← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 110

Sashe 85

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kai Allah ya shiryi yarinta, shi fai ya tafiyarsa masalaci
Yau tunda ta tashi bata tsaya bata lokaci ba, tana gama sallah da azhkar dinta ta fito a hankali tana tunanin tana iya yin girkinma ta gama bai sauko ba dan ai a tunaninta safia ce bata san bakwai ta wuce ba yau kuwa zai fita da wuri sosai dan su mika wasu yan ta'ada hannun Shari'a daga nan kuma ya je wajen daurin aure, hakan ya sa tuni yana zaune a saman table ne ya rafka tagumi yana kallon saman da tunanin ko dai ya tafiyarsa?

Hankali kwonce take saukowa , a jikinta riga da dan karamin wando ne baki wanda ko gwuiwarta bai rufe ba, rigar ta sama ce mai dogon hannu ta kasan kuwa siririn hannu ne da ita, gashin kanta kuwa a jiya Auta ta since mata shi dan ya isheta a kitsen ta sake shi a jikinta tana tafe tana dan sosa wuya ne da sauransu har ta sauko da takalmi irin na yawo a cikin daki mai gashishika mai ruwan pink a kafarta ta ja ta tsaya a falon sanan ta dan wara kafa kadan ta yi mika a bayane kadan ta ce" Wayo Allahna marata ciwo ko meye oho?" Ta idasa tana turo baki sannan ta juya da niyar hawa wajen kicin din
Idannuwanta ne suka sarke cikin nasa, hannayensa bibiyu a dafe a habarsa ya rafka tagumi yana binta da kallo
Ido ta kwalalo ta juya da sauri tana hailala a bayane ta shiga hawa matakalar da dan gudu gudu rigar ta sake fitar da shap din jikinta sosai du idan ta dan haura kafarta daya sai daga baya rigar ta dan sake daguwa, wandon kuwa jira yake ta fara gudu da shi dama ya sake yin sama
Bawan Allah sai ya yi wani tsuru a zaunen da yake yana kallon table din, gaba daya sai tunninsa ya hade ya cakule
A hankali ya kai dubansa kan wayarsa dake ta tsuwa
Hnnunsa ya sak ya dauka yana dan bin jijiyoyin hannun nasa da kallo irin yadfa suka yi wani irin birde birde a jikin nasa kuma yanzu ne suka yi hakan
Dna tsaki ya yi na takaici ya kara wayar ya ki yin magana
"Ka ganmu zaune ni da lubabatu, ita tace ta fi awama a nan din ashe, ni din kuwa a kadan gaskiya zan yi minti ashirin ga kuma abincinka inaga aka kawo, mu shigo ne ko yayane?" Aban AHMAD ya fada yana kimtse tasa dariyar dan Lubabatu har talabe fuska take yi abinta
Bai iya amsawa ba , sai Hum kawai da yace ya katse kiran ya ki tashi ya bude masu, ai ba code din ne basu sani ba, wani launin a shigar masa hanci a dukunkune ne, kuma zai fyato su yanzun nan!

Luba ce ta saka numbar shigar suka shiga, ita tafara shiga da salama a bakinta
Tun kafin ta ajiye kwondon ta ji maganarsa da fada fada yana cewa" ke nu saanki ne?"
Da sauri ta kallo inda ya mike ya taho, hakan ya sa ta ajiye kwondon da sauri ta yi bayan Baban Ahmad da ya zarro ido yana kallonsa da sauri ya ce" Kai kar ka daki matar mutane mana, ni kuwa yanzu ai ba zamu yi kokowa ba ko?

Mema mukai maka daga abin arziki?

Ni fa zuwa na yi na fada maka yau zan tafi dan kamar ka manta rabona da kai tun ranar da na rakoka, ita kuma abinci ta kawo shikenan sai mu yi laifi dan mune sarakan laifi?"
Da harare ya ce" Freind ba dai ni kake wulakantawa ba?

Ni ko?

Ba damuwa ka ci gaba, lokacin da zan rama ba zaka iya gane komai ba, ka ci gaba!"
Ya karashe yana zaunawa saman kujera ya bude abincin ya dauki plate ya shiga zubawa, ita kuma Luba ta sidade tana fadin" Ruwan goran ba naka bane da madarar kar ka sha"
Banza ya mata har ta tafi, shi kuwa Aban Ahmad ya saki murmushi ya zauna yana kallon yadda yake wani matse matsen kaffafuwansa ya tabe baki yana kada nasa kaffafuwan ya ce" Ango ango, ango ka sha kanshi"
Kanzil bai ce masa ba, shi kuwa ya dora da fadin" Kai ama wannan gyara y kayatar da ni, ka ga dole a sake zuba mata sak haka a sauran bangarorin tunda ba kishiya wa bilahilazi!"
Shi dai ci yake yi, zufa na dan tsatsafo masa dan koshin nasa wata fitinar ce kuma, sai dai ba zai zauna da yinwa ba, sai da ya kusa koshi sannan ya dauki wayarsa ya yi kiran sakatariyarsa ya umarceta kan ta je ta sanarwa mai bi masa su tafi aikin nan ya makara yau zai je wani wajen mai mahimmanci
Yana kashewa ya idasa ci ya yi nakkk, sannan ya je ya dauko ruwansa ya dawo ya daga waya ya shiga kiran dakinta haushi sai sake tukarsa yake shi kuwa Aban Ahmad kallonsa yake harda su juyawa
Da kyar ta daga, muryarta a kurya sosai ta furta " Hello?"
Dan shiru ya yi, shiru na rasa me zai ce mata,
A hankalin shima sosai ya ce" Abanki ya zo"
Dira ta yi a gadon ta ce" Allah?

Wehhhhh"
Ya yi dan shiru yana jin kwaramniyarta da wayar a hannunta, kasa kasa sosai ya iya budar bakinsa ya ce" Ki saka sutura plz"
Daga haka ya katse ya juyo yana sauke kakausan kallo a kan Aban Ahmad domin ba sai an fada ba yana ji a jikinsa shi ya sakawa ido
A kausashe ya ce" Wai meye?"
Aban Ahmad ya girgiza kansa yana watsa hannayensa ya ce" Gani na yi ka murmuje abinka"
Takaici ya sake shakarsa, wai ya murmuje, yana zaman jiran Allah koro abincin tana cen tana yawo tsirara bata da aiki sai neman fitina da son saka mutun a uku ko tausayin kanta bata yi, tana wani yawo a haka tana bankare bankare da danyun abubuwan da basu nuna ba kamar wace zata iya da maza?

Kak, walahi zai yi gagawar raba waje da ita tun kafin ta saka ya aikata mata aikin ba daidai ba a masa wani kallon!

Yana tsayen sunna jefawa junna harara ta sauko fuskar nan tata tamkar gonar auduga, hijab dogo kawai ta zumbula saman abinda ke jikinta, yo kayan ne du haka suke yaya zata yi ita da ranta?
Chapter 85 · 0% Book details