← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 110

Sashe 56

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tausashe sosai ya ce" Mamah, damuwar rashin Aban ne take ta bayana a saman fuskar ki?"
Mamah ta lumshe idannuwanta, hawayen da suke ciki suka samu zurmiyowa saman kuncinta, da sauri ta saka hannunta ta goge tana kallonsa ta ce" Abah, yaya zan yi toh?

Ai dole na yi hakuri da rashin docter tunda na san inda ya je nima zan je da zarrar an kirayeni, ba ma wannan bane damuwar tawa, gama yi min bayanin da kake tafe da shi"
A hankali ya dan matso kusa da ita yana kallonta, a sanyaye ya ce" Mamah mene ne damuwar me yake damunki?"
Mamah ta bude idannuwanta masu launin jajaja ta ce" Abah, bana son maganar yarinyyar nan, Minal, bana so kwata-kwata, tun ba yau ba na sanarwa Mahaifinka, bata kwanta min a raina ba yarinyar, ba dan ta min wani abu ba, ba kuma dan shekarunta ba, kawai a cen kasan zuciyata na ke jin bana so ta zamto abokiyar rayuwarka!"
Sai da ya samu kansa da sauke ajiyar zuciya, dan wallahi ya tsorata, a tunaninsa damuwar Maman ta rashin lafiya ne ko ta kannensa,
A tausashe ya ce" Mamah shi ne kuma harda zubar da hawayenki?"
Mamah ta ce" Na rasa ta inda zan bilo ne, sai wani zuwa take tana shiga jikinka, bayan ni ba ita bace burina a game da kai"
A hankali ya ce" Mamah, zuwan da take yi ai ina ga zumunci ne, kuma idan bakya so an bar maganar kar hakan ya daga maki hankali Mama"
Mama ta zuba masa ido, yardarsa da wuri haka ya bata mamaki, a sanyaye ta ce" Kana nufin ka amince cewar ba za ka aureta ba?"
Kai ya gyada a ransa yana ayyana ' in ba mama ba dama ba wai auren na zauna da ita nake da niya ba, niyyata na shaku da ita ta yadda zan san wacce ce ita ko na fita daga zargin abin da ya kashe min matata, amma tunda hakan na daga maki hankali zan bar maganar tunda idan na sanar maki nufina zaki fi da tsorata da ita ta yadda zaki gaza boye mata'
Mamah ta sauke ajiyar zuciya tana dan sakin dan murmushi ta ce" To mata fa?

Ka san ai ya dace ka yi aure ko Babangida?"
Ido ya dan kikifta yana kallon Maman, sai kuma ya kaucewa maganar yana sako maganar da ya wuni da ita , dan a gaskiya irin maganar nan Maman tana da fahimta a kanta sosai, hasalima ita ce ta fara saka shi a lamarin nan har ya mata binciken nan, a nutse ya sanar mata dan abin da ya fuskanta da irin rikicewar Aban Ahmad da komai
Mamah ta so rikicewa dan mikewa ta yi tsaye tana sallalami da kyar ta koma ta zauna ta sake mikewa ta sake komawa ta zauna
A dan birkice ta ce" Kira min shi, ka min kiransa BABANGIDA dan kuwa da wahala na iya barci dan farin cikin wannan lamari, Baban gida Allah da iko yake, Fatimana mahaifinta baban mutun ne irin aban Mai sunnan Docter?

Idan kuwa haka ne lalle da yawa sai sun ji kunyar abin da suke yi mata idan suna da ita kunyar, "
BABANGIDA ya dan yi tsai yana kallon irin tarin farin ciki da rudani dake yawo a fuskar mahaifiyarsa ta kasa zaunawa dan abin ya daketa sosai, a sanyaye ya ce" Mamah, wai da so na yi na tabatar, so na yi gobe in sha Allah na je kauyen na bincika, kin san dan an yi katari kauyen ya zo daya ana iya samun ba su din bane, kar mu fara hawa zancen ba tare da mun yarda cewar eh shi din bane, Mamah kina gani fa har yanzu Aunty amarya ta kasa amsar Abanta ina tsoron shi wani irin haduwa zata yi da shi?

Yaya zasu kwashe?"
A hankali Mamah jikinta ya fara yin sanyi, tabas idan Nana ta nuna bacin ranta a kan wannan lamari abin a barta ta yi ne, bale irin yadda take daukan ire iren abin nan da zafi a zuciyarta?

Lalle sai an yi da gaske ko da ana son gannin sauki saukin fushinta
Muryarta a sanyaye bayan ta koma ta zauna ta ce" Ba laifi Abah, ka je ka binciko din, duk da ni kam zuciyata ta bani shi ne mahaifin Zahrana,Sai dai yanzu kuma ka sakan tsoron matar cen, Allah ya mata riko mai tsanani a zuciyarta, ina tsoron fushin da zata iya nunawa, duk da ya cencenci koma meye ta yi masa shi ya ja, amma ina tausayawa yarinyata, koma mene ne ni dai ta yi ta gama Zahrana kuwa ta hadu da mahaifinta ita ma hankalinta ya dan kwanta dan ni na san yarinyar a damuwa take sosai, bama irin yadda wasu ke sakota gaba a kan maganar kamar ita ta halici kanta ko ta haifi kanta!"
Irin kallon da yake yiwa mahaifiyarsa na fasara girman mamakin yanayinta a kan maganar yarinyar nan, sosai abin ke ba shi mamaki a kullum idan aka dan yi wani abu da ya shafeta,
Idannuwansa ya dan lumshe a hankali ya ce" Mamah, kina son yarinyar nan sosai, Idan ana maganarta har wani annuri ke bayana a saman fuskarki Mamah"
Mamah ta yi dan tsai da murmushinta, sai kuma ta fadada murmushin nata ta kamo hannunsa tana kallonsa a sanyaye ta ce" Ka san mene ne Abahn Docter?, Idan ina kallon yarinyar ina jin farin ciki a raina , ka san dalili?

Idan na ga tana murmurshi ko na ganta a halin sukunin zuciya na kan godewa Allah na kuma saka a raina in sha Allah ita ma zata zama y'a mai yanci wata rana kamar kowa, Abahn docter ka duba ka ga son zuciya da neman fitina irin ta dan Adam irin yadda yarinyar nan ke fuskantar tsangwama, babu tsangwamar da ta fi keta bawa ta saka bawa a halin kaka naka yi ko halin fadawa a halaka irin ta bawa ya tashi mahaifiyarsa na tsangwamarsa, tunda Docter ya kawo su ina kallonsu daga nesa ne har na fahimci asalin abin da yake faruwa,Abah hawaye na yi a ranar da na ganta labe tana cin abincin da aka rage aka fitar dan wankewa, Tun daga ranar na daukarwa kaina alkawarin in sha Allah zan kula da ita , zan kokarta bata tarbiya na sakata a jikina, zan koyar da ita jin kai, zan koyar da ita jin soyaya a zuciyarta ba kiyaya ba, zan bambanta mata a duniya ba kowa ne yake aiki da son zuciya ba,
Abah in ban da batan basira irin na matan gidan nan sai kace su basu haifa ba?

Mutun ya yi kokari ya yi ta kansa ya yi ta addu'a, Allah na tuba duniyar nan ta yanzu mai tafe da rudani kana yi kan ka da kafarkama yaya aka kare bale kana ire iren wannan izgilin?

Yau ko Fatimana ne ta haihu iyya abin da zasu yi mata kenan bale haihuwarta aka yi, magangannu na batanci kala kala, sai yanzu nema Allah ya taimakeni su Adawiya suka gane abin da nake nuna masu cewar su sakata a jiki y'ar uwarsu ce, yanzun kam Alhamdulilah zan ce sai fatan Allah ya nunan na sakata a dakin miji, kai ranar Abah sai na kwana ina sallah ina godewa ALLAH"
A hankali ya yi murmushi yana dan murza hannayen Mama kamar alamu na murza hannu dan ta ji dadin hannun,
Muryarsa a sanyaye ya ce" Allah ya cika maki burinki, ya shiryar maki da zuri'arki, ya shiryar da ita ya bata miji na gari"
Mamah ta amsa da Amen ya Allah, duk da a zuciyarta ita kadai ta san me take kudurtawa, a hankali ta ce" Yauwa Abah, mai neman Auren ZAHRAH, sai kun zauna da shi fa, ka san ba zamu dauki kasadar bashi yarinyar nan a rufe ba, dan gudun abinda ka je ya dawo, ka san mutane"
Da kula ya ce"
Da kula ya ce" Mamah, kamar yaya mu zauna da shi?"
Mamah ta dan sauke numfashi ta ce" Ka san dole sai an sanar halin da ake ciki, ba wai a tsaya a masa wani dogon bayani ba, aa , a dai sanar masa kawai wace ce ita a takaice, ka ga idan har son na ta yake yi zai aureta kuma zai rufa mata asiri ko iyayensa sai ya so zasu sani bale wani, amma idan aka boye ka ga maganar duniya tana fitar da kanta da kanta ne, idan ya ji komai na iya faruwa"
Kansa ya dan kawar gefe yana fitar da dan huci, A sanar da mutumin da ba'a da tabacin shi din wane ne, mai yake tafe da shi da gaske a zuciyarsa, kawai dai an san ya ce yana son auren yarinyar, a fito a fada masa wannan sirrin da yake jinsa a cikin ransa, wanda da yana da hali baki kaf mutanen da suka sani sai ya bi ya goge masu ta yadda zata wala ta yi rayuwarta irin na kowa cewar wai ita bata da uba?

Idan dalilin halan ya ki auren na ta ya gujeta fa?

Me aka yi ke nan?

Haka kawai ya ringa jin wannan maganar ai bama sai Hassan ya ji ba, a kan me zai ji sirrin ZAHRAH?

Wannan din ai abin rufin asirinta ne, babar magana ne da ba kowa ya dace ya ji ba, magana ce mai girman gaske da yake jin bai dace ta fita ba, namiji idan ya fito da nufin aure in dai namijin na gaske ne ai wannan ba zai girgiza komai a kudurinsa ba, ake zuwa a dauki macen da ta mayar da haka sana'a a kilaceta a aureta?

Balle wacce take killace take karkashin innuwar gidan DOCTER, take amsar tarbiya daga hannun Hajia MAMAH?

Bayar da ita a wajensa alkhairinsa ne, samunta idan ya yi farin cikinsa ne, ba lalle bane a sanar masa maganar nan dan gudun zaman yau da gobe, namiji ne fa, idan wani dan abinsu ya hada su ya goranta mata fa?
Chapter 56 · 0% Book details