← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 110

Sashe 42

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Auta ai ciwo bai san inda rai yake ba da ya yi barna sosai, abanku bashi da lafiya ne shi yasa zamu kaishi ya ga likita kwana biyu kawai zamu yi mu juyo in sha Allah kun ji?"
A bayane take gannin alamu na samun salama a fuskokinsu, sai kuma ta ci gaba da fadin" Yauwa maza ku tashi ku dauko kayanku ku kashe komai ku rufo dan rufe nan din zan yi maza ku maida hankali, ke rukaya ki daukowa Zahra nata ina son yin magana da ita maza"
Da sauri du suka mike suka nufi saman, ita kuwa Mamah ta fuskanci Fatimah ta ce" Zahrah, yaya maganar Ma'awiya ne?"
Sai da gabanta ya yanke ya fadi, a hankali ta sada kanta tana murza yan yatsunta hankalinta na sake tashi
Mamah ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Ke nake sauraro?"
Muryarta na rawa ta shiga fadin" Mamah, ban san abinda yake faruwa da shi ba, wai yace ba shi ba ni"
Mamah ta yi tsai tana kallonta, tana kuma nazarin maganar
Kai ta cire tana dantse lebenta hadi da girgiza kanta sannan ta ce" Ba damuwa, Allah ya hada kowa da rabonsa, sai ki dauki darasi gobe ki bi a hankali, Alhamdulilah tunda bai wulakanta min ke ba, ama ki kula gaba kin ji?"
Kai ta iya gyadawa tana share hawayen fuskarta, karfi da yaji ne take ture abin dan bata so ta saka a ran nata ya zame mata matsala da mutanen dake tare da ita har ta fita a ransu, sunna yin iya yinsu kar ta sa su yi watsi da ita gaba daya saboda halayanta, irin yadda ta ga a yau sun jata a jiki, ba zata so ta bata ba, zata so hakan ya dore sosai
Sunna saukowa Mama ta sake aika Rukaya dakinta ta dauko mata abinda bata dauka ba, watau man zafinta ta rufo dakin bayan ta kuma kashe fitilar da ta kunna sannan suka fito gaba daya ta rufe bangaren ta tsaya ta tofe da addu'a da fatan Allah ya dawo da su lafiya baki daya
Itace a gaba su sunna biye da ita suka nufi bangaren aunty amarya, wanda hakan ya saka Fatima jin kafafuwanta kamar ba zasu sadata da bangaren ba , gaba daya jikinta ya dauki bari hankalinta ya nemi tashi
Babu wanda ya tsaya biye mata har sai da Maman ta shiga yaran suka shige ama ita tana tsaye a kofar dakin tana kallon Mama da ta juyo ta wanka mata harara da fadin" Zaki shigo ne ko ba zaki shigo ba?"
Jikinta na rawa da kyar ta iya shigowar itama , dakin gaba daya ya dauki kanshin suyar dambun naman da take yi ba ji ba gani na yan tafiya , naman kaza ne dan Abah baya cin naman da ba na kazar ba saboda ciwon kaffafuwan
Katon abin tsanewar ta fito da shi ta ajiye a nan falon tana kallon Mamah hadi da dan sakin fuskarta ta ce" Mamah Bismillah mana kunne ke tafe?"
Mamah ta ki zama har sai da ta gama ajiye kayan ta sake dagowa zata yi magana sai ta yi shiru gannin wace ke boyewa a bayan maman ga kuma su Rukaya a gefenta ita din suka zubawa ido sunna kallo
Mamah ta fuskanceta sosai ta ce" Zuwa na yi neman alfarma, ko za'a kular min da Y'ayana kafin Allah yake dawo da mu?

Ina nufin a nan bani da wace zan kai wani wajen idan har za'a iya amsar min a amshe su baki dayansu ?

Ko zaki iya amsa ki kular min da zuciya daya ba hantara ba zagi ba wulakanci?

Ko dai na kara gaba da abina?"
Fuskar Mamah ta tsure da kallo, sai kuma ta sada kanta, ta dauki lokaci ainun bata dago ba har Mamah ta saka a ranta ba zata amsa ba dan haka ta juya da yaran tana fadin" Shikenan ku wuce mu je dayan dakin ko a dace.............." Sai ta ji muryarta a sanyaye ta ce" Mamah"
Mama ta dakata ta juyo tana kallonta, sai kuma ta ga ta yi shiru bata ce komai ba
Mama ta ce" Ki yi magana mana Nana kik ga lokaci yana matsowa ai na san inda na barsu kafin mu tafi"
A sanyaye sosai ta ce" Sunna iya zama, Allah ya bani ikon kula da su"
Mamah ta lumshe idannuwanta sannan ta kamo hannun ZAHRAH dake ta boyewa ta fitar da ita daga bayanta ta turata kusa da Rukaya ta ce" Maza ku je ku samu wajen kwonciya dare ya yi, sai mun dawo in sha Allah"
Ko Auta bata nuna tarin damuwar da Zahra ta nuna na rabuwa da Maman, kuka ne kawai bata fashe da shi ba, haka itama Maman a bayane zaka fahimci kamar ta fi jin barin Zahran fiye da kowa, ba dan komai ba sai
dan tunanin dake ranta na irin kyamatar yarinyar da ake yi a cikin familly din
Maman na tafiya Aunty amarya ta ce da yan matan su je sama su zavi daki su gyara su kwonta , zata je ta kai kayan yan tafia ta dawo
Har sauri take yi wajen rigayarsu hayewar dan du tsoro take kar a barta a baya ta wartota ta koreta bayan Mama bata nan ina zata nufa?

Sunna shigewa dakin da suka zaba ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, hakan ya matukar ba yan matan tausayi har suka sake daukar niyar sake kusanta kansu da ita dan su kyautata mata su kuma taimakawa rayuwarta
Dakin bashi da wani dati, gado ne mamakeke sai kayan shinfida manyan barguna a cikin sif
Zannin gadon kawai suka cenza masu yin wanka suka shiga wa'inda basu yi shafa'i da wuturi ba suka daura alwalllah suka gabatar sannan suka layu saman gadon nan su hudu suka yi kwonciyarsu ba doguwar hira dan kowa da irin zulumin dake cikin zuciyarsa
Karfe daya da rabi suka kama hanyar a
roport, Abah da matansa da Baban gida sai amir wanda zai dawo da su
Basu juya gida ba sai da jirginsu ya daga karfe biyu da mintuna sannan ya mayar da su gida shima ya je bangaren samari ya yi kwonciyarsa dan ba zai kuma fita ba ya gaji sosai......................
___________________________________
Wani tsanin mai sakawa a tarda wani
Tunda yan matan Mama suka tare a bangaren Aunty Amarya harta yan aikinta sun zamto ne hoto dan ko dauke tsinke basa yi...., A yanzu ne ta fahimci dalilin da ya sa kwata kwata Mama bata da masu aiki dan yarenta ba dai aiki ba, sam basa gajiya da gajarniyar dauke cen dauke nan, bama wace ke so ido rufe sai ta san da zamanta sai ta fahimci tana kokarin itama, duda tunda ta zo bangaren maganar fatar baki bata taba hadata da ita ba, ama kuma ba zagin nan, ba kora, sai dai kuma ba gyara kayanka, asalima itama bata gigin gaisheta dan ba zata taba manta gaisuwar da ta yi mata ta yi rantsuwar idan ta kuma gaisheta sai ta wanke fuskarta da mari ba, ita a yanzun tana kiyaye dukkan abinda zai daga mata hankali fiye da komai, tana kuma hangen matar dake matsayin mahaifiyarta tana kare mata kallo, kamanin Aunty amarya ne tsaf a fuskarta, komai nata ne ta yo sai fari da ta fita, dan gaskiya farinsu bama iri daya bane na aunty amarya mai ja ne, nata kuwa mai haske ne fatttt din nan
Tsakaninta da yan uwanta zata iya cewa itace sabuwar rayuwar da ta tsinci kanta a ciki wace ta taimaka mata har ta ki neman Mu'awiyah
Shawara suka yi a tsakaninsu ne?

Yaya suka yi suka kai wannan waje?
Chapter 42 · 0% Book details