Sashe 71
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ji take yi tana mugun sonsa har bargonta, sai dai kuma da sauki kan irin ciwon da ta ji a kan Ma'awiya, bata ji zata iya guduwa ko ta tarda shi ba, batama ji in zata iya kiransa kan maganar ba, karshema tana kallo Rukaya ta dauke wayarta ta tafi da ita bayan ta lulubeta da abin rufa tace da ita idan ta gaza barci ta tardota dakinta, in kuwa karatun Alkur'ani zata yi ta yi karatu, in kuwa tana son kallo ta zo su kunna ko su yi fira ko su yi kunshi, duda yanzu rabonsu da yin kunshi tunda satin aure ya rage sato uku, Lallen ne Mama ta yi hadi da shi shi kadai ta cikawa kowace ya zamto kafin ki shiga wanka zaki shafa a jikinki har kafarki ki zauna minti talatin sannan ki shiga ki yi wankan da ruwan dumi, hadin lallen Mamah ta yi shi harda su turaruka fatar jikinsu du ta dauka, ga kuma wani magani da ta jika a katon randa irin na laka na gargajiya ya zamana shine ruwansu, tace maganin zahi ne, daga haka bata kara masu komai ba, wannan din kuwa ba komai bane sai sasake dan ya gyara masu mara ya rabasu da zahi da kannanun cutuka na yan mata, watau dai a boye tana gyara
anta ne da gyara mai daraja wanda zai anfanesu zuwa gaba
Idannuwanta kawai ta lumshe, sai take ji a zuciyarta tana matukar son ta ji dumi irin na uwa, tana so Mamah ko.....ko................a hankali ta lumshe idannuwanta hawayenta suka tsananta, inama ace tana da uban nan ?
Koda bai yanka mata rago ba, koda bai yantata ba, koda bai sameta ta hanyar tinkaho ba, itama dai ta ganshi ace dai yau ga wanda ya kawo ZAHRA duniya?
Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, tabas kunci bashi da dadi ko kaddan, Allah ya yi mata sasauci a lamarinta
Rukaya na rufe dakinta ta juyo ta saki wayarta sakamakon gannin Aunty amarya zaune ta kurawa hanyar shigowar ido tana kallo
Ajiyar zuciya ta sauke tana fadin" Lah aunty, ban san kina ciki ba ban yi salama ba, "
Tana fada ne tana kallon hawayen dake zarya a saman kumatun Auntyn, hakan ya so daga mata hankali
A hankali ta karasa kusa da ita ta zauna tana fadin" Aunty kuka kike yi?
Waye ya saka ki kuka Auntynmu?"
Tun a daren da aka yi abin nan da Aunty ta nuna ita bata haifi ZAHRA ba Mama ta zaunar da su ta sheda masu cewa kar wanda ya nuna mata irin girman nan na da da suke nuna mata tamkar mamansu, su zanta da ita kamar auntynsu, kuma kar wanda ya yarda ya kuma kamantata da mahaifiyar ZAHRA, daga yau Mama ce mahaifiyar Zahra ita kuma auntynta, saboda lafiyarta, sosai ta kwatanta masu abubuwan da suka basu tausayi ainun, kuma suka dauri niyar ce mata Aunty kawai, dama fa Aunty ba wata datijuwa bace, ba zata wuce shekara talatin ba inma ta kai, ai kuwa batama kai shekarun yayunsu mata ba
Hawayenta ta share tana ta sauke ajiyar zuciya a kai a kai
Da kyar ta iya budar bakinta ta ce" Wai wai shima ya daina auren y'ar MAMAH ko?, Ta sani ne Rukaya?
Tana cen tana kukan ko?"
Tabas wani irin tausayi da ya tsargawa Rukaya sai da ta share hawaye
A tausashe ta kamo hannayenta tana rikewa a cikin nata ta ce" Aa, bata kuka ai, Mama tace sai me Allah zai bata miji, tana cenma tana barci fa"
Dif kukanta ya yi tana kallon Rukaya, kasa kasa sosai ta ce" Ce Allah barci take yi?"
Rukaya ta yi dan shiru sai ta ce" Ni fa na kwontar da itama , tana barci fa, ko zaki zo mu je ki gani?"
Da sauro ta girgiza kai tana share hawayenta ta diro kaffafuwanta kasa da hannunta ta nunawa Rukaya tana fadin"Shiuuuuuuiiiiit babu ruwana, ba zan je ba, abindama ni ba Y'ata bace, y'ar Mama ce fa, karma ki ce kin ganni, na tafiyata kicin, ita ta sanima ta yi kukanta ai"
Tana fada ta fice a dakin, kana ganninta zaka fahimci ta samu salama a zuciyarta, sai dai abin nan shi ya saka Rukaya kuka, sosai ta yi kuka har ta gode Allah, lalle kowani bawa da irin salon kadarar rayuwarsa, ama maza masu yiwa
an mutane fyade su bada keya su yi tafiyarsu sunna tare da baban duhu mai wuyar fasara, a gannintama wata shari'ar sai a lahira
MAMAH na zuwa bangaren Maman Furera ta tarar da Maman na furera na waya , irin muryarta sama sama tana sheka dariya irin muguwar dariyar nan marar dadin sauraro
Tana gannin Maman kittr ta katse kiran tana zazaro ido hadi da fadin" Au Maman auta ce?
Bismillah mana Maman Auta"
Mamah ta yi murmurshi mai ciwo , bata zauna din ba tana kallonta ta ce" Au, Umaimat ce kike fadawa abinda ya faru tana tayaki farin ciki?"
Maman Furera ta dan kawar da fuskarta tana jin kamar ta tafka wani abu marar dadi, sai kuma ta juyo tana fadin" Mamah kema walahi da
orawa kai damuwa kike, To me wai kike jira ne da ita?
Ai sai dai hakuri kawai fa MAMAH gaskiya inma kin ga laifina so dai kika yi ki gani ai Mamah"
Mamah ta gyada kai tana murmushi, lalle zata so gannin fuskokin matan nan da
ansu idan abin nan ya fito, in banda batar basira da saka kai a ramin kai danka kake koyawa wannan muguwar dabi'ar?
Kai gaske Furera take ta baudewa a kan magana irin wannan, ba komai ai rayuwa ce
Mama ta ce" Hakane, dama na san baki san waye uban Zahra ba, shine nace bara na zo na fada maki, Zahra dai eh lalle an sameta ta hanyar da ba dadi, ama mahaifinta daga yau har ki gaza gani zakina ganninsa a gidan nan tare da ita, dan a gwuiwoyinsa ya duka yana kuka mahaifiyar Zahrah ta dube shi ta kiya, mutun mai daraja, mai girman daraja kuwa dan yau meye daraja a idannuwanku?
Kudi, mutun ne mai kudin gaske, kuma in fada maki sallarma dai yana yi alhamdulilah, tabacin Kadara ce da bata zarce kan kowa ba, ki yi ta kanki ki kuma ci gaba fa sake daka garin tarbiyar yayanki a haka, zaki girbi abinda kika shuka, in sha Allah idan Aban Ahmad ya zo ki tambayeshi wai shine uban ZAHRA?
Zaki samu amsa daidai da tambayarki, Zahra mai gata ce, rayuwa ce ta wahalar da ita take tare da ku kuke wulakantata, ZAHRA mai arziki ce dan ko a yanzu da zan fitar maki da dukiyar da ta malaka da sai kin summa, sai dai alkawarina ne sai ranar da zan mikata dakin miji na bata abinta, zata samu abinda ya'yan halak din basu samu ba, ki gyara zamanki da kyau, Allah ne ya tsaya mata ba mutun ba, kin ga kuwa dole ta hadu da jarabawa ama a tsaye take dirrr a kan kaffafuwanta gannin bayanta sai wanda ya haliceta!"
Daga haka MAMAH ta yi tafiyarta tana jin ta dan amayar da yar damuwarta kadan, ama ta sani ne sai ranar da zata wanke ZAHRA zata ji sauki a zuciyarta na wulakancin matan nan, ko a yanzu idannuwan Maman Furera ya nuna mata ta daku jin waye mahaifin ZAHRA, dole ta daku, mutun ne da ba kowa ya sanshi a cikin ahalin ba ama kowa ya dan kyautarsa, dan sai dai in bai zo ba kyauta daga ta tufafi har ta dukiya zaka samu ta mamaki, ko hira ake yi da marigayi in abinda ya shafi mutanensa ne kowa burinsa ya yi maganar kyautatawar Aban Ahmad, ta tabata daga yanzu har gobe da wahala ta iya shedar kirki , dan damuwa ce ai ta sakawa kanta sai hakuri
Tsabar kidimewa, nan Maman Furera ta zabura ta bar jakar kudin nan da ta amso daga wajen BABANGIDA ta yi cikin dakinta da wayarta ta ringa kiran numbar Umaimat har jikinta na rawa
Hankali tashe ta shiga labarta mata tashin hankalin da take hange, sun tsumu a hirar gabanta ya yanke ya fadi sakamakon tunk jakar kudin nan, hakan ya sa ta fito a guje har kamar zanin jikinta zai kunce ya fadi, sai dai kashhh, lalle ta yi sara da mutun a sama, kudi babu su babu dalilinsu, wannan lamari ya sakata saka ihu da kuka tamkar sabin kamu ta yi waje ta nufi bangaren MAMAH, kwata kwata ta manta irin dibar albarkar da ta tafka ta samu Mama tana kuka ta sanar mata tarin kudin nan an dauke babu an dauke daga shiga dakinta ta fito, ta sanar mata kwanakima an daukar mata dubu dari a kudinta, wannan abu ya taba Mama, ta kamu da tsoron me hakan yake nufi?
A cikin ahalin Docter?
Barawo?
Ko barauniya?
Me ya nema ya rasa?