Sashe 45
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Innalilahi wa inna ilaihi raj'une" ta fashe da matsanancin kukan da ya saka shi yin dan taga taga da ita din ya kusan dirkuwa a kasa , Allah ya sa Amir na kusa da sauri ya tare ta hanyar saka hannayensa ta wajen cikin MARSHAL ya tare da karfin da Allah ya bashi a birkice yana fadin" Subahanalah Yaya"
Da sauri security din dake ta kai kawo na airport
din suka nemi kawo agaji
Su suka taimaka masu daga MARSHAL din har Maman suka nemi a kaisu asibiti amma ya kiya dole aka saka su a cikin motar daga baya su dukansu Shi kuma Amir ya koma gaba ya tayar da motar sai kuka yake yana share hawayensa hankalinsa duk a kansu yana kula da irin yadda Marshal yake rike da hannun MAMAH har ya ga ta dora kanta a gefen damtsen hannunsa hakan ya saka shi jan numfashi a hankali ya dora kansa a jikin madubin motar ya zubawa hanya ido a lokacin da Amir ke tuki shi kuma ya lula a duniyar abinda yake cikin kwakwaluwarsa da kansa
Magangannun Abah a lokacin da suka kamo hanya har a cikin jirgi har suka sauka na neman halaka masa zuciya
Ya rasa ta inda zai kamo , ko a inda zai ajiye magangannun nan
Abah fa ya jima da gane cewa wannan ciwon nasa na ajali ne shi yasa ya ringa saka shi a ukun rayuwa da tunani kala daban daban
Yanzu yaya zai yi da ransa?
Ina zai kai wannan nauyin?
A lokacin da ya gama gyarawa Abah zama a cikin jirgi bayan zasu daga Abah ya nace kan sai ya dauki waya ya saka masa ya yi recording din magangannun nan da ya masa su suke dawo masa tamkar mutun ya hadu da fatalwarsa
Yaya zai yi da ransa ne?
Ina zai dosa?
Tsayuwar motarsu a kofar gidan, da saurin zuwan sojawa sunna kare mutanen da suka nufo motar rututu sunna fadin su bari ya fito da kansa sai su gaisa ya saka shi zubawa kofar gidan ido har zuwa jan motar da Amir ya yi ya shige da ita ciki dan ba zasu bari ya fito a tsanake a haka ba ya gangara har bangaren Abah shi kuma yana bin komai da ido tamkar ana zana masa ne a cikin kwakwaluwarsa ya sake zubawa kofar ido tarin matan dake zazaune da irin tarin jama'ar da yake hange daga ciki ya sake daga masa hankali, wadannan din dukansu sun zo zaman makokin Abah ne?
Shikenan Abansa?
"Babana, ka daina son katse maganata kuma ka saurara har na gama mana, dole fa ka jajirce bakinka ya bude , kaine ubansu dan kaine babba, lalle shekarunka sun dauko rigima dan kuwa ina tsoron rikicinsu ya hadasa maka furfura da wuri, ka ga dai ni yadda Allah ya yi da ni, dole kaine zaka jajirce, Babana wuka da nama a hannunka yake , Ahalina sun rataya a wuyanka Sulaimana......" Da sauri ya rintse idannuwansa tuna wannann magangannun, a hankali ya kali Amir ya ya duko kadan yana sheda masa sun fa karaso, ina zai kai Mamah ne?
A hankali Maman ta dago kanta dake sara mata
ta ce" Amir, kai ka raka ni wajen yan uwana, shi kuma ya fita wajen mutane ya zauna, Aban Docter ka dan taba wani abin ka ji?
Kar yinwa ta kayar da kai"
Idannuwansa kawai ya iya lumshe mata a hankali kuma ya budi bakinsa ya ce" Mamah, zaki ga docter, Please kar ki sha abu mai siga kin ji Mamah?"
Da kyar ta kakaro dan yannayi na son kwantar masa da hankali lokaci daya kuma ta ce" Bani wayar nan mai recording din docter"
Sai da ya ji gabansa ya fadi, niyarsa zai je ne ya zauna ya goge du wani abinda bai masa a hirar ba, dan akwai manyan abubuwan da Aban ya fada wa'inda baya tunanin in har shi din nan zai iya zaunawa da ahalin Docter su saurara tare ba, tun daga maganar gidan nan da ta aure, baya tunanin in har yana da abinda zai saurara daga gare su baki daya kalaman nan, sai dai gashi Mama na so ta masa abinda ba shikenan ba, dan ya tabata kamar yadda ta dauki alkawari a lokacin da aka rufe fuskar Abah da likafani sai ta aikata
Jiki ba karfi ya laluba aljihun wandonsa ya ciro karamar wayar baka ya saka a hannun Maman sannnan ya bita da ido har aka taimaka mata ta fita a motar aka nufi ciki da ita
Idannuwansa ya sake lumshewa ya sake jinginar da kansa a jikin kujerar kirjinsa na dokawa da karfin gaske, duka duka yau aka fara, ba yau ciyar da su shayar da su ko tufatar da su ke kayar masa da gaba ba, ko daya, dama ya saba, abu ne da yake yi sai dai a taimaka masa idan an yi niya, abinda ya fi kayar masa da gaba a yanzu fitowar da zai yi ya yi tsaye a gabansu a matsayin UBA, ya zamto zasu rataya a wuyansa ne, zai daina rayuwa da tunanin kansa shi shi daya, dole zai zauna ya dube su ya fuskance su ya ji damuwarsu, dole zai san hanyar magancewa, dole zai dauki mataki a lokacin da bashi da karfin hakan, dole zai dube su ya biya masu bukatunsu koda kuwa shi zai tauye nasa bukatun, dole zai shiga hurumin tsagairunsu da kansa, dole zai yi hira da yan matan baki daya dan ya san su waye su me suke nufi da rayuwarsu ta yau da kulun
Kiraye kirayen sallar magariba ya saka shi dole fitowa daga motar yana bin kowa da kallo
A nutse ya dakatar da masu shiga tsakaninsa da mutane ya hanna su aikata hakan sannan ya ringa amsa gaisuwar nan a tsanake har ya fice ya daura alwallah ya karasa masallaci da gaggawa ya bi sallah
A masallaci wata doguwar hira dole ya tsaya ya bi dan masu masa ta'aziya ga kuma kannensa maza duk a gefensa hakan ya saka shi kara jin wani girma na sake hawansa har suka gama suka nufo gida shi da yan uwansa da Aban Ahmad bangaren samarin gidan suka zauna a falo sunna sake yi masa ta'aziya da ban baki sosai shi kuma yana sauraronsu yana kuma amsa su yadda yaa kamata
Jalaluddeen ne ya shigo da kayan abinci ya ajiye ya koma ya sake kawo kayan shayi ya ajiye sannan ya zauna kansa a kasa ya ce" Babangida Wai maman Furera tace ka ci abincin nan Mamah tace masu baka ci komai ba"
Dan tsai ya yi yana kallonsa, sai kuma ya ce" Ita maman ka ganta ne?