← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 110

Sashe 14

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dana wannan lokacin sai matsalarta ta dan rage, harma ta amsa wayar saurayinta tana amsar gaisuwar da yake yi mata da neman izinin sake kiranta da dare, a nan ta amince suka yi salama ta yi zurru tana tunanin rayuwa....kai gwarama ta yi hakuri da fushin nan da take yi da Ma'awiya ko zai maida hankali ya nemi aurenta ta karra gaba, domin idan har ta biya fadan yaya Amir haka za'a zo a wanke yan matan dakin nan kaf tana gantali har a zo kan Auta, a lokacin ne kuma abinda ake mata ikirari zai tabata, watau Y'AR ISKA
Magariba na yi Auta ta sake zuwa ta kawo wanu abincin, sannan ta dauke kwanukan na ranar da sauran wanda ta rage dan ci da dare, daga nan ta sake sakin ranta ta fuskanci karatu kala kala dan samun nutsuwar zuciyarta, takan bude window ta zubawa masu kai kawo ido tana kallo, idan ta gaji ta koma ta yi kwonciyarta har aka yi kwana uku , aka yi Adu'ar sati, sannan gidan ya fara ragewar jama'a har ya zamto sai su ya su na gidan sai dangin marigayiyar
Yau kwana takwas da rasuwar, ra fito daga wanka tana ciro kayan wankinta da take so idan an rage ta kai ta zuba a machine
laver ta ji an bude kofar an shigo da salama
Da sauri ta juyo tana amsawa sai kuma ta yi saurin sada kanta sakamakon wanda ta gani.............
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_9_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
Da sauri ta juyo tana amsawa, sai kuma ta sada kanta sakamakon wadda ta gani atsaye tana yi mata kallon tuhuma
Mamah kuwa dake kallonta tawasali take sake yi ga ubangijin talikai, Allah da ya halici bawa, ya yi baki ya yi fari sannan ya kawata halittar su
Tabas Fatima Zahra tana cikin bayi masu kyakyawar hakita da nutsatsen zanen halita, tun daga yannayin tsarin halitarta har zuwa gashin kanta masha Allah ta keru , a dole zata sake dage mata da addu'a domin wani lokacin kyauma yakan janyo wata masifar idan ya yi yawa kuma aka ringa wasa da shi ba kula da kiyaye bakin duniya
Ita babu abinda ya dameta da wani nasabarta, yarinya fa bata da laifin komai, haihuwarta aka yi, idan ta fito ta wannan hanyar a hanyar zuwam duniyarma ta hanya rikitaciya watau a zamantowartama shegiyar ta rikitacen hanya ba yanna nufin an shawarceta ba bale har a tsangwameta, burinta Allah ya wanke miji ya bata na gani na fada mai adini da tsoron Allah ko masu kyamatarta sa ji kunya da tsoron lamarin ubangiji, sam bata so a cikin kadarar yarinyar wani mugun abu ya sake fitowa a tare da ita komai kankantarsa kuwa, shi yasa take kafa kafa sannan take yin addu'a da dukkanin karfinta dan ta san bata isa ta kare ba sai dai Allah ya kare mata
"Bana son gaisuwar, shin Auta bata sanar da ke nace ku ringa saukowa cikin mutane ba?

Ke kennan kin fi kaunar kauracewa mutane ko?

Ba zaki daina wannan banzan sabin ba ko?

Meye kike yi a dakin sati guda?

In na hayo da dare har kin yi barci, gashi da sasafe nake sauka a lokacin na tabata kina azkar, meye wannan sabuwar akidar ne?

Bana so fa"
Kanta a sade take ba Maman hakuri tana sheda mata tarin karatun dake gabanta ga sauka da ta yi ita kadai a dakinta, wannan ya sanyaya zuciyar Maman har ta umarceta kan ta sauko yau maza ta shiga kicin ta dama waina ta yi sadaka, ai ba'a yin sauka ba'a raka da sadaka ba
Da wannan Maman ta sauka, ta barta da zulumin sauka cike da tsoron kar aje ta sake hadewa da mahaifiyarta, duda ta san da wuya yau kwana takwas fa kennan da yin rasuwar
A kalla ta dauki awa sannan ta fito sanye da hija mai doguwar riga, irin hijaban nan na Turquie masu fadi da kyan gaske, ruwan kasa ya kama fuskarta dasss ya bude hananyenta a cikin hannun hijaban mai roba mai tsayi, ya dai amsheta sosai hijabin, kafarta kuwa dauke da safa fara kalll irin mai velours din nan mai kyau, sai dan sansanyan kanshin turaran da take yi ta idasa saukowa tana tafiya a hankali ta nemi nufar hanyar kicin din, sai dai bata kai ga nufar ba idannuwanta suk sauka a kan mutanen dake falon a zaune aka tataunawa, wace ta so juyawa ta koma, sai dai Mamah dake kallin hanyar saukowar ta ce" FATIMA wuce mana ki yi abinda ya sauko ki kina jan jiki ashe baki sauko ba sai yanzu?"
Dagowar mata ukun dake zaune suka zuba mata ido ya sake neman sakata faduwa, nan da nan kuma tsoron wanda ke zaune hankalinsa ba a kansu ba ya darsu a zuciyarta tana tunanin Allah ya sa ba shi bane a wajen
Da kyar ta iya aro jarumta ta karaso inda mutanen ke zaune ta duka kar kasa daf da Mamah muryarta a sanyaye ta ce" Barka da warhaka, yaya karin hakuri?"
Amsawa suke yi su dukansu, Mamah ta ce" Alhamdulilah Zahrah, kin ga mahaifiyar narigayiyar nan, ga yayarta ga kuma kanwarta........"
Sannan ta dube su ta ce" Hajia y'ata ce, sunnnata Zahrah"
Da kula suke sake gaisawa, a sanyaye take amsawa sannan a dari dari
Dan murmushi wace aka kira da yayar marigayiyar ta yi tana duban Hajia ta ce" Mamah na zata su Maryam ne kawai yan kannan nawa....................?"
Mamah ta yi murmushi ta ce" Baki santa bane, itama yata ce"
Sai kuma mama ta kalleta ta ce" Tashi ki je ki fitar da dukkan kayan bukatarki ki je kicin din filin gida ki ba baba ta gyara maki komai sai ki toya da kanki, nima ina jira kwanona maza yar albarka"
Kai ta gyada ta mike da dan sauri, domin dama kamar an wani daureta haka take ji ko dan mutanen wajen bakinta ne da kuma wanda yake dodo a wajensu baki daya?

Da sauri ta shige kicin din, sai kuma ta ja turus tana kallon ikon Allahn da ake yi a babar kofar kicin din ta baya, watau kofarsu ta aikata munafurcinsu daga boye, itane ake rufewa da gini bama da kofar ba bale su yi tunanin wata rana a bude
Dan gwauron numfashi ta sauke sannan ta shiga harhada kayan bukatarta gaba daya ta fito da su ta wuce tana mamakin hali irin na yayansu,
Yanzu zaman makokinma ba zai yi da manyan suturu irin ka su ABAH ba?

Kuma a gaban sarakuwarsa ne yake zaune haka kirji a aune yana binsu da kallo ido cikin ido,......uhum Allah shi kyauta
Mama dake kallon iyayen marigayiya da mahaukacin mamaki irin mai neman kashe bawan nan da kyar ta iya jan gwauron numfashi tana dauke dubanta ta maida kan Baban gida, sai dai yadda ta ga ya saka idannuwansa cikin na matar da aka gama magana a kanta tamkar yan giya yana kare mata kallo daga sama har kasa ya sakata jan dan numfashi hadi da yin alamun da shi take , kafin ya juyo dubansa ya daj zuba mata ido sai kuma ya dauke duban nasa ya mike tsaye ba tare da ya basu amsa daya ba ya dan sada kansa a hankali ya ce" Zan je office yau, sai na sauko"
Gaba dayansu sai wani katon shakunsa ya nemi kama su, banda Mama dake kallonsa a ranta tana tunanin hala tafia zai yi ya barta da basu amsa bayan ita bata san me yake tunani da wannan magana ta shirme ba?

Da kula ta ce" Baban gida ama ai magana ake yi ko?"
Fuskar mahaifiyarsa mai tarin ni'ima irin haske na fuskar uwa ya zubawa ido, sai kuma ya lumshe luhu luhun idannuwansa masu shige da na mashaya a nutsensa ya ce" Ku gama maganar Mamah"
Daga haka ya sake juyawa
Har ya kusan ficewa ya kuma jin muryar mahaifiyarsa a daf da shi, watau biyo shi ta yi a sanyaye ta ce" Kai, yaya zaka mike ka barni da mutanen dake zaune dominka kace wai na yanke hukuncin da ya dace bayan ka san ana iya yankewar bai maka ba?, Ni abinma ya girmami tunanina, su da suke da macen yau dududu kwana takwas da rasuwa su fito da wannan maganar?

Kuma yayarta bama wata kanwarta ba?

Ama ka fadi abinda ke ranka zai fi ka ji tunda kai zaka zauna da ita ba kowa ba"
Shi kam bai ga menene na jan maganar ba, ba yace a yanke hukuncin ba?
Chapter 14 · 0% Book details