← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 110

Sashe 53

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Hasan fa shi ya kawo kansa, maganar aure ake yi ba wasan boyayoniya ba, babu wanda yake tafia saman kai da zai tashi ya yi aiki irin na marar ilimi ya dauki y'a ya bashi a rufe, ko menene iyayenki ne zasu fuskance shi, kina abu kamar wata wace tale rayuwa ita daya, to ki kula kar ki ringa sakin baki da kai a gaban namiji, ko menene sunnansa namijin da zaki aura daga haka ba kari, zama kuwa ana nufin zama na sannin waye wa, yau da gobe, sannu sannu abubuwa sa ringa bayanuwa na halayansa da naki baki daya, a haka wasu suke kasa zama da junna idan suka gaza hakuri........., Koma menene ki kiyayi abubuwa kamar fadin laifin danginki a gaban mijinki, da sauransu, hakan ba daidai bane, ki bari manya su san ta inda zasu fuskance shi su sanar masa, Hasan dai ba shi ya yankewa kasa cibi ba, ba kuma shine karshen maza a duniya ba, bai fi kowani namiji daraja ba, in yana so in an sanar masa ya nuna baya yi, Allah zai baki wanda ya fi shi, tashi maza Babangida ke kiranki yana diner na kasa" Rukaya ta fada tana tare numfashin Zahrah bayan ta zabga mata harara
Ido ta zarro a dan tsorace ta ce" Ni kuma?"
Rukaya ta gyada kanta ta nufi wajen hijabinta na sallah ta dauko ta miko mata ta ce" Saka hijabin nan walahi maza tashi, ni dai yau nice da girki na gana tunda duku duku babu abinda na yi na laifi , na ganshi shi da abokinsa ne saman table, kin san ba gane fushinsa kake yi kai tsaye ba , fuskar dai yadda na saba ganninta ne , ta yiwu wani abu za'a tambayeki, ke dai maida hankali ki je
Idannuwanta ta sada zuciyarta na dokawa sannan ta amshi hijabin ta zumbula ta sauko gaba dayanta tana barin wayarta a nan
Maimakun ta bi bayan Rukayar a guje sai ta nufi dakin Mamah, dan in dai Mamah na nan babu abinda zai sakata gangancin zuwa kiran Babangida ita daya kamar wata wace aka cewa jeki kya gani, wama ya san girmaman laifin da ta tafka aje ya shiga zaneta kafin Maman ta ji ta sauko ya halakata
Tana zuwa ta tarar Maman bata nan, hakan ya saka ta idasa sarewa ta nufi bayin Maman ko zata yi koda fitsari ne, dan kar aje ta sake shi a gabansa
A kasa kuwa, abincin suke shirin ci shi da Abun Ahmad, ama sai suka dakata sakamakon miyar da Mama ta mayar wuta tana fadan ya yi yaji shi kuma ba cin yaji yake yi ba ko kadan , hakan na iya hanna shi cin abincin , dan haka sai suka shiga hira a tsakaninsu kadan kadan
Abu Ahmad, baban abinda ya saka shi amsa gayatar Mamah cewar ya zo ya karya mana wata rana iyalinsa basa nan ama shi ba zai zo ya ringa cin abinci ba?

Shine yana so ya sake gannin yarinyar nan koda yayane, yana tune bai taba ganninta a gidan nan ba, ya rasa a wani bangare take ne, shi gaba daya bakuwar fuska a gidan nan wace zai ce bai sani ba ai kamar Aunty amarya ce, dan kuwa bai santa ba sani na fuskarta, dan ko ranar da ta shigo sunna nan shi da Babangida ko gaisuwar kirki basu yi ba bale a ga fuskarta ta yi saman Mamah, har hankalin Maman ya yi kanta suka tafi suka basu waje..........., Ko dai ita ce Aunty amaryar?, To ama idan itace yaya aka yi ranar da ya fara ganninta bai ji komai ba?

To abinda ya jinma me yake nufi ne?

Na menene?

Yau ya fara gannin farar mace ?

Ba dai wannan ba, ba dai maganar kyau ko fari bane ya saka shi kure yarinya karama da kallo har ta bacewa ganninsa, ko menene ya tabata ba karami bane, ya kuma shafe shi...............

"Yaya kake gani?

Basmati ne ya dace a yi ko kuwa Oriba rice?" MARSHAL ya fada kasa kasa
A hankali ya dawo da hankalinsa kansa yana saike ajiyar zuciya, Allah yana gani da ace zai barshi zuwa dare su yi maganar kampanin nan da ya ji dadi, dan a yanzu da wasu magangannun ba wani fahimtarsu yake yi ba, gashi magana ce mai mahimmanci dan yana son tura kampani biyun dake yin shinkafun nan dan su ga wane zasu bude shigowa da shi kasar nan ya zamto duk rintsi ba zaka neme shinkafar ka rasa ba a nasu shagon da yake son budawa na harkar shinkafar, dama yana yin na makaroni da mai na girki
Zuwan Amir na biyu kennan bayan na farko da ya zo ya nuna masa dukkan tsare tsaren karshen wata da suke yi na gidan ya sake zuwa fa takardar ya zauna ya shiga gabatar masa da komai daki daki sannan ya fan saurara a nutse ya ce" Yaya, da na so a dan rage harkar ACN gidan nan, ka ga irin kudin da ake kawowa karshen wata na wutar da muke sha, Aban Abah ka dan saka baki a lamarin nan, ka ga ya'yan nan ya zamto wasa suke yi fa da wuta, sai a fita a bar AC na ci tun safe sai an dawo a shige a jone da shi haka, ai ana duba yannayin rayuwa wani abin ba sai an fada maka ba ko dan ba kai kake biya ba ka san nema akoy wahala, da na so na tara su na masu maganar sai kuma nace sai na sanar maka dan kar aje na yi kaina tsaye"
Aban Ahmad ya dauki maganar yana fadin" Gaskiya wannan abu ya dace ne tunda farkoma a saurari maganar Docter, ni din nan da nake zuwa na wuce na san yana magana a kan barnar ya'yan nan, shi barna bashi da wani anfani idan kuma kana yin abu da ciki biyu ne dan ka lalata na wani kai bama zaka malaki nakan ba bale har a lalata maka, hakan kuwa ai bashi da wani anfani, gaskiya a yi kokari a kwatanta masu, idanma da hali kawai a dora masu dokar hakan , AC in aka saka a dakunnan iyayensu da kuma baban falo ai ya wadatar, na dakunnan kowa din nan ya dace ka duba Babangida, dan dawainiyar ba ta wutar kadai bace ai, cikuluftun gidan da yawa Masha Allah"
A hankali ya gyada kansa yana sauraronsu, sannan yana tunanin me ya dace a yi ta yadda ba zasu ga da wuri har za'a fara yi masu wasu abubuwa ba
A nutse ya ce" Abah ya jima yana fadan hakan, bale da ya soke min kudin wuta da ruwan gidan nan a gaskiya nima sai nake gannin kamar abin ya masa yawa ama firr ya ki sai shine ke biya, shi yasa a lokacin ban ce komai ba dan shine da ikon hakan, ama yanzu ina gannin ya dace din a dan daidaita wasu abubuwan ko dan su din kansu su gane menene rayuwar bcs ba kowa zai samu damar hakan ba"
Da murmushi Amir ya ce" Hakane yaya, ina gannin kawai a cire Acn dakunnan kowa a bar na falo din da na dakunnan su Mamah ya wadatar, idan sanyin kake so la je falo ka huta"
Shi dai dan shiru ya yi, dan har ga Allah a ransa baya so su yi tunanin dan Abah ya kau a doron kasa ne zasu ga haka, duda ya san a yanzu dole ya fuskanci lamari irin na komai suka gani su bashi fasarar dake gyara su, a hankali ya san zasu fahimci me yake nufi, yayan Docter fa basu san babu ba gaskiya, sannan wasunsu akoy almubazaranci na mamaki, Mamah kan cewa wani abun kamar bakin ciki idak suka aikata?

Fitowa Mamah ta yi ta ajiye kwanon tana cire safar girkin dake hannunta ta ce" Yauwa inaga yanzu na rage yajin, Rukaya?

Rukaya?
Chapter 53 · 0% Book details