Sashe 67
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Motocin na tsayawa da gudu Sergent ya bude masa bangaren da yake zaune
Fitowa ya yi da dan sauri ya nufi wajen masu aikin, hakan ya sa Hasan dakatawa dan ya nufo da nufin zuwa ya gaishe shi, domin tunda motocinsa suka shigo suka mike daga shi har ZAHRAN sunna kallo har suka tsaya , sunna tsayawa ya cewa ZAHRA bara ya gaishe da baban yaya, ita kuma ta yi wani tsuru tsuru ta gaza cewa komai har ya dawo yana fadin" Inaga yaya sauri yake yi, koda yake yau kin ga kayan aiki ne a jikinsa ta yiwu yana kan aiki ya dakatar dan wani abin"
ZAHRA kam du hankalinta kuma ya yi ciki, dan haka ta yi dan murmushi tana fadin" Zan koma ciki kar a ga na jima"
Murmushi ya yi yana fadin" Toh shikenan nima bara na tsaya ya fito na gaishe shi sai na wuce, sai mun yi waya love"
Murmushi ta yi ta yi gaba tana dan saurin ta shige bangarensu ha ta iso wajen sojawan dake msaa rakiya ta dan risina ta gaishe su
Basu amsa gaisuwar ba sai Sergent da ya ce" Sir yace ki je bangarensa "
Wani irin turus ta yi ta juyo tana kallon Sergent, ta ga hankalinsa bama a kanta ba su duka hudun dake nan kowa aikinsa yake yi,
Ido ta kikifta tana tunanin ita kuma?, Sai kuma ta juya ta kalli hanyar da ya nufa, sannan ta juya ta nufi bangaren nasa tana ta addu'ar Allah ya sa ba wani abu ta yi ba
Bangaren Mamah na da, shine yake zaune yanzu kafin ya gama gyaran bangarensa, jiki ba karfi ta bude ta shiga da salama sannan ta samu waje saman kujera ta zauna ta sada kanta tana ta fatan Allah ya rabata da shi lafiya
Ta dan dauki lokaci a zaunen dan a kadan ta dauki minti ashirin ta ji an bude kofar an shigo
Da sauri ta mike tsaye tana kallon fuskarsa, lokacin da ya juyo da dubansa kuma sai ta sada kan nata kasa tana ta faman murzar hannayenta tana Adu'ar Allah ya kubutar da ita lafiya, dan ba zata manta shakoya da ya yi ya cirata daga kujera a mota ba
Kare mata kallo yake yi har ya karaso falon tun daga kanta har kafarta da ta dan leko daga kasan doguwar rigarta mai igiya
Zama ya yi a saman kujera , irin zaman nan na dan baki baki sannan ya hade hannayensa yana sake kallonta da jiran gannin ta motsa
Jin shiru ya sakata dan dagowa, sunna sake yin ido hudu da sauri ta duka kasa tana gaishe shi da muryarta dake rarabuwa tana hahardewa
Shi dai bai amsa ba har sai da ta sake dagowa da hannunsa ya nuna mata wajen zama yana dan hanna girarsa hadewa dan ya kula kamar tana da saurin rikicewa
A hankali ta dubi bayanta inda yake nunawa, kujerar dake bayanta ce, a sanyaye ta sake nunawa ta ce" Na zauna?"
Idannuwansa yaa lumshe yana mata alamun Eh, dan haka ta dan mike a darare ta zauna din ama wani irin zam na alamun a tsorace take ko memenema dai gatanan dai
A hankali ya dan bude bakinsa , kasa kasan da bai san ko na menene ba ya ce" Shi, bashi da lokacin zuwa zance ne FATIMA?"
A hankali ta dago idannuwanta, da suke ta cika da kwala tana shanyewa, haka kawai kwarjininsa ko gaisheshi zata yi yake hadasa mata kwallah da hawaye
A sanyaye ta sake sada kan nata ta ce" Yayanmu, ban san zai zo ba, yace daga asibiti yake ne ya biyo mu gaisa, sai Aunty tace na je mu gaisa"
Shiru ne ya dan biyo baya, yana gannin lokacin da ruwa ruwa ya daso daga cikin idannuwanta, a hankali sake budar bakinsa ya ce" dama kulunma toh a shirye kike ne?
Na ga fa kin shirya ne?"
Yanzu kam maganar ta so ta bata mamaki, dan har ga Allah a sanyaye ya yi mata tambayar kuma kallonta yake yana jiran amsar hakan, hakan sai ya zame mata wani iri, tana iya cewama banbarakwai namiji da sunna Hajara, sanyin ne ya yi yawa, yadda ya yi tambayar ne kuma ya yi sanyi da yawa
A hankali ta hadiye dan yawun bakinta ta sake dagowa tare da sakin hawayen cikin idannuwanta suka biyo saman kumatunta, a hankali ta dan girgiza kai ta ce" Sai da ya zo ne, Auta ta dauko min na cenza"
Sai ya ringa neman gane waye baya ji a cikin kannen nasa ne?, Daga Auta har RUKAYA, sai ya ringa tunanin ita din wannan ai bata da wani laifi, tunda ai ta fi su yarinta, kawai sai a yi bako rana tsaka su wani shirya su zo ganninsa?
Baya tunanin in zai iya lamunce masu haka baki dayansu, ya dace ace akoy wani matakin bi kafin a ringa ganninsu ba kai sake ba
A tausashe ya ce " Kina ji?, Idan ya kuma biyowa daga gari, ku gaisa ta waya, karshen weekend kawai yake da damar zuwa da yama ku gaisa ya tafi, kin ji?"
Da sauri ta gyada kanta tana sauke ajiyar zuciya
"Tashi ki tafi" ya fada yana sake binta fa kallo
A hankali ta mike bayan ta yi godiyar tata da ta saba sannan ta nufi hanyar fita
Har sai da ta kusa fita sannan ya iya juyowa ya zuba mata ido har ta fice a falon gaba daya
Kansa ya dawo da dubansa gabansa a hankali yana lumshe idannuwansa ya jinginar da kan nasa da jikin kujerar falon
Girarsa ya dan murza a hankali sai kuma ya mike yana kawar da wannan magana da suka yi a tunaninsa, duda abin yana neman bashi matsanancin mamaki, shi da ya nufo falon da niyyar yana zuwa ya balbaleya da fada?
Sai gashi yama kasa tuna irin harshen da ya mata magana da shi gaba daya
__________________________________
Allah bays yankawa bawa kazar wahala yace ba zai fige ba, kofa yake akace sa kai ya fi komai a duniya, babu kuma mai juriya irin mai mugun nufi, dan kuwa sai ya kai ga ci yake iya samun sasauci
Daga gida dan acaba ne ya warceta suka ringa bin bayan HASSAN ta sheda masa du tsiya kar ya bari motar ta bace masa, ta yi dace da gagarare a babur gata gagarariya sai kawai ta gyara zama ta rike babur suka fantama
Tafia ce mai nisan gaske dan a kadan sun dauki minti arba'in dan sun tsaya go slow da danjijin hanya kafin su dauki wata doguwar hanya su hange shi ya tsaya a kofar wani mamakeken gida mai kyan fasali
A nan ta sauka, yan kudaden da ta warta a hannun Sahabi da su ta samu ta biya dan acaban nan sannan ta karasa wajen get din da aka bude masa ya shigar da motarsa
Da gudu ta shige mai gadi na tura get, hakan ya sa da sauri ya ringa fadin "ke wacece ke?
Ina zaki je?
Ke malama ana magana dakata daga nan, dakata kar ki shiga ciki!"
Sai dai ina ita bata wani tsaya ta kula shi ba, dan ta san lokacinta zai bata mata ta hanyar hannata shiga a banza a wofi
Turus su Hajia baba suka yi, da mahaifiyar Hasan, haka shima da sauri ya fito a motar yana dan ja baya gannin har kamar zata fado masa dan masifa tana dakatar da mai gadin nan ta ce" Malan kar ka taba ni mana, ka bari na sanar masa abinda ya kawo ni na yi tafiyata dan ba neman arziki ko maula ta kawoni ba!"
Da sauri, da zafin rai Hajia Baba ta nufo wajen tana fadin " Meye wannan shashancin, ke wacece ke?
Me kike nema a nan?"
Da ido LARABA ta bita, sannan ta kalle sho, kwarai akoy jinni mai karfi dake fuzga dan Hasan kama da mahaifinsa ya yi sak shi kuwa mahaifinsa kamarsu daya da yan uwansa hudu
A dan kidime ya dubi hajia ya ce" Hajia, ban santa ba walahi, ke wa kike nema?"
LARABA ta tabe baki ta ce" Da wahala ka sanni, ama ni na sanka, ni y'ar gidan su FATIMA ce, wace kake neman aure"
Da mamaki, da rashin gastawa yake kallonta, Hajia baba kuwa ta kure shi da kallon tuhuma, dama yarinyar da ake maganarta yanzu haka yan gidansu suke da rashin kamun kai ko menene?,
LARABA ta dora da fadin" Tunda ka fito daga gidan nake biye da kai dan ina son yin magana da kai, Bawan Allah shin ka san Zahra shegiya ce bata da uba kuwa?"
Wani irin kauuu da ya ji a zuciyarsa tamkar an soka masa mashi ya saka shi a rikice ya ce" Ke, baiwar Allah ke kuwa me yayi zafi haka?, Me kike nema da duniya da zaki ringa yiwa mutun shari?
In kin ce shegiya ce sai me?
Bayan wannan y'ar uwar taki kike tonawa asiri me ta maki da zafi haka?"
"Ni babu abinda ta yi min, na ga ne ana neman maka rufa rufa nace zan zo na taimakeka, bayanshi ba wani abin, Allah na tuba mema zai hadani da ita?