake annurin fuskar labila yagushe"" khadija talurah dahakan tace meyafaru sahiba??? Kodai bakiji dadin abunda nafadabane???

Labila tace bakomai kawaidai naji raina yabacine!!! Tatari nunfashinta dakikaji na ambaci umma ko???

Waime yasaka kullum naketa jankunnenki akan muhimmancin umma agareki?? Tanisa kodayake tunda kinada itah araye bazaki gane mahimmancinta ba saikin rasata

Labila tace sahiba kenan wlh dama nice ke dama tun wajen haihuwana tamutu"" khadija tayi saurin rufemata baki tace a uzubillahi Allahumma izna min hazal kalamiki"" kinkuwasan mekike fada???

Kinaso yayanki sucemaki hakan"" wasu hawayen takaici tashare tace inhar banzama nagartacciyar uwaba bazanga laifinsuba koda jifana sukai da dutse

Khadija tadafata tace kome kikeji agameda ummah hakuri zakiyi itace dai mahaifiyarki kuma kinsan babu Wanda zai karkare hakan

Labila tanisa tace babban takaicina kenan danashigo cikin tsatsonta inama ace babana ba itah ya auraba har aka haifeni

Khadija tabata fuska tace sahiba waime yasakike hakane kin isah kisauya hukuncin Allah ne"" kisani kowa dakikagani aduniya bai isah yagoge kaddarar saba

Ballanata ummah batada wata makusa kawaidai dankina yarfarine yasa batajanki ajikinta tokuma bakece kawai akayiwa hakanba kigaggauta Neman tuba awajen Allah

Tashare hawayenta tana maineman yafiya awajen Allah astagfirullah wa atubu ilaihi"" aranta kuwa tana mamaki yanda take kasa sanarda wani damuwarta

Khadija ce tajawo hannunta tafada saman gadon"" tace kiyi hakuri kinji sahibata wlh banason inaganin damuwa atare dake kwata kwata kasa samun sukuni nakeyi

Labila tayi murmushi nadaina sahiba kinga ya muktar fa yana jiranki muje narakaki indawo wajen dad

Tace to tareda mikewa "" aranta tanata addua Allah yasa bayacikin falon labila tanagaba tana binta baya

Yana nan kamardai yanda sukabarshi Amman yadorah kafarsa daya akan dayaa sabanin dazun dayake danna waya yanzu idanuwansa kyam sunakan kofardasu labila suka shiga

Suna fitowa yatada kansa zuwa fuskarta take idanuwansu suka sarke cikin najuna dasauri khadija tasaki likaf yakarasa rufemata yan idanuwanta dama sune kawai abude

Wani iri yaji aransa kardai yarinyar nan tagano itah nake kallo??

Muryanta yaji tanacewa dady sai anjima""" yadago ahankali yakuramata ido saikuma yasaki murmushi yace to Khady kigaida gida" taresuka fita da labila yarakasu da ido

Khadija kafarta har sassarfa takeyi"" sunafita Usman yadafe kansa yace ya salam meyake shirin faruwa dani wannan wane irin abun kunyane zuciyata takeson kaini gareshi kawar yata!! Yayi saurin kawarda tunanin aransa tunkafin yasamu matsuguni

Wayarsa yadauko yakunna kira a yadorah akan kunnensa yadan kishingida saman kujerar babu jimawa barci yadaukeshi awajen

Hajiya yaji tana tashinsa yatashi yayi sallar la asar gashicen anyi kirah mikewa yayi tareda mika yawuce zuwa dakinsa dayake gidan

Yana nan tsaf dashi tamkar akwai mutum aciki toilet yashiga yawatsa ruwa sannan yadauro alwala yawuce masallaci acen yahadu da Hafiz

Bayan sundawo ahanya yake masa maganar yaushe zaikoma america yace wani sati ainakusa gamawa inhuta yawon nan basonsa nakeyiba

Usman yace Allah yataimaka aini namatsu kagama in hannan tamaku dukiyarku"" Hafiz yace habadai Yaya niba fa kasuwanci zanyiba aikin gamnati zanyi
Kawaidai kacigaba dakula dasu

Yana dariya yayi maganar Usman yace naki wayon nauyi yayimun yawa akaina bazaku ragemunba"" Hafiz yace aigirman Kane""Kaine fa babanmu dole kakarbi girman"" Usman yace naji waikai yamaganar auren inata zuba ido naji tsit karfa yarka tarigaka aure???

Kakuwasan dakaji kunya'' Hafiz yasosa kai yace aini karamin ubane bazanji kunyaba tunda Ban isah aureba"" Usman yaharareshi yace ahakan???

Tokodai kafitarda mata ko inhadaka da Abu mai kuli kuli da awara"" baki Hafiz yarike yace abun haryakai cen tokwantarda hankalinka dazaran nadawo zakaji komai

Usman yace sauran watanawa??? Hafiz yace bakwai koyanzu walimar labila tadawo dani danbanaso ayi bana nan"

Usman yace shikenan munadai zuba ido daidai sunkai kofar gidansu sukashiga tare sunafira suna raha hajiya bakaramin dadi takejiba idan taga yayanta cikin farinciki

Saman kujerah suka zube labila tadauko masu abinci sukaci sukahau firah sai shida saurah Usman yayi haramar tafiya harbakin mota suka rakashi yawuce yana daga masu hannu

Labila batakoma gidan sahiba ba saboda hankalinta yanakan yayanta shima washe gari tunda safe zaikoma""


Agogon Nigeria yabuga karfe biyu nadare alokacinda nasan kowa yayi nisa cikin barcinsa saikuma masu ibadar dare. Bakajin motsin komai saikukan karnuka dasuke cikin layin

Inkadauke Usman dayake tsaye yakai gwauro yakai mari tunsanda yabaro kano yakasa samun sukuni cikin ransa"" komai yakeyi fuskarta yakegani sanye cikin nikaf haryana ayyana suffarta yanda zata kasance

Gabadaya ta dabai bayemasa zuciya dakuma tunaninsa hatta abinci idan zaici fuskarta yake hangowa akan plate wanan wace irin makauniyar soyayya ce???? Kawar labila yafurta ahankali komawa yayi saman gadon yazauna yadafe kansa wanda yayimasa nauyi

Kai bazaitaba yuyuwaba wlh tunwuri dama kindaina son abunda bazakitaba samun saba dawanne ido zan kalli labila ince inason kawarta ???

Taya zata kalli maganata?? Yakamata inhana zuciyata afkawa inda baichanchanci yazama muhallinaba "" wata zuciya tace masa taya hakan zai yiyu kokamanta soyayya batayin shawara dakowa

Yayinda zatashigeka batadubà matsayi kochanchantar Abu"" yace idankuwa hakane gaskiya bataimun adalciba saboda abun nan bazaitaba yiyuwaba""


Wata zuciya tacemasa yiyuwa kai saidai inhar bakace kanasontaba koda kaki fada Dole sai zuciyarka ta tilas taka
Yace wlh karyane wannan abun kunyar badanibà ganin abun yanason haifarmasa da damuwa yayisaurin kawarda tunanin abun yafaskara tashi yayi yadauro alwala yasoma nafila yanarokoñ Allah yaciremasa sonta tunkafin yayinisa

Saikusan asuba yakwanta Amman abun mamaki maimakon yaga sauyi aransa saiyaji kamar ansake linka sonnata sau ashirin acikin zuciyarsa


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 53 · 0% Book details