← Book details Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 28 OF 121

chapter 32

Hatsabibin Boka Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

By
Gentle Lady💃🏽


Dasauri tamike zuwa bandaki yabita da kallo tunda suke tare bata tabayin wanka aLookacinda suka taraba

Koda yace tatashi tayi wanka cewa takeyi bayanzu zatayiba saida safe idan suntashi sallah Amman yanzu dabama Kusan tarta yayiba tajeyin wanka yanatsaka da tunaninsa tafito daure da towel

Yasake binta dakallo yana hadiye yawu shikam baisan yawan bukatarda yakeda itah ba baitabajin ya gamsuba komenene dalili

Ruwan jikinta tadan watsamasa yadago yana kallonta gira tadaga masa tace tunanin me kakeyi???

Yace kekanki kinsan tunanina bayawuce matsalarki wlh kokadan banji nasamu natsuwaba hartausayin kaina nakeyi

Kusa dashi tazauna tana goge kanta tace hakuri zakayi basaura kwana sha huduba aikamar gobene zaka angwance ni idan kayi auren nayafemaku kayi wata daya dakinta kasamu kamore amarcinka

Cikin alamun nunajin dadi yace dagaske kikeyi??? Talunshe ido tabude kadaina shakka ko kokwanto akan maganata babu abunda bazan iyaba indai akankane"" fatana shine kasamu abunda kakeso

Inason ganinka cikin kwanciyar hankali yalumshe ido yabude yace nagode matata farincikina

Tace karka damu kaje kayi wanka ko yace hakane yamike yadaura towel yashiga toilet dasauri tadauki wandonsa tareda abunda kecikin kwalba lakame da towel dinta tafita zuwa dakinta

Tanazuwa ta ajesu waje daya tasaka kayan barci tafito zuwa dakinsa koda yafito yasameta hartakwanta wasu kayan barci yasaka shima yahau gadon

Yajawota jikinsa tareda saukarda ajiyar zuciya sosai yanason jin duminta Amman tunsanda batada lafiya batasake hada shinfida dashiba kullum dakinta take kwana sake jawota yayi cikin jikinsa barci maidadi yadaukeshi tareda mafarkai masu dadi washe gari saida yasake wanka kafin yaje masallaci

Bayan kwana biyu yashigar mata da kayanda yasiyomata tanata murna tanayaba kayan"" yadaukesu sukaje kasuwa yace kowa yazabi kalar abunda yakeso

Sunkawo kaya sosai duka yabiya kudin Dan sainan nan yakeda itah" tuni tasanarda kawayenta suzo ranar asabar maizuwa akwai fatynda tashirya Na musamman"" agidanta Sam bata sanardasu aure Usman zaiyiba

Ankai lefe gidan Amarya kuma duk wadansu kudi da ake bukata ankai dagashi sai Abdul sukeyin hidimominsu saboda"" bashida wasu abokai""

Ranadai bata karya saida"" uwar diya taji kunya""yaune dubban jama a suka shaida daurin auren Usman da suwaiba akan sadaki dubu Dari biyar"

Daurin auren yasamu halarta mutane sosai dayake Usman mutumen mutanene"" ango yasha farar shadda sai wasar hakorah yakeyi shikadai yasan abunda yatanada adaren yau

Lubabatu ce cikin dakinta tareda kawayenta sadiya larai sajida aneesa rabi atu"" sadiya tace waini kince muzo gidanki Amman bakisanardamu komaiba kuma munga gida cike da alamun biki akeyi""

Tamurmusa tace biki akeyi kuwa"" larai tace bikin mene??? Tace aure dadyn majeed zaikara kusan tare suka hadabaki aure????

Tagyada kai tana shan lemu "" sajida tace tirkashi kuma kike zaune anan??? Takalleta tace tome kikeso inyi kinasone intada hankalina bayankuma mijina yanasona???

Rabi atu tace soyayyar banza ai wlh duk sonda danamiji yakemaki dazaran yakara aure zakizama photo"" aiyanzu yadaina yinki tunda yasamu yarinya bayankuma shine yamaidaki hakan

Ta aje kopin hannunta tace ninasan mijina yanasona sosai"" kuma babu tayanda wata zatafini matsayi acikin zuciyarsa

Sajida tasheke da dariya tace naga alama giyar soyayya batagama sakinkiba tokibude kunne kiji namiji dakike ganinsa tsohon munafukine bazaki gane hakanba sai ankawo matar

Barinma ya tas tata yagano tafiki sweet hmmm sunanki sorry kinaji kinagani zakikoma borah agidan nan
.takarewa gidan kallo kinga wannan gidan wlh kinagani zai gagareki zama

Dake dayayanki gidan nan zaikoma maku tamkar kurkuku bari kiji yanda mukayi da dadyn ihsan lokacinda yakeson yin aure Sam bainunamun komaiba kamar yahadiyeni dama gayanda muke kullum sai riritani yakeyi da dadin baki

Nikuwa ahaukana sainaga aisonda yakemun kamar baxaiso wata bayan idona ba"" saiban dauki matakin komaiba nayita rawar kafa har aka kawo Amarya

Nikam sai lokacin nasan natabka babban kuskure na aminta da danamiji dansaboda kawai yamun dadin bakin soyayya

Idan yanadakinta wlh ko motsinsa bakyaji saidai inshige daki inyita kuka saboda takaici sairawar kafa yakeyi inhar girkinta yazagayo Amman ranar girkina sainaga baya walwala bayanuna zakuwarsa

Lubcy tace toyakikayi??? Tace hmm aisaboda naga wankin hula yanashirin kaini dare" kawai nakai sunanta wajen *hatsabibin boka* aka kadamun Yar banza hatta cikin datafita dashi aka narkardashi yabi mazubar ruwa

Sukasa shewa suka taba rabi.atu tace wlh kinmun daidai"" aikishiya ba abokiyar zamabace mekike jirah kinsandai yanda kikashigo rayuwarsa danhaka idan kikatsaya wasa wata tashigo takarbemakishi

Lubcy hmm kawai tace sajida tace kaikudaina wahalda kanku tasan abunda tataka"" lubcy takwashe da dariya tace kudai akeji mahaukaci yafada rijiya

Kamar ance sudaga Kansu sukayi arba da labila tanarike dakugu takallesu dai bayan daya tace hmm wannan muguwar hudubar kukazauna kuna koyawa mamana duk danasan batada mugun hali Amman bazan shedetaba danzata iyah sauyawa

Danzama damugayen kawaye irinku hatsarine garayuwar iyali "" lubcy tadago afusace takunduma mata zagii abunda bata tabayiba tace asheke shasha shace??? Anandin kinunamun abokin wasanki

Wlh karnasake ganin kin shigomun daki waima tsaya labe kikemana ko??? Idanuwanta sunakawo kwallah tace komadai menayi wlh muddin matar dady wani Abu yasameta saina sanardashi gun boka kikezuwa lubcy tataso daniyar dukanta taruga dagudu tace kukuma kuji tsoron Allah inkuwa bahakaba kuyi mummunan karshe takafro kofa ganin tana niyar dankotaa


Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠
Chapter 28 · 0% Book details