← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 110

Sashe 98

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu abinda baka yi da ni ba, ka ciren kayana ai k................"
"Lah ha ila ha illah, muhamadu rasululah, Sallallahu alaihi Wa salam, innalilahi wa inna ilaihi raj'une innalilahi wa inna ilaihi raj'une innalilahi wa inna ilaihi raj'une " Mamah ta dauka tana kaiwa zaune hankali tashe ta sake zubawa Furera ido, zuwan da Furera ta yi dan sake tambayar tafia suren kawarta shekaran jiya da abin Mamah ta kwana a ranta, tunda yarinyar ta zo yannayinta ya ringa ba Maman mamaki, sai dai da gagawa ta cire abin a ranta ta kuma yi fadan ita fa bata da lafia ta yaya take son zuwa wajen aure?, A yanzu kuwa gaba daya abin ya dawo mata sai ta idasa ganni kwado kwado a bayane, tana daya daga cikin mutanen nan masu baiwar gannin wata kama a tare da mutun idan suka kalleshi, yannayin mutin ne kawai ke nuna masu hakan, hankali tashe cikin muryoyin kukan nan Mamah ta ce" Ke Furera, yaushe rabonki da gannin al'adarki?"
Nan fa wajen ya dauki shiru, shiru na dif lokaci guda, sannan kowa ya juyo inda Fureran take hankali tashe ya zuba mata ido, Sayadi kuwa dake rike da kansa a tsugune tana ta fama da zafin faduwar da aka maka shi a tsorace shima ya kallo inda take
Hankali tashe ya ce" To walahi in dai ciki ne da ke ba ni bane, dan ie shaida ce ban taba saka maki abina a naki ba, a baki baki dai nake gogawa daga haka ki saka wandonki ki yi tafiyarki, watarana wandonma bakya cirewa, in dai ciki ne da ke toh bama ni bane mai laifin da za'ana dukana na rantse bama ni bane!"
Yanzun kam babu wanda ya ankara sai jin faduwar mahaifiyar Furera aka yi a kasa, ta fadi sumamiya, Nan fa hankalin Mamah da maman Abul ya yi kanta, Amir kuwa ya saka kuka ya kai tsugune hankalinsa tashe a gaban yayansu ya ce" Yayanmu, dan girman Allah ka barni na harsbe shi nima a harbeni, yayanmu ka barni na kashe shi nima a kasheni, wayo Allahna ya wulakantamu ya wulakanta mana kanwa, yayanmu ya wulakanta mana kanwarmu bayan mu mun rike kawunanmu daga duban
an wasu, yayanmu ya wulakanta mana kanwarmu bayan mahaifinmu har ya mutu yana kafa kafa da addu'a da komai, yayanmu ka barni na kashe su su dukansu biyun nima ka harbeni a kaimu a birne baki daya, yayanmu dan Allah ka barni wayo Allahna wayo Abanmu wayo Allahna wayo Allahna tonon asiri innalilahi wa inna ilaihi raj'une......"
Kuka Amir yake yi wanda ya saka su Auta kuka ita da ZAHRA
A hankali ya dauke dubansa daga kan Amir din ya sauke a kan fuskar Zahra , wace tun shigowarsa bai ganta ba sai yanzu
Hawayen dake saman kumatunta yake kallo da ita din kanta
A hankali ya dauke dubansa, jikinsa du ya yi nauyi ya sake kallon kan Amir dake saman cinyarsa yana kuka
A hankali ya iya daga hannun nasa ya dora a saman gashin Amir din yana dan shafawa alamu na rarashi sannan ya zubawa su Mamab ido, maman na su Furera ta farfado sai dai idannuwanta a rufe kuka take yi kamar ranta zai fita, fadi take yi inama mutuwa ce ta risketa kafin wannan ranar?, Maman Abul kuwa gaba daya hankalinta ya tashi, ta rasa ina zata saka kanta, magangannun dake yawan dawo mata irin nasihar Mamah a kan muzgunawa yar mutane, magangannun Mama cewar su ji tsoron Allah, su guji kamuwar Allah, kar su ga sunna kilace basu isa su zagaye kadararsu ba, su bi duniya a hankali su yi ta kansu ke ta dawo mata a ranta,
Allah yana gani, wani irin dana sani ke mata yawo a zuciya, ta yi zaune sokoko ne ama gaba daya jinninta ita ta san ya hau ne
Da kyar ya iya sake duban Furera, wace kana ganninta ka san a yau dukkan wani tashin hankali na duniya ya taru a kanta, a tsugune take ama babu inda baya rawa a jikinta......, Ta kalli wannan ta kalli wancen ne, gaba dayanta a firgice take ne
A hankali ya ce" Zo Furera, zo nan"
Ta riga ta san a yanzu bata da wata madafa, bata da wajen buya bata kuma da yadda zata yi, abu ya riga ya fito du irin yadda take iya yinta dan kar ya fito din, wannan tafia da ta nace bama wajen aure zasu je ba domin babu kawartan da take aure a wani gari, ta sanarwa kawarta damuwarta ne kawar tata ta sakata samun permition a gidansu su je gannin likita a mata daukan jinni idan har cikin ne su zubar su dawo duda ta sanarwa kawarya Sayadi bai taba ratsa tantanin budurcinta ba, ama kuma wasa na gidan duniya da azakarinsa babu abinda bai yi ba a jikinta kuma a nan yake zubarwa da abinsa bata taba damuwa ba dan watarana har barci suke yi hankali Kwonce sai ta je gida take wankewa dan a tunaninta ai ba ratsata aka yi ba babu abinda zai sameta, sai ga tashin hankali, bakon al'amari bata ga al'adarta ba tun auren su yayansu, shiru al'ada bata zo ba, hakan ya sa ta yarda da maganar kawar tata har ta fara neman hanyar tafiyar, domin ko hauka take ba zata yi tafia haka ba tare da an san ta yi ba
Da rarafe ta karasa ta duka jikinta na ci gana da yin rawa
Yana kallonta ya ce" Furera, yaushe rabonki da gannin al'adar taki?"
Furara na kuka ta sanarwa yayansu bata gani bane wannan watan
Da kyar ya sake budar bakinsa ya ce" Furera, bayan wancen yaron da wa kuma kuke lalatar?"
Sosai maganar ita da kanta ta mata soketa, tai mata nauyi, ta mata zafi bale mahaifiyarta da kuma Maman Abul, wai yau ita Furera itace wannan abin ya sameta ?

Yau itace a gaban kowa take tabatar da eh lalle ta aikata aikin nan?

Shin me ya kai wannan kunya da tashin hankali?

Sai take ji inama itace ZAHRAh, sai take ji dama itace ZAHRAh
A sanyaye ta ce" Yayanmu, banda shi walahi walahi ban taba kula kowa ba, a duniya shi kadai nake kulawa shine saurayina a gidansuma an sani, a nanne kawai ya ki ya gabatar da kansa a wajenka wai sai ya tara kudi, yayanmu kuma bayanshi walahi walahi ban taba kula kowa ba da sunnan wani abin, yanzu haka a kaini asibiti a dubani walahi ban taba iskanci da wani ba yayanmu Allah ban........."
Wani irin rikitacen mari da Amir ya kantsa mata a dole ta hadiye maganarta lokaci daya tana dantse harshenta....

Bai barta ta sarara ba ya mike ya shiga kwalo da ita yana zare belt dinsa ya ringa tafka mata
A rikice Mama ke son rike shi ama ya kasa rikuwa
A haukace su ZAHRAh suka yi bayan kujera suka labe sai bari jikinsu yake yi dan an saba irin dukan nan gamido ake yi a zane kowa da kowa shi yasa yanzuma suka yi ta kansu suka kuma yi tsittt da kukan da suke yi danma kar ya saka a san da mutane a wajen a janyo su
Da kyar ya iya mikewa ya rike shi yana kallonsa a kausashe ya ce" Ya isa haka, ka je da shi maza kuma kar ka kuma dukansa ka bari idan an gama bincike in har yana da laifin da ya shafi fyade ko ya ki amsar abinda yake cikinta dai ka shigar da kararsa, bayan wannan hukuncin zina kawai ke kansa, ba dole ya yiwa kanwarka ba ta fada maka da bakinta, ita ta tarda shi ta shaida maka itace take zuwa inda yake, ka yi hakuri Amir, ka yi hakuri ka daina kukan haka, ka je kawai ka yi abinda ya dace, kar kuma ka daga muryarka domin mune bamu da gaskiya, ta wuce shekarun ace wayo yake yi mata, yaudara ce dai ta namiji ta bi sawu, ta yiwu wata ishara ce ta rayuwa Allah ya nuna mana baki daya, dan kasancewarta y'ar Docter ko a kilace ai ba shi zai hanna hukuncin Allah sauka a kanta ba......, Ko menene saukin a wajen Allah zamu nema, dan bata ga al'adarta ba ta yiwu ba komai bane wasa ya fara mata.......ko wani abin, idanma abinda ake tunanin ne sai mu bi a hankali kar mu yi kirari mu dabawa kanmu wuka.....

So ka je kawai da shi ya yi tafiyarsa, sai ka yi bincike ka ji?"
Amir da kirjinsa ke ta sama yana kasa, hankalinsa tashe ya ce"
Amir da hankalinsa ke karra tashi yana kallon yayansu da kuma Sayadi da ya fice da kansa da sauri tunda ya ji an bada amanar ya tafi ya ce" Yayanmu, idan fa cikin ne da ita?

Yaya zamu yi da ranmu?"
Idannuwansa ya rintse, jajayan idannuwansa na sake daukan ja, muryarsa na sake raunana ya ce" Yaya zamu yi kuwa?

Amsa zamu yi, domin babu mai zubar da shi sai ta haife shi, ta yiwu ta gane me ake nufi da bin duniya a hankali, ta yiwu baki daya ahalin gidan Docter hanyar da zasu gane abinda Docter ke fada masu ba dare ba rana ne ta laluma har ya koma ga ubangijinsa yanzun Allah ya fito da hanyar da zamu ji asalaun ji?, Amir ka sani babu abinda ya kai min wannan ciwo, inama zan iya rusa kukan nan nima?

Amir tun yanzu na gaza, tun yanzu na gaza Amir?

Laifina ne ko?, Na gaza rikewa , da ransa ai hakan bai fito ba, yana rasuwa har an fara irin haka?

Ba kaine da kuka ba Amir nine nan da kuka................"
Ya karashe yana zaunawa ya sake dora hannayensa gaban goshinsa ya rintse idannuwansa kwallah na cika idannuwan nasa......

Maman Abul dake sharar kwalarta ta ce" BABANGIDA, kar ka yi kuka ka ji?
Chapter 98 · 0% Book details