← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 110

Sashe 34

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan kennan
Sallar asuba ta gama ta nade kaffafuwanta a saman salayar ta dauki wayarta ta sake shiga neman layinsa
A hankali ta ajiye tana jin hankalinta fa ya fa fara tashi da shirun nan na MA'AWIYA, kiransa take yi yau kwana biyu kennan bata samu, ta san basu same shi ba dan ya gudu ai, kuma ta san zai kashe wayar ne dan gudun kar su same shi da wuri, ita tana so ta same shi ne dan ta masa albishiri din da
ansu yace cewar ya turo magabatansa a hade auren da na su Rukaya, tana matukar son jin irin ihun murnar da zai yi, har imagine take yi irin farin cikin da zai shiga.............

Murmushi ta yi tana sauke ajiyar zuciya ta mike tana ninke salayarta sannan ta shiga gyaran dakinta
Yau itace da girki, ga kuma aikensu da za'a yi
Tana son fita aiken dan yau duk rintsi sai ta nemo inda yake dan ta masa albishir din, ta tabata Adawiya ba zata hannata nemansa ba
tunda maganar aurensu zata kai masa, itama tana rufa mata asiri ai a zamansu na yau da kulun, so take yi a yau ta sanar masa dan ya maida hankali a yi a yi maganarta itama..................bata jin tsoron a san ta neme shi yau, dan ai a kan gaskiyarta take, da wannan ta shiga aikinta da karfin jiki tana kafkaf dan ta gama su tafi ta hadu da burinta ta sanar masa sakon da sai ya fi kowa farin cikin ji, Mamah tace ta lalabashi ya kawo?

Mamah bata san burinsa bane?

Dama matsalarsu muhali, ita bata da damuwa zata zauna a dakin mamansa har ya gama ginnin, ko ta yi zamanta a nan wajen Mamah har ya gama sai su tafi..................
20 dakika
A ganinta idan ta sanar da shi wannan albishir zai nemi ganin fuskarta dan ya ga kalar nata farin cikin, hakan ya sa ta ca
a adonta, ba wai irin ado na jan baki da hoda ba, iya kwalli ne kawai a idanunta, sai fuskarta dake fitar da
yallin mai
on da ya kasance halittarta ce haka, wanda ke alamta ba ta da busashiyar fata, sai man le
e da shima ta shafa bakinta na ta
yalli, hijabinta ta saka dogo har
asa mai hula biyu, take kyawunta da kamalarta suka bayyana.

Kasnacewar babu turaren da za ta yayyafa a jiki, dole ta
auko anbur
in da take sakawa a
ashin kayanta wanda ko ba ta shafa turare ba ma ya wadatar, haka ta samu ta gogashi a bayan kunnenta da wuyanta da duk wani matse matsinta sannan ta fito ta samu Adawiyya na jiranta.

A nutse ta
araso suka idasa kusa da Mama da ke zaune su ka gaya mata sun shirya, takardar hannunta ta basu tare da fa
in "Sai ku kula da kyau, kun san akwai wa
anda idan su ka ji na aikeku za su min kallo ne mai kama da saukar mari, dan haka ku hanzarta ku dawo min gidan nan, kun ji?"
Fatima jinjina kai ta yi Adawiyya kuma tace "E Mama."
Kama kunnenta ta yi ta sake maimaita "Kun ji da kyau?"
Tare suka sake amsawa da "E Mama, mun ji."
Gyara zama ta yi tace "To, Allah ya tsare, sai kun dawo."
Hanya suka kama suna amsawa da Ameen, saida suka
acewa ganinta sannan ta sauke jiyar zuciya, kuma har lokacin fatanta a kansu shine dawowa lafiya.
....

Tun fitarsu daga gidan take ci gaba da kiranshi, har yanzu da suke
aukar abubuwan da aka turosu siya a babban mall
in, rabin hankalinta ya fi karkata kan kiran masoyinta da burinta kawai shine ta masa babban albishir d'in nan da ta fi kowa sanin zai sumar da shi dan da
i.

Waina idon da ta yi ta ja tsakin da ke fito da ainahin damuwarta ya sa Adawiyya juyowa ta kalleta, matsowa ta yi daf da uta ta dafa kafa
arta tace "Zahra, lafiya ki ke tsaki?"
Kallon Adawiyyar ta yi ta sake
an jan guntun tsaki, aje kwalin cornflakes
in da ta
auko ta yi ta fuskanci Adawiyya da kyau, ba za ta iya
oye mata wannan tashin hankali ba, ko ta na da zurfin ciki a rayuwa ba dai a abinda ya shafi Ma'awuya ba, dan haka za ta fa
a mata wata
ila ta taimaka mata, dan in har ba ta sameshi ba, to tabbas daga nan wajen duk da ta san za ta sameshi za ta nufa, ko da kuwa hakan na nufin ta kwana tana nemanshi a garin nan, dan ita jikinta ba lafiya yake bata ba gaskiya.

Cike da raunin murya tace mata "Adawiyya, kinga ke yar uwata ce ko?

Yaya Ma'awuya ne na ke ta kiranshi yau kwana na uku kenan, amma har yanzu ba'a samunshi, kina ganin lafiya kuwa?"
Numfashi Adawiyya ta sauke tace "Ina ganin lafiya lau, kuma idan ya damu da ke ai zai kiraki?"
Kamar za ta fashe da kuka ta yi sauri tace "Ba haka bane Adawiyya, ni jikina yana fa
a min ba lafiya ba, bai ta
min irin haka ba fa, gaskiya ni a dame nake sosai...kawai ina ga."
Kallon tuhuma ta mata tace "Kawai ki na ga me?"
Ba tare da kowane fargaba ko shakka ba ta dafa hannun Adawiyya tace " Ko za ki rakani mu je ind..."
Adawiyya ba ta bari ma ta
arasa ba ta ja baya tace "Subhanallah!

Zahra kin manta me ya faru ne?

Ko ki ke Yaya Amir ya kashemu ko?"
Idanunta taf da hawaye ta sake ri
o hannun Adawiyyar ta ce "Ba zai sani ba yar uwata, kinga wallahi b za mu jima ba, kuma idan ban gaya masa abinda ke faruwa ba, ta ya zai san halin da ake ciki?"
A hankali Adawiyya ta girgiza kai tace "Gaskiya ba zan je ba, ki sake kiranshi dai a waya, ko ki kira wani da ya san shi."
Sake girgiza mata kai ta y da yanayin rarrashi tace "Ba za ki gane ba Adawiyya, ni wa na sani na shi, ko Mamanshi ma ban ta
a gani ba."
Cike da rashin damuwa Adawiyya ta ci gaba da
aukar abubuwan da suka zo siye tana cewa "Gaskiya sai dai ki yi ha
uri Zahra, kullum ina taimaka miki game da abinda ya shafi tsakaninki da shi, amma yau kam ba zan iya ba gaskiya."
Cikin jin haushin ba ta samu yadda take so ba tace "Shikenan, tunda ke ba ki ba ni zan je nemanshi"
Juyowa ta yi ta kalleta tace "Wallahi ke ma ba za ki je ba, dan ba zan barki ki je ba Zahra, kuma kina tafiya zan kira Yaya Amir na gaya masa kin gudu."
Kamar za ta sha
e Adawiyya haka take ji, me ya sa za ta mata haka?

Ko dan ita ba ta san me ye so ba?

Shin ba za ta fahimci irin abinda take ji a zuciyarta ba ne?

Wai me ya sa mutane ba sa mata adalci ne?

Ranta
ace kuma a daddafe suka
arasa wannan siyayya sannan suka fito daga mall
in, mota suka nufa inda dreba ya kar
o kayan hannunsu ya nufi mota da su da sauri, kamar daga sm suka ji wata nutsatsiyar murya an ce "Sannunku?" Ta bayansu.

A tare suka juya dan son ganin ko wanene?

Sai dai a take Zahra ta maida dubanta ga motar ta kama murfin ta bu
e ganin ba ta sanshi ba haka kuma ba ta ta
a ganinshi ba.

Adawiyya kuma da ladabi da kuma kulawa tace "Ina wuni?"
Da wani sanyayyan murmushi a fuskarshi ya amsa da "Lafiya lau, muna lafiya?"
"Lafiya lau." Ta fa
a ita ma tana matsawa kusa da motar ganin Zahra na neman shigewa, kallon Zahran ya yi da fara'a yace "Sannu ko?"
Sake juyowa ta yi ta kalleshi a da
ile fuskarta ba fara'a, dan a nan kusa kam ba ma wannan da ba ta sani ba, ko wanda ta sani ba ta jin za ta iya sakar ma fuska bare wani, cikin da
ilalliyar murya ita ma tace "Ina wuni?"
Cikin gyara tsayuwa ya amsa mata da "Lafiya lau, dan Allah zan iya magana da ke na minti biyu?"
Maganar fa Ma'awuya ake, ya ake neman saka mata wani tunani na daban?

Haba dan Allah!

So ake sai an ga gazawarta wajen yin ha
uri?

Haka ta daure ta cihe sosai tace "Ka yi ha
uri, sauri mu ke, kuma an hanamu tsayawa a titi."
Da sauri ganin za ta shige mota yace "Na sani yan mata, ko da na ganku kamalarku da nugsuwarku ta nuna min haka, dan Allah to ki ban lambar wayarki?

Idan ya so sai na sameki gida mu yi magana."
Saida ta ha
e fuska sannan ta gimtse baki tace "Bana da ita."
Daga haka ta shige motar sannan ta rufe k'ofar, wani irin murmushi ya yi ya kalli Adawiyya da ke shirin zagayawa ita ma yace "Yan mata, ke
awarta ce ko?"
Jinjina masa kai ta yi alamar e, dan haka ya sake yin murmushi ya na
an mi
o mata wayarshi yace "Dan Allah ki taimaka mana ki ban lambarta, kinga bai kamata na tsayar da ku a titi ba, dan alamu sun nuna daga babban gida ku ka fito."
Cikin ladabi tace "To shikenan, ka saka lambar zan gaya maka." Dan ba ta so ta kar
i wayar da hannunta, zayyana masa lambobin ta yi shi kuma ya shigar a wayarshi, da fara'a ya ce mata "Nagode ko, sai na kira
in."
Jinjina kai ta yi tace "To."
Har za ta wuce ya sake cewa "Wane suna zan saka?"
Murmushi ta yi tace "Fatima Zahra."
Murmushi ya sake yi shima yace "Fatima Zahra, ashe jan ajinta asali ya samo, tauraruwar mata ce."
Yar dariya kawai ta yi ta zagaya za ta shige mota, sai kuma yace "Idan na kira sai ki saka sunan *Hassan* a lambar."
a murmushinta ta yi tace "Lahhh!
Chapter 34 · 0% Book details