← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 110

Sashe 27

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da sauri ta karasa bayi dan daura alwallah ta fuskanci alkibla ta sanarwa ubangiji damuwarta,, ta tabata ko menene zai sanyaya mata
_____________________________________
"Baba, ihun me Zahra ke yi dazu?, Na san uwar na cen rai bace ina fata ba Amir din bane ya sake zane mata ya'ya?" Abah ke tambayarsa da kula bayan sun zauna a wajen hutawar Aban sun tatauna kan maganar auren da ya zo masa da ita nasa
Dan shiru ya yi, sai kuma ya yi murmushi yana kawar da kansa yana kallon dawisun da yake son yawon dare a hankali ya ce" Laifi ta yi ne inaga"
ABAH ya yi murmushi shima ya cire kansa bai takura shi sai ya sanar masa ba, dan ya tabata ya boye masa wani abin ne kamar yadda ya saba boye masa dukkan abinda zai iya daga masa hankali matsawar hakan ba zai gagareshi tarewa ba
A tausashe Baban gida ya ce"
16. 5s
A tausashe Baban gida ya ce" ABAH, nace, idan har yarinyar nan tana da tsayaye me zai hanna a hade aurensu da na su Rukaya?"
Docter ya dan zuba masa ido yana jan carbinsa, ya dakatar yana dan sake dubansa ya ce"
Wai Fatima?"
Kai ya dan gyada yana duban Aban
Abah ya yi dan tsai sai kuma ya ce" To a sanina dai bata da tsayayen, ama idan har akoy shi, zan fi kowa farin cikin hakan Baba, sai a hade da na yan uwanta, tunda ai ta isa auren a irgena zata kai shekara goma sha tara yanzu zuwa ta ashirin ai babana, ka san dama ni bana ra'ayin yiwa ya'ya miji, ya'yan yanzu idan ka masu haka zasu tabatar maka sunna da nasu ra'ayin, daidaiku zasu zauna, da na so na hadata da dan gidan Elhaj Nasiru, sai kuma nace bari dai na dakata"
Baki ya dan tabe, shi kam yana mamakin wani abin wani lokacin, sai dai ba mamaki tunda adini ne ya tanadar da hakan , ba mamaki, ama shi kam a shekara ashirin bai ga mace ba gaskiya sai shiririta da shirme, sannan baya cikin harkar hade haden nan sam, salon abu ya zo ya ki dadi a ringa cewa wane ne dai ya hada
A tausashe ya sake kallon Abah, ya sake budar bakinsa ya ce" Abah, saura kwana hudu tafiyarmu ko?"
Murmushi Aban ya yi, yana kallon kafarsa......, Wato ciwon kafar nan na bashi tsoro, sai kuma ya yi hamdallah, ko menene ai an mora rayuwa, ciwo ne dai kulun gaba yake yi, yanzun gaba dayanta kafar idan ta sandare sai an taimaka masa ya zauna, idan dare ya tsala wani lokacin rintsawa sai ta gagare shi saboda zafin ciwo, mahaifiyar yarinyar nan bashi da abinda zai ce da ita sai godiya, daga Mamah sai ita a cikin matansa masu zama su taya shi jinya bakinsu alekum, abinda ya sa yake jinjina mata yarinya ce ama kuma ta daukarwa kanta jinyar tsoho
Sun dan karra zama har kusan takwas da rabi ya mike ya yiwa ABAN rakiya har falonsa sannan ya masa salama ya tafi ya bar Aban da niyar fara kaima Allah kuka a kan maganar da Baban gidan ya zo da ita cewar yana so a hade aurensa da na yaren nan da yayar matarsa, bai taba tunanin zai yarda haka ba, haka kawai yake tunanin da wani abu a kasa, duda bai nuna masa ba, bai sanar masa da komai ba, bai kuma bashi damar fahimtar komai ba, ama shi ya haifi Baban gida, yana iya gane lauje cikin nadin harufan bakinsa, yana iya bambance me yake nufi da kalaman bakinsa ko da motsin hannayensa......., Ya san abu ne mai wahala namijin da ya saba rayuwa da mace jure wani dan lokaci ba mace a gefe, sai dai kuma abin nan ya tsaye masa a rai, da wannan ya haye sama da niyar kaima wanda ya saba share masa kukansa ba tare da gajiyawa ba,
Gida suka wuce direct shi da direbansa da abincinsa a kwondo an rufe ruf a tsaftace, sunna karasawa Shafa'i da wutiri ya gabatar bayan ya yi wanka da alwallah , ya ci abincinsa sannan ya kwanta dan neman hutu ya ajiye wayoyinsa a kunne baki dayansu dan bai cika kashe waya ba gaskiya, domin aikinsa ba aikin da zaka zo dan zaka dan rintsa ka kashe wayoyi bane, ana iya nemansa da kowani lokaci kan mahinmin abu
________________washe gari
Sai kusan karfe tara ya karasa wajen aiki
Yana zuwa suka shige meeting da ma'aikatansu, sunna gama wannan kusan karfe goma sha daya ya je amsa kiran Minister na army suka shiga wani aikin mai zafi kan mutanen da za'a tura jeji , ba shi ya baro wajensa ba sai kusan karfe uku na yama, a cenma ya ci abincim rana dan an kawo masu abincin ya kuma ga da tsafta sosai
Yana dawowa office ya sake tsayawa kan takardun da sekatariyarsa ta kawo masa dan saka hannu, kasancewar sai ya san me takarda ta kunsa yake saka hannu ya dauki dan lokaci har lokacin sallar la'asar ta shigo ya ajiye takardun ya mike ya nufo masalacinsu ya gabatar da sallah, suka fito sunna dan zantawa da manya manyan dake nan basu tafi gida ba har ya dawo wajen office dinsa ya sake shigewa yana mika hadi da salati
sakariyarsa ta biyo shi da girmamawa tana sanar masa wa'inda suka yi kira dan son gannawa da shi sati biyu da suka wuce, a nan ya dauki mutun biyu kadai dan abubuwan dake gabansa da yawa , ya ci gaba da aikinsa hankali kwonce
Yana tsaka da yi aka sake yin kiransa aka sheda masa Amir din ya zo, ya bada damar ya shigo da bakin nasu
Jim kadan Amir din ya shigo kasa kasa yana fadin" Ka kama kanka kar ka yi masa ihun da kake yi a cen walahi wannan ya fi ni dukkan abinda kake tunanin na tara na halaka munafuki irinka, shi nasa a boye yake ne tsaf zai iya aika ka kiyama wawan banza"
Gaba daya a jigace yake, ya yi jina jina kamar an saka shi a cikin bakin mai an fitar, harta rigar dake jikinsa ta gayu ta yage, sai hade hannayensa yake yi yana saka su a tsakanin kaffafuwansa yana kuma fitar da su yana zarro kwala kwalan idannuwansa da yinwa ta sake fitar da su, danma ya ci Sa'a yanzu da zai kawo shi ya bashi masa hudu ya ci , shi kam ya tsinewa soyayar nan da ta kawo shi wannan rayuwa a yau,mema ya yi ne da zafi jama'a?

Dama sai da ya ji dar din aikatawa abokinsa ya bashi kwarin gwuiwa, idan shekara zai yi a nan kuwa babu wanda zai damu ya sani ne ba wanda zai neme shi
Sai da ya gama mayar da takardar da ba zai saka hannu a cikinta ba ya dago ya fara kallon Amir da ya sara masa tun dazu yake tsaye yana jira ya bashi wajen zama a tausashe ya bude bakinsa zai ce Bismillah su zauna mana ya zubawa Ma'awiya ido yana kallonsa sai kuma ya kalli Amir da ya sada kansa a nutse ya ce" Wannan kuma me ya same shi haka?"
Amir ya kalle shi, ya kalli Baban gida ya sada kansa ya ce" Ya ki ya sanar min me yake nufi da Zahra ne"
Kuka Ma'awiya ya fashe da shi yana zubar da gwuiwoyinsa kasa kansa a kasa ya ce" Na bi Allah na bi ku, Oga ka sanar masa Walahi Walahi dan yatsanta ban taba tabawa ba bale a kai ga wani abin, kuma na sanar masa ban zo dan lalaci wa Fatima ba, ama ya ki ya yarda, ku rufa min asiri ku salameni in sha Allahu ko labarina ba zata kuma ji ba bale har mu hadu, ko ta waya daga nan zan taune layina na hadiye da yawun bakina, dan kuwa ba zata kuma sannin an haliceni a duniya ba, dama tsautsayi ne ya biyo da ni ta hanyarta dan Allah ku rufa min asiri ku salameni na je gida na tarda babata na tabata tana cen a halin kaka naka yi dan bana kusa da ita"
Magana yake yi, shi kuma yana kallonsa har ya dasa aya
A nutse ya ce" Soyayar tata ce kake kira tsautsayi?

Soyayar da ta sakata fitowa kai kuma zaka dauketa ka bata wajen zama ce kake wulakantawa?

Dama ba soyayar kuke yi ba kennan?"
Sake rushewa ya yi da kukan da ya saka BABAN GIDA lumshe idannuwansa a kausashe ya ce" Ka min shiru da shewa kamar wata mace a nan!

Rufe min baki ka dawo saman kujera ka zauna mu yi magana!"
Da sauri ya zarro ido yana toshe bakinsa da hannayensa yana fadin" Toh, toh, Allah ya baka hakuri toh yalabai Allah ya huci zuciyarka"
Ya fada yana karasawa wajen kujerar, maimakun ya zauna sai ya dan dosanu hankalinsa du ba a jikinsa ba, ya yi wani iri kamar zai haukace, wai a gaban dan Adam kennan, ina ga bawa ya je gaban wanda ya halice shi?

Takardun ya mayar gefe sosai ya hade hannayensa waje daya yana dubansa , ina anfanin rashin ji jama'a?

Me dan Adam zai maka da zafi wanda Allah bai maka ba?
Chapter 27 · 0% Book details