← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 110

Sashe 36

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan kar ki sake kirana, idan ma kin kirani ba za ki sameni ba, zan bar garin nan da kuma canza layuka na duka."
Ya na gama fa
an hakan ya juya da sauri ba tare da ya kula da yanayinta ba, Fatima da ba ta
arasa fahimtar zancenshi ba sakamakon fita hayyacinta da ta yi, idanunta a kakkafe suke a kanshi, ba za ta ce hawaye take zubarwa ba, dan kuwa kalaman na Ma'awuya dai dai suke da jinin jikinta ma ya tsitsaye ya barta.

Tunda ta ji saukar guduma a kanta mai
arfin tasirin da ta dakatar da gudanar jinin jikinta, bugu da
ari ta hana hancinta sha
ar iska, sannan ta kasa fito da wanda ta sha
a a gaba
a wunin yau, daga zuciyarta ta san yau ita ce ranarta ta
arshe a duniya, dan suka alamomin fitar rai sun bayyana a kanta a yanzu.

Luuuuuuuuu!

Ta yi baya ta fa
i saboda komai na jikinta ya daina aikin da zai anfaneta ta iya gabatar ma kanta da wani abu komai
antarshi... *Waya* ce a kunnenshi ya na amsa muhimmin kira, dama kuma idanunshi a kan komai da ke faruwa suke, bai san ya aka yi ba wayar ta ku
uce da ga hannunshi ta fa
asan motar, Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!

Idanunshi a tsaye suke a kan shemammiyar amanar Ummanshi, ba tare da ya bi ta kan wayar ba hasalima kamar ya manta da lamarinta ya bu
ofar ya zuro
afarshi
aya a hankali ya rintse idannuwansa dan jin wani daci a saman lebensa na bacin rai...

Amir kuwa da ya ga haka da gudu ya fita daga motar ya nufeta, Ma'awuya da ya ganshi da gudun nan sai ya dur
ushe
asa yana
aga hannayenshi sama a firgice yana fa
in "Wallahi ba guduwa zan yi ba, babu in..."
Ganin Amir ya giftashi ya wuce ya sa ya juya da sauri, sai lokacin ne ma ya ga Fatima a kwance dan bai san ta fa
i ba, mi
ewa ya yi tsaye ya matsa kusa da su shima ya na kallon fuskarta daga nesa
Sunkuyawa Amir ya yi yana kiran sunanta, shiru ba motsi bare ya saka ran za ta amsa, da gaske dai suma ta yi?

Ko kuma mutuwa?

Tunanin mutuwar da ya yi ya sa shi sake rusunawa ya ya janye hijabinta ya dora yan yatsunsa biyu a saman wuyanta
A hankali ya sake zuba masu ido daga inda yake
Abinda yake hange ne ya saka shi jin sam hakan bai dace ba, kanta a fili Amir ya tsaya wani taba mata wuya
Sake zuba idannuwans aya yi ya ga Amir na tatare hannayen rigunnansa
A hankali ya fito daga motar, sai kuma takunsa ya zamo banban da fitowarsa daga cikin motar
a lokacin da Amir ya nemi talabota dan daukanta ya dakata jin an dafa hannunsa da hannun da ya kusan cike damatsunnan hannunsa
Daga agogon ya gane Baban gida ne, dan haka ya dago yana kallonsa
kallonshi Amir yake yi shi kuma hankalinshi na kan ta,
A hankali ya saka hannunsa daya ya dago kafadarta, sannan ya talaba da dayan ya daukota gaba dayanta a hannunsa gashin kanta ya warware yana yawo a hankali ya sauke dubansa a kan fuskar Ma'awiya, da idannuwansa ya masa alamun yana iya tafia, hakan ya saka Ma'awiya da sauri ya ringa godiya yana dukawa bayan Amir ya fasara masa ya fece kawai, sannan shi kuma ya yi sauri ya bude masa bayan motar ya shinfidar da ita a bayan ya mike yana dan yiwa yan daidaikun mutanen dake masu sannu yake sannan ya dan shafa gefen hancinsa kasa kasa ya ce" Adawiya ta gudu, kar ka ce mata komai, ka yi kokari ka cewa Mamah na aiketa ta wanke kwanonin gidana, kafin na kaita asibiti ta farka, idan kana tune ranar da mama ta ji ta tardo shi kuka ta yi......ba zan iya yafe mata ba idan ta sake lodawa kanta wani laifin.....ban san yaya zan iyay............mmm..........."
Sai kuma ya yi shiru kawai ya rufe motar da karfin da ya saka Amir ja baya yana kallonsa da mamaki , direban ya gyara zamansa ya sake nutsuwa, shi kuma ya zagaya ya bude gaba ya shiga ya kai hannunsa wajen sajen fuskarsa ciki ciki ya ce" CLINIQUE MARTABA!"
AMIR na tsaye suka warci motar suka wuce, ido ya karra budewa a bayane ya ce"
21 5 scnd
Amir na tsaye suka warci motar suka wuce, ido ya karra budewa a bayane cike da jimami ya ce" Ke kam kin shiga uku, dama a iya ni kika tsaya duka ne kawai zan maki, wa ya san wani irin duka yau zaki sha a hannunsa????

Rashin jin ki sai ya saka Baban gida ya taba lafiyar jikinki?

"
A haka ya juya a kafarsa ya nufi gida yana ta tunanin ama gwara da aka yi haka, sai yanzu hankalinsa ya idasa kwonciya, da farko ya yi zaton yayansu zai ba wannan banzan mutumen yarinyar nan, am yanzu ya fita daga wancen zulumin, yana kuma yi mata Adu'ar Allah ya hadata da mutun na kirki wanda ya san darajar iyali........... ai gwara a bata dan mutunci ba wannan banzan ba
Da wannan ya isa gida
Yana zuwa cikin dabara ya samu ya yi wuf ya tarda Adawiya kicin tana zaune ta yi tsuru tsuru, tunda ta shigo Mama na sallar azahar bata hau sama ba, tsoro ne fal a kirjinta tamkar zata yi fitsari haka take ji, sai da tace da Zahra kar a yi haka kar su sake tarda shi a wajen da yace ama Zahra ta nace, yau ta ja masu tashin hankalin da bata tunanin idan zasu fadi wani abu a yarda da su, basu da wata kalma da zata kwace su a yau
Shigowarsa ya saka ta mike da karfi gabanta na yankewa ya fadi tamkar zai faso daga kirjinta ya faso ya fito
A tsorace take kallonsa tana jan baya har ta hade bayanta da baban ma'adanar spice mai dauke da kwalabe kala daban daban shake da spice
Fuska a hade sosai ya ce" Sakarya, wai ke baba kece kika yarda har ta ja ki ko?, Ba laifi zaki fadawa yan garinku ne walahi ko ba yau ba, Baban gida yace a ce maki idan kin shigo kun hadu da Mamah ki ce ya aiki wancen yarinyar ta je ta wanko kwanonin gidansa ta hado a kawo, saura a wajen fadin ki yi gigin yankawa kanku kazar wahala, walahu na kwana ina dukanku bata ce min komai sakarkarun bamza da wofi da basu san ciwon kansu ba!"
Kai kawai take gyadawa jikinta na rawa sosai har ya gama ya fice a falon kwata kwata dan bayama so su hade da.

Mamah gaskiya
Sai da ta gama wanke fuskar kukan da ta ci na tsoro, ta yiwa kanta alkawarin gabanan ba zata kuma biyewa Zahrau ba, tunda ita ta zama sha dukar karshen zamani ita ba da ita ba walahi!

Jiki ba karfi ta fito ta ringa kwasar kayan tana kaiwa saman Mamah har ta gama sannan ta zauna tana amsawa Mamah tambayar ina Zahraun?

Sun jima fa daga zuwa nan da nan su siyo kayan bukata?

Da kyar ta iya fadin sakon kirjinta na dokawa, tana gama fada ta bar dakin danma kar a ja maganar Mamah ta fahimci karya ne ta yankata a dakin nan
____________________________________
Tun daren jiya FURERA ke cikin hali na tashin hankali
Fita take nema ido rufe, ama abin ya gagara
A yau ta yi tirr da yajin aikin malamai, ba dan komai ba sai dan ta san da ace ana makaranta hanya dubu gareta da zata iya gannin jikin yaa sayadi
A sace ta shige dakin mamansu ta dauko wayarta, dan a nata wayar ba cajin kati ta fito ta labe ta loda numbar Balaraba ta yi kira
Ya dan jima yana ringin ana ce mata Balarabar na cikin waya, hakan ya dan sake daga mata hankali dan bata so Mamanta ta yi cigiyar wayarta bata gani ba, tana iya dukanta a kan katin wayar nan, koda yake ta saba a kan wayar ta yi mata duka kamar zata kasheta,
Da kyar Laraba ta daga wayarta, sai da ta sauke ajiyar zuciya muryarta kasa kasa sosai ta ce" Haba auntynmu, ina kira tun dazu kina ta waya bayan ba wayata bace?"
Murmushi Laraba ta saki, domin aa duniyarta burinta ta ga an wayi gari ita Laraban gidan Auwal ta malaki burin zuciyarta, idan ta zamo mata a wajen Baban Gida ta san ta gama morewa, ba a anguwa da gidajensu kadai zata zamo mai mulki da isa ba har a cikin gari
Da murmushi a saman fuskarta ta ce" yi hakuri kanwata, ina nesa da wayar ne , yaya nake jin muryarki wata iri ne?"
Numfashi ta ja, sai ga hawaye na bin gefe da gefen kumatunta, muryarta na rawa ta ce" Auntynmu wai yaya jikin Yah sayadi ne?

Rabona da shi tun jiya da safe ya ce min yana fama da ciwon kai, shiru bana samunsa, bai yi kirana na, gashi na yi na yi na samu hanyar da zan dan fito na rasa, kin san yan saka ido da wannan shagun masu gadin da aka baza mana kamar wani gidan shugaban kasa an hanna mu motsi da ranmu, na so na dan leko na gaishe da Mamah sai na ga jikinsa ya gagara....."
Laraba ta yi mamaki ainun jin wai yayanta ba lafiya?

Sai kuma ta basar dan ta san soyayarsu shi da Furera kamar wasu Juliet da romeo,
Agogon hannunta ta duba, ita da kanta tana matukar son ta mayar da gidan Docter wajen zuwanta a kowani lokaci, ta tabata boyayoniyar da take yi da wannna bawan Allahn ba zata taba kaita ga ci ba, ana iya wayar gari ta ga abinda bai yi mata ba, gwara ta ringa giftawa ta samu ta saci zuciyar mamansa, kai Maman cema ke dan bata tsoro, mata sai shegen fadan tsiya, ita kadai masifa take yi, in na dan shi na ita har ba zata ringa yi mata girki da wanki ba?
Chapter 36 · 0% Book details