Sashe 2
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saukarsa kawai suka gani a gabansu, hakan ya sa Yusuf mik'ewa tsaye a ba zata yana kallonsa, sai kuma ya koma da sauri da idanuwansa yana yiwa Bashir ido kan maganar da suke yi, lokaci d'aya kuma suka ringa yi masa sannu da zuwa kusan du aka nemi tashi a bashi abin zama.
Murmushi ya yi ya zauna saman kujera yana gyara zamansa da kyau ya kalli Yusuf, wanda shine uban dabar ya ce" Baba zan samu shayin kuwa?"
Yusuf ya wani dan duk'ar da kai ya ce" Sai oga, shayi kai akoyshi oga, bari na ziga maka shi."
Daga haka ya yi shiru, haka wajenma gaba daya tarin samarin ya d'auki shiru kamar ba kowa, har sai da aka zuba masa shayin nan ya amsa ya sha sannan ya mik'e yana murmushi ya d'aga masu hannu ya masu salama ya k'arasa cen wajen motarsa ya bud'e ya shige ya tafi.
Wata wawuyar ajiyar zuciya Abbas ya sauke yana d'aga yar yatsarsa da ya murje sigarin da yake busawa da ita ya talabe hab'arsa da hannayensa bibbiyu ya ce" Baba dama oga na kawo ziyara nan har na zo da wannan askin na kuma kunna sigari?"
Yusuf ya saki daria yana kallonsa ya ce" Kai baba yanzu fa ka gama cewa kai shege ne, ina cewa yanzu ka gama d'udd'urawa masu kaki ashariya kace kai ba dai mutun ba sai dai Allah?"
Abbas ya yi dariar shima yana mayar da kwalin sigarinsa cikin aljihun wandonsa ya mike yana gyara takalminsa k'ato mai nauyi ya ce" To kun ji, ni kam na k'ara gaba, kai in ba wulak'anci ba Baba ta yaya zaka had'a karnukan sojoji da ubansu?
Mutumen nan fa baya duka kwata kwata, ni da idona na ga ya mari kannin matarsa ya summa, uban wa ya aikeni wasa da numfashi?
Ce maka na yi ina fafatawa da k'annanun karnukan ba wai SULAIMANA ba , na fasa kawai sai kum faso."
Kusan d'aid'aikun yan jagaliyar watsewa suka yi, dan sun gani sarai ciki ya shige, yana anguwar , ba zasu d'auki kasadar d'ora daba a wajen ba yau, dan komai na iya faruwa ciki harda ya tub'eka ya zaneka tasss yace baya son rashin kunya kuma babu abinda ubanka ko babarka zasu yi, hasalima ce masa suke Yah SAYYADI.
A nutse yake tafia cikin babban filin gidansu, jifa jifan yakan had'u da samarin gidan, su gaishe shi da girmamawa sannan su wuce bayan ya amsa masu ta hanyar basu hannu, sannan ya d'an ja ya tsaya yana k'are maka kallo, hakan ke saka su saurin sadda kai su ringa kame kame kamar sun aikata laifi, bayan shi ba Dukansu yake yi ba, babu wanda zai ce ga ranar da ya saka hannu ya dake shi a gidan nan, ama sun fi jin tsoronsa tamkar ransu fiye da wanda yake da masifar maganar da dukansu kamar zai kashe su da zarar sun yi laifi.
A kofar falon mahaifinsa ya ja ya tsaya yana dan sake gyara shigarsa, ya sani ne koda ABAH bai ce komai ba sai ya bishi da kallon an yi girman wofi saboda shigarsa
Da wannan ya yi dan murmushi ya kama abin bud'ewar ya shige yar k'ofar farko sannan ya dannan abin budewa ya ja ya tsaya, ya san za'a haska fuskarsa ta camera kafin ya samu shiga
Minti biyu tsakani jar wutar ta bada blue, hakan ya saka shi murdawa ya shiga , a nutse ya cire takalman kafafuwansa yana dan satar kallon Mahaifinsa dake zaune saman kujera zaman mutun biyu yana murmushi yana fad'in" Marhababika Abahna."
Dan murmushi ya yi yana tsayen nan har amaryar Docter Ahmad SULAIMANE ta shinfid'a sabuwar darduma a saman lalausan cafet din dake malale mai kyan gaske da tsafta tana murmushi da zumbulelen hijabinta tana nuna masa tare da fadin" Babangida barka da zuwa, Bismillah Abah."
Murmushi ya sake yi ya k'arasa a nutse ya hau saman dardumar dake daf da kaffafuwan mahaifinsa, ya sada kansa sosai a tausashe ya mika hannayensa biyu dan amsar na mahaifinsa dake miko masa ya ce" Barka da hutawa ABAH, yaya ibada?"
Musabaha suka yi mahaifinsa na kallon agogon hannunsa har suka gama ya zauna a nan kusa da kaffafuwan nasa ya dauki kaffafuwan ya dora saman wandonsa a hankali yana dan murzawa yana jin muryar mahaifinsa a tausashe ya ce" Yaya iyali?, Yaya fama da jama'a?"
Murmushi ya yi kasa kasa ya ce" Alhamdulilah..."
Sai kuma ya dago yana kallon fuskar mahaifinsa mai dauke da furfura fara kal a gemunsa baki daya, sai tsili tsilin bakin gashi ya ce " Yaushe rabon Docter da zuwa gidan nan?"
Kin bashi amsa Docter Ahmad ya yi ta hanyar kamo wata maganar ya ce" Abahna, na tambayeka iyali baka ce komai ba?"
Aunty amarya ce ta yi murmushi bayan ta zuba masa ruwa a kofi mai kyau da tsafta ta ajiye ta ce" Babangida, ai ba zai baka amsa ba , Docter baya son ganin likita, sau biyu yana zuwa yana kin bashi dama, dama so nake ka zo na sanar maka."
Baki Docter Ahmad ya kama yana kallonta, sai kuma ya yi murmushi ya ce" Gaba kad'an zan ringa lab'ewa ne tunda an fara saka min ido a gidan nan, in ba abin Umman *FATIMA ZAHRA* ba me ya yi saura da ya wuce shiga kabari?
Wai ku Docter zai cewa na daina cin nama, sai dai Allah ya bashi hakuri domin babu abinda zan daina d'and'annawa a cikin launin dandanon dake dadad'a min zuciya dan gudun abinda yake rubutace ba kuma zai kauce ba."
A hankali *SULAIMANE AHMAD SULAIMANE* ya d'an zubawa fuskar Aunty amarya ido dan gannin reaction d'inta, sanadiyar sunnan da ABAH ya ambata , sai ya ga kanta a kasa na yan dak'ik'u sannan ta mike ta nufi Kicin ba tare da ta kuma furta koda A ba.
Kansa ya maido wajen ABAH , a lokacin da ya girgiza kai bayan ta bar wajen ya ce"...
*Alhamdulillah.*
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_2_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
Kansa ya maido wajen ABAH, a lokacin da ya girgiza kai bayan ta bar wajen ya ce" Ban san ranar da zata fuskanci rayuwa a kan y'ar da ta haifa da cikinta ba, Allah shi kyauta."
Bai ce komai ba, sai ci gaba da ya yi da dan mamatsa
afafuwan Aban nasa, a haka Aban ke ta yi masa bayani a kan abubuwan da suke da buk'ata, ba wai kayan abinci, sutura ko harkar wutar lantarki ba, a'a, abubuwa na rayuwa dake iya b'illowa yau ko gobe, wasu taimako ne da sauransu, sannan ya kawo masa karar kanninsu mai sunna JAMILU cewar an kawo karar baya karatu a makaranta, ya yi abokan banza yana yawace yawace a makarantar, har ya yi sa'in'sa da malaminsu, a nan nema ya dan yi dan tsam ya ce" Shi JAMEEL din?"
Aba ya sheda masa kwarai kuwa,
Bai ce komai ba ya ci gaba da sauraron Aban har ya dawo kan maganar yan mata biyu da za'a aurar da kuma k'anninsa AMIR Ahmad SULAIMANE, shi ake jira ya saka rana da dai sauransu, watau bayanin kud'ad'en gadajensu da dukkan abinda ake yi.
Murmushi ya yi ya sake d'agowa ya dubi mahaifinsa ya ce" In sha Allah, za'a yi komai, Abah, sai kana hutawa fa, ka ringa rage magana sosai da yaren nan, idan sun yi ba daidai ba ka saka a kawo su cen in sha Allah zamu zauna mu tattauna."
Baki da Hanci ABAH ya bud'e yana kallonsa, sai kuma ya yi daria ya ce" Kai Babangida, kai Babangida, so kake ka yiwa Y'a'yana mugunta ko?
Gaka nan fuska fara, hannaye farare ama ban san me kake yi masu a cikin duhu ba da suke jin tsoronka, shikenan dan sun min laifi sai na tura maka su cen inda bana nan ba zan tare masu ba?
Aa gwara ka daka a gabana ta yadda idan zaka karya zan tare.
"
Shima murmushi ya yi yana sake sada kansa tamkar wani wanda ke gaban sirikansa , yanzun ma bai ce komai ba.
Sosai ABAH ke hirantarsa, shima yana bashi amsa a matsayinsa na wanda ya fi sakewa a gabansa fiye da kowa, sai da ya d'auki lokaci a gabansa sannan ya mik'e yana yi masa sallama da niyyar bi d'aki d'aki ya gaisar da iyayensa har zuwa na mahaifiyarsa sannan ya wuce gida.
A hankali Abah dake kallonsa ya ce" Nace ba, wannan agogo kuwa tai min kyau, nawa ka siyeta ne?"
Ja ya yi ya tsaya, ya juyo yana kallon Mahaifinsa, dama tunda ya ga yana bin agogon nan da kallo ya san da wata a k'asa, watan kuwa ba komai bace face son sanin kud'inta, dan ya tabbata so yake yi ya san shin ya sayeta da mak'uddan kud'i ko da sauk'i?
In da mugun tsada ne yanzu a bud'e babin wa'azi kala kala harda su maganar zakka, bayan Alhamdulilah yana kamanta abinda adini ya zo da shi.