← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 31 OF 121

chapter 35

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Mamaki matuka yacika labila tana tambayar kanta meyasamu dadynta yau"" majeed tuni yakoma barci daman""
Bangaren lubcy kuwa" tana ganin yafita tadauko ruwa dasauri tawatsawa suwaiba take tafarfado tachandara ihu

Lubcy tarufe mata baki tace Dan Allah kidaina ihun nan makota sunajinmu fa"" sai alokacin hankalinta yadan dawo jikinta takallijikinta taga batada kaya dasauri tajawo zanen gadon tarufe jikinta dashi tafashe dakuka tana girgiza kanta nashiga uku

Yazanyi Anty"" lubcy ce tadafata tace kiyi shiru kinji kanwata tashi mukoma cikin gida "" idanuwanta tadago zuna zubarda kwalla tace Anty na aikata babban kuskure arayuwata wlh aikin shaidanne ninasan idan mahaifina yaji wlh saiya kasheni

Lubcy tanisa tace bama zaijiba insha Allah kitashi muje kigasa jikinki gobe zanbashi hakuri"" tasake kallonta akaro nabiyu tace wlh nasan bazaitaba hakura ba kakama matarka da yaronka suna aikata zina ai hankalima nazai daukaba ballantana tunani

Lubcy tace hakane Amman meyakaiki aikata hakan da iliminki??? Tashare hawaye tace Anty wlh banason baban majeed wannan shine saurayina atadalilin kudin sa dayace yanasona sai mahaifina yadage saina aureshi nima sainaji inasonsa narabu da kb saboda baida kudin aurena

Tunranarda nazo gidan nan sainaji Sam banasonsa soyayyar kb tasake linki acikin zuciyata hardai ranarda naganshi gidan nan amatsayin driver duk hanyarda zanbi dannaga nakadaita dashi bansamuba saiyau da shedan yakadamun gangarsa batareda kokonton komaiba naziyarceshi domin yakawarmun da muguwar sha awarda tatasomun tasake fashewa da kuka tace wlh Anty niba yar iska bace bantaba yin iskanci dakowaba yanzun ma ina mamakin kaina da abunda yakawoni dakinsa nayi takaicin wannan ranar

Lubcy tajawota jikinta cikin alamun tausayawa tace na fahimceki Amman mahaifinki baikyauta makiba aiyanzu andaina auren dole kinga saka kayanki mukoma cikin gida

Tadago dasauri tana girgiza kai tace wlh zai iyah kasheni tatoshe bakinta saboda kukanda yakwacemata

Tace taya zaikasheki kitashi muje kinga masu aikin gidan nan suna waje mujeciki Dan Allah tamike tajuya tace kisa kayan

Bakin kofa tafita tasamesu tsaitsaye bata fuska tayi tace tomekuke jirah kowa yakoma yakwanta sumui sumui sukawuce tana tsaye saida takwatanci tasa kayan sannan tashiga taja hannunta suka wuce cikin gidan

Cikin falon suka samu labila zaune rungume da majeed tana ganinsu ta ajeshi tace mom lafiya??? Meyasamu Anty??? Me akaiwa babana???? Wadan nan tambayoyin tajefowa lubcy tace bakomai kidaukeshi kukoma daki dagahaka batace komaiba tawuceda suwaiba zuwa dakinta

Harkuryar daki takaita ta zaunarda itah fita tayi zuwa kitchen tasamu ruwan zafii tagasamata jikinta tabata magani tace tasamu takwanta

Ta share hawaye wadanda suketa zubowa akan idonta tace Anty konakwanta wlh bazan iyah barciba

Tace kiyi hakuri kidaina kukan nan saiya haifarmaki daciwon kai kikwanta kinji kaitagyada mata itakuma tamike taimata saida safe hartakai kofa takirata Anty

Ta amsa tareda juyowa tace nagode da soyayyarki agareni agaskiya kinchanchanci duk wata soyayya dankuwa samun mai irin halinki sai antona nagode

Tasaki lallausan murmushi tace karkidamu yiwa Kaine tawuce tana sakin shu umin murmushi aranta tace kadan kenan yarinya wannan aikin *hatsabibin boka* ne kaitsaye bangarensa tanufa

Taturah kofa tajita kulle tayita bugu yayi banza da itah karshe takoma bangarenta takwanta

Daga labila har Usman suwaiba babuwanda yaruntsa nasan bangaren KB ma hakanne Amman lubcy barci harda minshari

Bata farkaba sai bakwai agurguje tasauya kaya"" koda tafito masu aiki harsungama komai saidai tazuba akula tadaura saman dinner

Bangarenshi tanufa taturah kofar saitajita bude da sallama tawuce ciki tsaye tasameshi yanadaura agogon hannunsa tace ina kwana

Batareda yakalletaba yace lafiya yadauki takardunsa da key din motar sa yafita"" dasauri tabishi tana kiransa kowaigenta baiyiba harsuka sauko kasa

Labila tsaye da itah da majeed sunyi shirin skull cikin uniform
Lubcy tasauko kamar tafadi tace abban majeed Dan Allah katsaya

Afusace yajuyo yace wai lafiya??? Idan natsayà mezanyimaki"" gabanta saida yafadi tadan dake tace bakomai naga zakafita bakayi break ba

Yace nakoshi yasakai yawuce labila""tabishi dasauri zuwa waje tanakiràn sunansa kamar karya tsaya bayaso labila tafuskanci hàlinda yakeciki ya juyo tareda kirkiro da fara a

Takaràso tace dady morning"" yace morning my doter kintashi lafiya tace kalau idanuwanta sunakawo kwallah

Yace menene nakuka labila" yayi maganar yana dago habarta tace dad nagakamar kanacikin damuwa

Dariyar yake yayi yace bakomai banada damuwa maza Kira majeed insaukeku makaranta

Tace dad kabeer fa??? Yadanyi Jim sannan yadago yace bayajin dadi yatafi gida maxa kirashi karku makara

Tace to sannan tajuya cikin gidan yabita dakallo yacije kasan lebonsa""

Lubcy kuwa tunda yafita tayi tsaye sakeda bakiii suwaiba wacce tasauko duk akan kunnentà komai yafaru dasauri takoma saman tanakuka


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 31 · 0% Book details