← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 87 OF 121

chapter 86

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Doyar datasiya da dankali saidai tazubar shara"" tana zauna sai sake sake takeyi aranta"" tamatsu dare yayi"""

Su khadija basu suka saukaba sai dayamma"" dama usman yana yawan zuwa Dubai bayazama a hotel gida yake kamawa haryagama zamanda zaiyi Amman gidan kusa dawani babban hotel yake"" mamallakin hotel din shiyakeda gidan yayishine dama saboda saukar baki""

Gidan tsab tsab dashi Dan akwai ma aikatanda suke shareshi su goge kullum saboda irin haka karbako yafado kokuma Wanda zaidauki hayarsa yazamana yanada datti""
Bayan sun aje kayansu saman kujerar falon khadija tazube saboda zaman jirgi Usman haryanzu yakasa gane kanta kumashi yakasa yimata magana

Idan tunaninsa gaskiyane Deejarh tana kishinsane"" murmushi yasaki ahankali ganin ko kallon inda yake batayi

Rigarsa yacire yabar wando sai farar singlet dinsa"" kusa da itah yazauna yajawo hannunta yace zo injimana Deejarh na wannan cin maganin duk na menene???

Kanta yanakasa haryanzu takasa dagodakai takalleshi"" yanisa please Deejarh na kisaki ranki dan Allah kodai garin nan ne bakyaso??? Kaita girgiza masa alamar ah ah

Yace towani abun akaimaki??? Nanma tace ah ah yace shikenan kitashi kiwatsa ruwa nibari insiyo mana abunda zamuci yayi maganar yana mikewa yadauki rigarsa yasaka yafita

Tabishi da kallo aranta tace meyasa hakan mezaisa inyi kishi matar sacefa??? Nibataji haushinaba danarikemata miji saini

Haba zuciyarta baikamataba mahaifiyar sahibar tawa saurin mikewa tayi tayishirin wanka "" tashiga toilet da addua aljanie haruzzal yana biye da itah saboda cika umurnin shugabansa""

Allahumma inni a uzu bika minal hubusi wal haba isi sannan tashiga take haruzzal yamakance baya koganin gabansa haka yayita bin hanya baiganin komai

Khadija kam batasan wainarda ake toyawaba bayan tagama wanka tadauro alwala tanafito wa Usman yana shigowa da sallama ta amsa masa sallamarsa ledarda take hannunsa takarba shima yayi shirin wanka maikawai tashafa sai powder tasaka wasu Riga da siket sundan matseta bakamar siket dinma""tafesa turare tasa hijab

Koda yafito hartasoma rankon sallarda take kanta shima yashirya cikin jallabiya yatada sallah bayan sungma sukai addua"" tajuyo da fara a tacemasa inawuni

Yasaki murmushi koba komai yaga fara arta yace qalau sarkin zuciya dariya tayi tace nifa dad bafushi nakeyiba kawai yanayin zaman jirginne yasaukarmun da gajiya

Yace kedai fadi gaskiya ainalurah dake tungida kiketa shan wannan kamshin harcikin jirgi kinkasa bari muhada ido

Ledarda take gefensu yajawo yajata jikinsa yace nasan yunwa kikeji bari kici abinci kozakifi sakewa danni banason ganinki cikin damuwa

Sinasir ne damiya dakuma jelof din shinkafa yace wanne kikeso dagaciki??? Dahannu tanuna masa jelof din

Yace to inazuwa yatada itah daga jikinsa yaje kitchen din gidan yadauko plate da cup da chokali yazuba jelof din sannan yazuba ruwa dakansa yarika bata abaki tanaci hartakoshi""

Yace ga ferfesun tace nidaikam Alhamdulillah yace tonidai bari naloda yadauki chokalin zaici tarike yakalleta yadaga girah alamar mene???

Tace nima dad zanbaka"" yasaki murmushi tonaji Amman banda katuwar loma kinga bakin yanda yake very small

Dariya tayi tanarike baki"" yace yidariyarki an jima nima zanrama"" tadibo abincin tasoma bashi yace wannan saiyawuna suntsinke kafinma tabanie kiyi dasauri kinsanfa cinedani kamar gara

Tayi dariya kai dad tobari nadinga baka dasauri tayi maganar tanaciko chokalin harbaka"" yace bafa cewa nayi kidibo Wanda yafi karfin bakin nawaba tace to sannan tarage tabashi baiwani cidayawaba yace yakoshi tace kaifa kace cinedakai

Yace aiwanda naci bakici korabinsaba""" murmushi kawai tayi tace shikenan jin ansoma kiraye kirayen magrib yamike bari naje sallah"" bayan yafita itama tayi alwala tayi sallah Usman baidawoba sai bayan isah koda yashigo yasamu hartayi barci saman abar sallah tada itah yayi yace takoma akan gado

Takoma takwanta sai lokacin yabude wayarsa yashiga wanka yanafitowa kiran labila yana shigowa yadauka da fara a tayi sallama ya amsa yace nasan tundazu kinyita kirah kikajita kashe

Tace wlh kuwa kunkai lafiya??? Yashafo Kansa Wanda yake jike daruwa yace qalau muka sauka aitundazu """ muka sauka mantawa nayi ban bude wayarba"""

Tace ayya ina sahiba""" yakai kallonsa wajen khadija wacce tasake juya kwanciya saboda jindadin iskanda yake kadata""" yasaki murmushi yace tayi barci ko atada itah..

Tace no barta tahuta nasan gajiyace kawai gobe kaafada mata nakirah yace shikenan harkinje kano??? Tace ah ganima kusa da hajiya tace tana gaidakai yace kibata mugaisa mana tace to""".

Sannan tamika mata"" takarba tareda sallama ya amsa hajiya inawuni tace lafiya qalau babangida"" ya khadijar yace qalau take harma tayi barciii

Tace ayya aidole Tasha hanya idan kuntashi kagaisheta "" yace zataji hajiya ina Abdul"" tace Abdul Dan Rigima aidarensa yayi yanacin abinci yayi barci""

Usman yace ainahuta kullum nazo saiyadameni anty labila hajiya tace aibakasaniba dayaganta shareta yayi waiyayi fushi saida tanuna masa sweet sannan yaje wajenta usman yayj dariya yace sarkin rigima ai hajiya kina fama" " tace toyazanyi tunda yanace saini aidole inyita hakuri kafin yasamu sabon jini kuma ni awatsani kwandon shara

Labila tasomayimata dariya sundade suna fira sannan yayi masu saida safe yashirya cikin kayan barcinsa masu taushi yahau gadon addua yayi masu sannan yakwanta yajawota jikinsa yakura mata ido kamar maitunanin wani abun daga bisani yasaki murmushi yasunbaceta saman kananun labbanta sannan yajata jikinsa barci maidadi yadaukeshi

Lubabatu tanaganin karfe Tara nadare yayi tayi shigar ta kamardai almajirah tahau motarta zuwa kasuwar nesa da kasuwar ta aje motarta tataka dakafa zuwa wajen tayi sa akuwa maidoyar tatashi dadan karenta taje Wanda zata tona koda akwai zafi wajen

Babu mutane wajen duk anwatse tawuce kamar tana Neman wani Abu daidai wajen mai doyar ta duke taduba babu mai kallontaa wajen kuma akwai ragowar wuta

Tajaye garwasun tayi gina tajefa layar tamiyarda toka tarufe tajawo gawayi maiwuta tazuba tamike"" takarkabe jikinta tawuce saida tayi nisa tatsaya taga kodawani bakowa awajen tasakai takoma wajenda ta aje motarta tashiga tatada mota tawuce gida ranta fariii tasss hankalinta kwance bayan tagama abunda zatayi takwanta""

Makale yake da itah kamar Wanda yaji ance za arabasu cen cikin barcinsa yaji kaamar dakinne yakecida wuta

Al amarinda yafaru da khadija. Kenan kusan tare suka farka kowanne yaja gefe sukahau kallon kallo"" Usman yamurza idonsa ahankali yasake kallonta yace waibakida lafiyane???

Tayimasa duban rashin fahimta tace mekaganie dad??? Yace jikinkine yayi zafi rau kamar wutaa hannu tasa tashafo jikinta bataji komaiba tace nima naji zafin Amman banyi tunanin jikina bane"" yace shikenan tashi yayi yasake kara gudun ac sannan yacemata sukwanta

Sake kwantawa tayi yasa hannu yajawota daniyar tamatso jikinsa zafin dayaji yanzu tamkar anwatsamasa ruwan tafasasshiyar dalmace hakan khadija ma tajiii Amman dukkaninsu gefe sukah koma suna jefar juna da kallo"""

Usman yadade zaune sannan yajuya nesa da itah yakwanta yana mamakin wannan suracin dayakeji yana fesowa jikin khadija haryanzu baidaina jin zafinba dolensa yamike babu shiri yakoma falo

Yanafita yajishi wasai yasaukarda ajiyar zuciya yana kwantawa saman kujera barci yayi awongaba dashi

Bayan fitarsa khadija tadago tabishi da kallo aranta tana mamakin wannan lamarin barcin ma saiya kauracewa idonta ganin kamar tunani zaidameta tamike tadauro alwala tatada sallah

Saida asuba tafita falon daga nesa tatsaya tatadashi sannan tajuya dakin bayan tagama sallah saman abar sallar barci yakwasheta bayan tagama azkar

Sauri takeyi danyau tadan makara bata tashi dawuriba"""bayan tagama hada kayan kokon tabawa yarta tace taje tadorah kafin tazo tace to sannan tadau itacen dakomai tawuce

Dayake banisa daga gidan zuwa kasuwar tanazuwa tazube kayan tashirya itacen tahurah wutaa"" tadorah dahuwar ruwanda za adama koko""

Usman yana kusa da khadija tanabarciii yakuramata ido yana nazarinta firgigit tatashi daga itah harshi kusan taresuka mike

Usman yarasa inda zaisa kansa dasauri yajuyaa yabar dakin Amman baiji sassauciba dole yafita gidan yanatafiya dasauriii

Saida yayi tafiya mainisa yadainajin komai ajikinsa bakin wata bishiya yazauna yadafe Kansa yanamaida numfashi

Bangaren khadija ma saida Usman yabargidan tadainajin zafiii ajikinta""" natsuwa tana dawomata tasoma furta innalillahi wa inna ilaihir rajiun

Harkusan azahar batasake ganin Usman ba"" shikuma yanacen dazaran yatunkaro gidan saiyajie kamar anasake huromasa zafii atakaicedai wani hotel Yakama nesa dagidanda khadija take
Harzuwa yanzu bakin Khadija baidaina addua ba"""

Al amarin mai doya kuwa tunda yarta tadorah koko hartasiyar Amman badukaba tadorah doya harkusan marece hajiyar jiya batazoba gashiyau tayi dayawa kumayau bakasuwa"" kawai saita saukartà tallen suya tajaye wutaa tadauko wuka tahau Gina kasa

Saida tayi Gina maidàñ zurfiii saiga layu sunyi jajirr sunata fesarda wutaa"" aikuwa tacirosu tawatsar tadibo ruwa jikinta yanarawà zaninta kamar zaifadiii tawatsawa layarnan sannan tacewa karamin danta yayiwa layar fitsarii


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 87 · 0% Book details