← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 110

Sashe 86

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Luba ta ki kawo mata kayanta ne
asa ta duka tana gaishe da mahaifinta, shima sai murmushin yake yi yana amsawa da yi mata yan tambayiyi na bakunta, sannan ya wani gyara zama ya shiga yin nasiha a bi miji a yi kokarin yin biyaya dan aljanarta tana karkashin kafafuwan mijinta, ya juya wajen MARSHAL ya yi masa tasa shima nasihat harda su a ringa hakuri da yara a kuma kiyaye dukan hakokin iyali, nan ya mike ya sanar mata zai yi tafia sai ya dawo, ya ajiye mata ambulop dauke da sako da kuma numbarsa ta waya sannan ya tafi yana jiran MARSHAL
Marshal ya girgiza kai ciki ciki ya ce" Na tafi"
A hankali ta ce" Allah ya tsare, a dawo lafiya "
Shi dai ya fice sai kumbura yake yana batsewa ya shiga motar suka fita tare sunna tafe sunna yi kamar su tsaye su daku dan kuwa wannan yace wannan yace har dai suka fito daga daurin auren sannan ya ajiye shi gidansa suka yi salama kan dukkan abinda zai faru da waya zasu sanarwa junna
A bangarenta kuwa, yauma haka ta wuni tsna dirkar madarar nan da ruwan nan na basir wai, kafin kake cewa yama ta yi sosai cikinta ya wani irin daurewa hakan ya sa ta shige da wuri ta kwonta lamo batama san shigowarsa ba sannan ta bara masa amvelop din wajen mahaifinta ko budewa bata yi ba ta ajiye masa saman table ta san zai gani idan ya shigo
A haka washe gari Luba suka daga ita da mahaifiyarta, ita batama san da mamanta a tafiyar ba, ta dai san Lubar zata tafi domin ta zo ta bata maganin basir din nan da na madarar ta sanar mata ya kasance tana sha koda yaushe zai wanko mata dukkan datin cikinta, ta kuma sanar mata ai marartama da tace tana mata ciwo kar ta damu wankewar ne yake yi, ....haka dai ta ci gaba da rayuwa a gidan, sukan hadu da safe dan ta zuba masa abincin da aka kawo daga wajen Mamah, idan ya tafi sai dare ita kuwa ta yi barcinta, shi yakan shiga ya kunna fitila ya ga eh t yi barcin ya kashe mata ya tafi dakinsa, a kulun kuwa idan ya ganta da shigar kannanun kaya ne sai ya girgiza kai kawai, ya daina kureta da kallo in ba ya zama dole ba, yana so kuma MAMAH ta gane manufarsa ta son ya raba masu waje, ba dan komai ba sai dan lafiyarsa da ta yarinyar, yau kimanin sati biyu kennan da aurensu, an daina kawo masu abinci daga wajen MAMAH, babu abinda ta gaza domin tunda aka daina kawo abincin ita ke tashi tun kafin ta yi alwallah ta daidaita komai tana gama sallar asubahi ta sake sauka ta kwashe komai ta daidaita saman table , wani lokacin tana shiryawar yake saukowa , wani lokacin kuwa sai ta gama ta haye yake saukowa ya ci , sai kuma ta sake komawa barci karfe tara na yi ta fito ta shige kicin, du irin azabar ciwon marar da take yi haka zata yi har na yama ta kilace Auta ke mikawa Yaya Amir ya kai masa na ranar , na daren kuwa ta gyara masa ta kilace saman table ta haye sama ta yi ta murkususu baiwar Allah ta ci gaba da shan ruwan nan da madarar a tunaninta sauki zata samu har sai da abin ya fara fin karfinta, domin a daren jiya kwana ta yi tana kuka, jikinta ya rufe ruf da zafin zazabi, bata da karfi ko daya a jikin nata, a hankali a hankali kafin safia ya idasa wayewa ta idasa fita a hayacinta, aka yi rashin Sa'a a ranar karfe hudu na dare ya fice sakamakon kira da ya samu an tare motocin minister barayi sun kawo masu hari bayan fitar boye ne zai yi, hakan ya sa ya fice da gagawa ba tare da ya tasheta ba a tunaninsa barci take yi, zuwansa kuwa abu ya ja dama domin sun dauki hanya da mota daya dole ya sa suka bazu ake aiki ba ji ba gani
Karfe tara da wasu mintuna Auta ta karaso ta bude ta shige tana salama hadi da kiran auntyn nata, sai dai shiru ta ji ba amsa ba alamar za'a amsa
Zama ta yi ta kunna TV ta shiga kallo a kalla ta dauki wani minti talatin a haka, gannin dai shiru ya sakata ta hau ta tsaya kofar dakin ZAHRAN tana dan bubugawa tana kiran sunnanta dan yayansu ai baya nan, kuma da itama ta fita kofar koda ta saka code din ba zai bude ba dan kilewa zata yi idan har fita zata yi
Kamawa ta yi ta murda dan gannin ko a kile dai kofar?

Tana murdawa ta ga kofar ta bude, nan idannuwanta suka sauka kan Zahra shame shame tamkar wace ta mutu
Da sauri ta shiga tana kiran sunnanta, idannuwanta a lumshe suke, hannunta ta kai dan tabata, nan ta ji zafin da jikinta ke fitarwa, hakan ya daga mata hankali ta ringa kiran sunnanta tana fadin lafiya?

Menene?

Ama ina Zahra bata da karfin aiwatar da komai, sam bata cikin hayacinta a dole ta fita da gudu ta yi bangaren Mamah ta sanar mata auntynta na cen Kwonce ba lafia tana tunanin ko har amai ta yi dan ta ga abin amai kasa
Hankalin Mamah ya matukar tashi, ta rasa yaya zata yi, fitarta uku tana sin tafia ama sai ta gaza ta tsaya a balbalin gidan tana son zuwa ta saka daya daga cikin matan ta je ta gano mata ama ta gaza shima domin tunda aka yi auren nan Matan docter ko Allah ya sanya alkhairi babu wace tace,
Da kyar ta koma ta dauki wayarta ta yi ta doka masa kira, hankalinta a rabe gida nawa nawa, abubuwa biyu ne kawai suka shiga kwakwaluwarta, ta yiwu yar tata har karuwa ta samu, ko kuma dai rashin lafiyar tasa ce?

Ita dai ta kasa zuwa kai tsaye dan matar Babangida sunnanta, kuma
angaren babangida ne, ko yayane dole ta gaza shiga, babangida fa danta ne na farko
Da kyar MAMAH ta same shi, a lokacin shi dinma yana hanyar gidan da nufin zuwa ya yi wanka da yama ya sake fita, dan haka yana dagawa ya ce" Salam MAMAH yau ban leko ba ko?

Na fita ne ama ganima na kusa karasowa"
MAMAH ta ce" Baba bama wannan bane , Zahra ce ba lafiya dan Allah ka yi sauri ka karasa ka mikon ita idan dole mu je adibiti dai mu tafi dan ka ga likitar nan du in ba kai ka kireta ba ta cika bata lokaci ka ji?"
Faduwar da gabansa ya yi dan kawai an ce ba lafiya ya saka shi dan dagawa ya yiwa direba nunin ya yi gagawa sannan ya sanarwa MAMAH gayanan
Yana kashewa ya yi kiran likitar ya fada mata su hadu gida yanzu yanzu sannan ya ajiye wayar ya zubawa hanya ido yana tunanin me yake damunta ?

Bata da lafiya?

Da sauri sauri yake haurawa dan ji yake yi burinsa ya ganta ya ga lafiyarta a yanzu, da sauri ya saka hannunsa ya bude kofar ya.......

Ya saka hannunsa ya bude kofar ya shiga dakin yana baza dubansa dan son ganninta, har cikin zuciyarsa yake son gannin inda take, zuciyarsa kuwa na dokawa da karfin gaske
A hankali ya karasa inda take kwoncen nan ya duka yana dage gashinta da ya rufe mata gefen fuskarta
A sanyaye ya dan ringa shafa gefen kumatunta muryarsa a sanyaye yana kiran sunnanta, sai dai sam bata motsa ba ko alamun motsawarma bata yi ba
Yauma a jikinta riga ce doguwa ama tsagar rigar har saman cinyarta kuma lafafiya ce ta barci, ga kuma zafi da jikinta ya dauka kirjinta kuwa ta rigar nan sai dai idan baka kalleta ba ya yi tsini da shi ya dan kumbura fiye da da
A hankali ya dane wayarsa da ta kwashi kuka dan kar ya tasheta a tsorace, dan idan ya ambaci sunnanta tana amsawa cen kasan makoshinta, ciwo ne kawai ke nukurkusarta ya hanna mata walwala ko wani motsin kirki sosai
Sake bugo masa da aka yi ya tabatar masa kawai doctern ta zo ne, dan haka ya kashe wayar gaba daya sannan ya saka hannayensa bayan ya cire rigar kakinsa dan yau da kaki ya fita ama da wata bak'ar riga a kasa mai kananan hannu irin daidai da damtsen hannu wace ta rikeshi da kyau din nan
Gaba dayanta ya talafata a jikinsa, a hankali ya dago hannunsa dan danshin da ya ji a inda ya rikota ya dan zubawa abin ido ya dan murza a hannunsa ya ji da dan danko danko hakan na nufin ba fitsari bane, sannan abin ba ja kennan ba jinni bane, sai kawai ya dafe bayanta ya basar da abin ya fice da ita a haka ya sauka kasa inda yake jiyo muryar Auta da Mamanta da kuma Docter, watau Mamah ta gaza hakuri ta biyo docter
Mamah na hango haka ta mike tana masu salama dan kuwa ba zata iya zama a idasa abin nan a gabanta ba, rungumar wata iri jama'a, sai kawai ta yi fatan Allah ya bada lafiya ta kada keyar Auta dake dan zarro ido sula fice
Saman kujerar ya shinfidata sannan ya zauna gefe yana ba Likitar damar ajiye sara masan da ta yi domin docternsu ce ta wajen aiki
Hannun nasa ya dan karra tabawa, abin ya bushe yanzu ba fan danko dankon dan haka ya dubi Likitar dake aunata tana dan juyar da kanta ta bude idannuwanta ta haska yar fitila a hankali ta ce" Tana da ciki ne?"
Da dan mamaki ya kalli likitar, ciki kuma?

Sai abinma ya saka shi dan sakin murmushi, yo itama yaishe aka haifeta?

Allah ya tuba ya haki mace iya haka na shekara nawa bata dauki ciki ba sai y'ar yar nan da aka bashi jiyan nan?

Kuma bai yi mata komai ba?
Chapter 86 · 0% Book details