← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 110

Sashe 6

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajia ta bud'e baki a nutse bayan ta ga ta gama sallar ta ce" Shafa'i da wuturi ne kika yi, ko nafila ne tun yanzu?"
A hankali ta juyo tana kallonya, a sanyaye ta ce" Nafila ne Mamah "
Hajia ta gyada kanta ta juya tana sake kallon kofarta ta ce" An fi son nafila idan dare ya tsala, a lokacin da babu hayaniya babu yawan kai kawo, a irin lokacin da wasu bayin ke barci kai ka kokarta ka mike ka gabatar, ka nemi lahira sannan ka nemi duniya, a irin wannan lokacin Allah ya fi amsar addu'ar bayinsa kin ji Zahra?"
Kai ta gyada tana sadda kanta
Hajia ta dan yi jimmmm ta ci gaba fa fadin" Ba zan taba gajiyawa da tunatar da ku baban abu mafi mahimmanci a rayuwar y'a mace ba, shine mutunci, Zahrah ki kasance cikin bayin da zasu rike mutuncinsu domin Allah, ko me kike ciki ki ringa fadawa Allah sannan kina kokarin kiyaye hakokin adinninki, ke mace ce, kina da daraja sosai, Allah ya yi ki mai rauni sai dai ya dora maki aiki mafi daraja a duniya, shine haihuwa da tarbiyantarda, idan ka tuna zaka haihu wata rana, zaka bada tarbiya sai ka sake kame kanka, ka ci gaba da kare mutuncin kanka, dukkan abinda sauran dunniya zata dubeka kuwa ko menene ka musu uzuri, mafi wawan cikinsu shine wanda ya shagala har ya manta cewa Allah baya kare halitar bawa da daina dora masa jarabawa har sai an saka shi a cikin kabarinsa, FATIMAH na san kina fuskantar abubuwa fiye da tunanin kwakwaluwarki, ki ci gaba fa addu'a ki daina kuka sannan ki rike amanarmu mu iyayenki, ki yi mana adalci, ki yi kokarin saka mana ta hanyar kare mutuncin kanki kin ji?"
Wani irin rauni ne ya daskare zuciyarta, da kyar ta iya amsawa Mamah har ta tashi ta fita ta rufo mata dakin tana sake kallon yannayin kofarta da tunanin lalle da wahala idan ba fita ta yi ba, sai dai tunanin ta ina ?

Ya dakata kawar da wannan tunanin ta ci gaba da ziyartar sauran dakunan yan matanta, su uku ne dama sai ZAHRA ta hudu, a cikinsu babu wace ta yi barci, wayama suke yi sai Ummi auta dake karatu dan tana fa exam gobe, dukansu kuma da sun ji alamun motsin hajiar sukan boye abinda suke yi ne, sarai tana fahimta, itama cikin nata hikimar take ta yiwa tufkar hanci da kuma tsayuwar dare tana rokon Allah ya kare mata, dan abu ne ya riga ya zama gama duniya, ko baka ba yaron waya ba za'a bashi a waje, Docter dai ne baya son zance, ba'a yi masa zance, idan ka tsaya da saurayi an kusa aurenku ne kawai, shima ba wai da dare ba, no, zaka zo ne da yama ku gaisa ka tafi, sauran maganar kwa yi a waya, shima ba wai masifafiyar wayar nan ba
Fatima Zahra kuwa, Mamah na barin dakinta ta samu kanta da fashewa da kuka har ta kasa zama da kyau sai da ta kwonta tana nade jikinta a cikin hijabi
Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, shin me yake damun kanta ne?

Me yake faruwa da ita ne?

Ko dai dan abin ya taba nasabarta ne ya sa yake bibiyarta?

Yaya aka yi yai har Ma'awiyah ya ci galabar sakata fitowa a irin wannan lokacin daga gidan shehin malamin da ake koyo da tarbiyar gidansa ta tarda shi?

Da ace ya daneta a cikin motar nan ya yi mata wata muguntar kuwa me zata dubi wannan matar mai daraja ta ce mata?, Yaya zata ce da matar da ta rungumeta bayan mahaifiyarta ta tsangwameta ne?

Ita ta san idan ta dauko abin kunya Allahn da ya haliceta da kuma Hajia sai Abah sunne wa'inda zata ji tsoron haduwa da su, shin menene wannan masifar dake bibiyarta ne?

Ita da kanta ta san tana yiwa Ma'awiyah son da ya dace ta daidaita ko dan rayuwa, shin idan har ya gujeta yaya zata yi kennan?

Yanzu haka tana tsintar magangannun da basu yi mata ba sam, idan abu ya sake rikicewa yaya kennan??

Da kyar ta iya samun barci, shima mai wartar nan ne mai wahala bayan ta yiwa kanta alkawarin duk rintsi ba zata kuma fita da dare haka ba, gwarama su rinha haduwar yammarsu kamar yadda suka saba in har ta ci gaba da kulashin wai!
_________________________________
A gajiye ya karaso gidansa, hakan ya sa bai leka bangaren matarsa ba, duda ya san sunna da baki yan uwanta da suke nan yau kwana hudu kennan
Wanka ya yi, ya saka jalabiya a saman karamin wando sannan ya fito dan zuwa wajen diner, domin shi a rayuwa baya wasa da lamarin cikinsa, sai kuma ya yi Sa'a ya fado kan wace take iya yinta a harkar girki, gaskiya bata da laifi a lamarin sarafa hannu, wannan ya sa yake girmama girkinta sosai
Yana zama ya shiga bubudewa hadi da zubawa abincin ido yana nazarin yau kuma wani sabon salon aka girka masa ne?

"Barka da zuwa mijin Manal" ta fada a lokacin da ta shigo take karasowa a hankali sakamakon ciwon da mararta ke yi tamkar zata zage gida biyu, kai lalle ta sarawa maganin matan nan na wajen yar uwarta, lahauli da ta sani da bata sha shi da wuri ba walahi, gayanan yana neman fasa mata mararta
Dan murmushi ya yi yana zubawa , bai ce komai ba har ta ja kujera ta zauna tana sake kashe idannuwanta da salon kisa irin tamu ta mata ta ce" Yaya gajiya, yaya aiki da fama da mu?"
Dan tsai ya yi yana kallonta,....tana acting like mai rikaken wayon nan, .....

Lokuta da yawa takan kwatanta irin halayan nan idan tana cikin bukatar wani abu mai girma ko tana son tafia mai tsayi......., Abin ya kasun masa gida biyu, na farko ya yi tunanin kirsa ce irin ta mata.......sai daga baya ya fahimci idan ta yi haka tana tunanin cin galaba dan ta girme shi da shekara biyu......, Shi kuma yana matukar jin dadin zuba mata ido idan tana irin haka, dan yana son hakan......ba dan komai ba sai dan karra karantar *WOMEN* da yake yi rana zuwa rana daga wajenta
"Oga, wai dog din nan bayar da shi zaka yi da gaske?

Bayan kana son sa sosai?" Ta sake fada cikin yannayi na tsantsar kisa, da layewa abu dan cinma wani abin irin namu na mata
"Yeah" ya bata amsa a takaice yana sake daukan abincin da ya masa dadin dandano a bakinsa ya sake kaiwa bakinsa ya ci..., Wato zai iya cewa zab'insa yana tafe daidai da tsamaninsa, ko yace baban kokarin zabinsa na kayatar da shi daidai misali........, Ta kasance wace ta ci gasar iya sarafa abinci......., Tana daya daga cikin manyan masu yiwa yan mata nasiha.................., Ba laifi tana yin iya kokarinta dan tafiyarsu ta yi karko, kuma yana yaba hakan
Sake sauke dan ajiyar zuciya ta yi, ta ce" Gani na yi du cikin karnukan nan babu wanda yake da kishi da iya ba ababen kiwon nan tsaro irinsa, ba'a isa a tunkari wajen kajin cen manya ba fa, sosai yake bada tsaro a wajajen nan, sauran sunna bin bayansa ne......"
Ruwa, marrar sanyi ya sha, a hankali ya lumshe idannuwansa yana adu'ar godiya ga Allah, hannunsa daya kuwa a saman shafafen cikinsa , tamkar ba a ciki aka zuba abincin ba, asalima idan kana kallon cikin sai ka dauka baya wani ci, dan gida gidan nan na masu gymn ne da shi, dama su in dai zasu rike shi dole sai da abinci mai gina jiki sosai, in ba haka ba kuwa akoy matsala
Manyan idannuwansa ya dauka ya sake dorawa a kanta, yanna kula da ita tunda ta shigo tana yawan dan tsamure fuska, sai kuma ta yi gagawar saki in ta kula zai dubeta
A hankali ya ce" Kin sha maganinki kuwa?"
Yannayin da ta shigo da shi na tabaci da sannin abinda take yi ne ya so kubuce mata, sakamakon tuna mata da ya yi a yanzu haka a irin zaman da suke zama ne dan an yi da wajewa ya buga ya buga itama ta ja ta ja cewar ta yarda ba maganar haihuwar, ba dan komai ba dai dan a lokacin aurensu basu je suka yi gwaji ba, sai a bayan aurensu aka tabatar da jinninsu irin jinnin nan ne mai dauke da cutar da idan suka haihu tare yaron na iya rayuwa cikin wahala, eh lalle abu ne na gwaje gwajen zamani, sai dai gaskiyar itace hakane!, Yaron na iya zuwa duniya da cutar nan mai karfi watau cutar kashi, ita ke dauke da mai karfin watau SS, shi tasa sunnan yana da ita ne kawai , kasancewarsa mutun mai kokari da sport da komai, sai ya zo masa da sauki, inma ba ya yi niyar tunawa ba akan mance cewar yana dauke da ciwon, damuwar daya ce idan har suka hadu suka haihu zasu samu yaro mai ciwon mai karfi, yawanci za'a zo a yo ta wahalar rayuwa da yaron, astagfrulah lamari ne na ubangiji domin da yawa sun take, wasun kuwa haka za'a yi ta fama yau da gobe, yau da gobe sai hamdallah, wannan abu da aka gani ya saka shi shiga tashin hankali a lokacin da ta ta
a yin wani bari, saima suka tsaya a matsaya guda cewar zasu tafi a haka....watau babu haihuwar, domin ya yi ya yi ya sawake mata ta nuna yanzu ta ga wajen zama, tana daukan magani ne na hanna daukan ciki, wanda ba kulun ba dan wani sa'in saima ta manta da shi kwata kwata, bama irin yanzu da yayarta ke cewa a kan me zasu yi haka?

Ta tabata Docter Ahmad bashi da labari, da ya sanar masu ai komai na Allah ne, itana ta san mijinta bashi da wajen gannin rauni irin yara, shi yasa ya zabi kar ya haihun a haka.

A sanyaye ta ce" Na sha"
Dan tsai ya yi, sai kuma ya kawar da maganar ta hanyar fadin" Auren su Aba karami ya tashi......"
Nan take yannayin fuskarta ya so cenzawa, da kyar ta iya kokarin kawar da maganar tana fadin" Oh wauh har auren ya tashi?
Chapter 6 · 0% Book details