← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 110

Sashe 13

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A wannan rana ta ga rayuwa, har sai ta tuna lokacin baya kafin ta je bara wajen DOCTER AHMAD SULAIMANE, a lokacin da take wuni a boye da yinwa
Sosai abin ya so rikitata har ta manta cewa a dakunnansu babu wanda zai rasa dan abin tabawa kama daga madara da biscuit da ake ajiye masu bayan na kicin, dan dukkan kokarin iyayensu dan su ji dadin zama a gefensu sunna yi, har sai da dare ya raba tsaka , shiru ya wanzu a kowani lungu da sako sannan ta tino, a galabaice ta karasa wajen ta wawuro ta nufi bayi ta cika kofi da ruwa ta kada ta kafa kai sai da ta yi nak ta ajiye ta dawo gefen gadonta ta zauna tana ambaton Allah da zikiri har barci ya yi awon gaba da ita cikin salamar zuciya, dan kuwa babu damuwa ko tashin hankalin da zai ziyarci bawa ya kasa samun sauki idan ya sanarwa ubangijinsa
Washe gari, har kusan karfe goma, yan gaisuwa na ta shigowa, yayan gidan du sun zo sun gaishe da masu zaman makoki , harda mahaifiyarta dake nan da yayarta, da yan uwanta du sunna nan, ana ta shige da fice ana ta sadaka da karatu ba ji ba gani gata irin na malamai tana samu ta ko'ina hankula du sun karkata a nan, har sai da sha biyu ta yi sannan Mamah ta kula cewar rabonta da Fatima tun jiya, yau yayan gidan sun yi ta sunturi bara ganta ba, nan hankalinta ya dan so tashi ta yi kiran auta ta aikata dubo mata ita
Kwonkwasawa Ummi ta yi, sannan ta yi salama ta dakata tana jira
Jim kadan ta ji karar bude dakin da ky, dan haka ta tura ta shiga da salama a bakinta tana sauke dubanta a kan FATIMA
Tsaye take da doguwar riga mai siriri
n hannu, kanta sanye da hula irin ta kulun zare kore mai haske ya rufe gashin kanta ruf, dogon karan hancinta ya yi zuwat da shi sai kyali yake yi, fuskarta sai fitar da annuri take yi duda kumburinta da kuma kumburin wajen idannuwanta ama annurin bai bace ba, ta kalli litafin dake hannunta litafin hadisi ne mai larabci ziryan sannan ta idasa shiga dakin tana jin kanshin da yake fitarwa da kuma sanyin da yake dauke da shi
"Ummi lafiya?" Fatimah ta tambaya da muryarta fake kurya, hakan ya sa Ummi sake juyowa tana kallonta, a hankali ta ce" Lafiya kalau, dama Mamah ce tace bata ganki ba tun jiya na nemo mata ke ko lafiya?"
Idannuwanta ta lumshe, tana karyata zuciyarta dake ce mata koda zata shekare a dakin babu mai nemanta , da ace itace ta rasu babu mai yi mata addu'a har ta samu wani sansanyan murmushi ya subuce mata a hankali ta ce" Aya, ki ce ina daki ina so na yi sauka ne kafin sati, ga kuma karatun harda da zamu bada ta bagara a makaranta".........

Ummi ta kureta da ido, haka kawai sai ta ji ta kasa yarda da maganar,
Ita dai ba wata yarinya karama bace gaskiya dan yanzu haka shekarunta goma sha biyar......., Takan gane wani abun da aka so bata shi a baibai , bale lamarin FATIMAH zata ce ta fi sauran fahimtar wacece ita
Wajen gadonta ta duba, ta hangi dan kayan kwalam da makulashe da masara da kofi.......

Ta san mahaifiyarta na wajen nan kwonciya kawai ke mayar da ita bangarenta, itace a tsaye a kan komai, sauran matan na Aba kowace a nade take tana mus mus da baki sai utace ke kai kawo da bada umarni a dukkan abinda ya dace, ta kuma san babu halitar da take tsoro irinta, itama babu halitar da ta ki jinnin waigowaa ta gani irinta, ita da kanta ta sha sheda marin da ta dauka na mahaifiyarta dan kawai ta gaisheta, har sai da ta daina gaishetan idan ta ganta har sai ta bar waje take dago kai, ta tabata da wani abin, hakan ya sa ta ce" Aya Allah ya taimaka Aunty, ama ki ringa leka Mamah kin san fa ba zata karbi uzurinki ba, bata son irin hakan, ko ba wannan bama kema ai bai dace ki shige ciki ki labe ba bayan rasuwar matar Baban gida ne, ya dace ace kina cikinmu ana sauka ko?"
Tsareta kawai Fatima ta yi da ido tana sauraronta da mamakin furucinta, uhum ita?

Idan ta je ai zata tsinci rashin hankalinta a hannunta dan ta tabata sai sun gwada mata bata da wayo walahi, wannan lamarinma gata ne tana gannin akai mata gwara ta zauna inda Allah ya ajiyeta
Haka fai Auta ta gama ta fice ita kuma ta rufe dakinta ta koma bakin abinda take yi, jiya zuwa yau ta yi kuka ya fi a irga, idan ta yi kuka sai ta yi karatu, in ta gaji sai ta yi ta rawatawa a cikin dakin tana ciro kayanta ninkaku tana sake ninkewa dan dai kar zaman ya zame mata damuwa ne
Ci gaba ta yi da karatunta har rana ta yi
Tana kallon madarar nan tana jin ta gundureta , ta shiga tunanin me zata ci?

Yaya zata yi ta samu?

Aka buga mata kofa a karro na biyu da salamr muryar Ummi
A gajiye ta mike ta karasa ta bude kofar ta dan ja baya tana kallon Ummin da ta shigi da plate mai dan girma dauke da flask na abinci da kuma wani dauke da miya, sai cokali da goran ruwa manya biyu ta kai t ajiye mata nan kusan kwalin madarar bata ce nata komai ba ta dawo zata fita, a nan ne ta iya budar baki muryarta na rawa a hankali ta ce" Ummi, na gode, Allah ya saka da alkhairi"
Ja Ummi ta yi tana jin zuciyarta na neman karyewa, ai kuwa ga tabacin abinda take tunanin, ta yiwu mahaifiyarta ce ta hannata fitowa
Subahanalah, shi yasa take gannin beken da yawan mutanen gidan nan da suka tsangwameta, da ace zasu fuskanceta su barta da zafi mai zafin gaske tsana irin ta uwama da sun tausaya mata sun taya ta da addu'ar samun sauki, ama du sun saka mata ido ba tare da ta yi masu komai ba, bata zaune a kansu, bata tsare samunsu ko lafiyarsu ba, sunna manta kadara idan har abinda ya kawota duniya ya same su yaya zasu yi?

Ita bama ita ta aikata ba ama tana kwasar tashin hankalin duniya da mutanen cikinta, to da itane ta aikatan yaya kennan?

An fi tsangwamarta fiye da mahaifiyarta ko dan mahaifiyar tata bama zaka ganta ba sai in ta kama ne ita kuma dole zata fito ta cudu da kowa ko dan zuwa makaranta?, Tana matukar tausayawa wannan baiwar Allahn, gaba daya rayuwarta abin tausayi ce, gata da wuyar sabo da wuyar sakin jiki, kusan tsoron kowa take ji a gidan dan an tsangwameta
Dubanta take yi har dai ta dan yi alamar zata rufe sannan ta sauke ajiyar zuciya a nutse ta ce" Mamanki ne tace a kawo maki, kuma tace saura ki rike byro har ciwon kanki ya tashi ta gamu da ke...." Ta karashe tana dan sakar mata murmushi, ta kirayi Mamah da mamanta dan ta ga r
action dinta, so take ta taimaka mata ko yayane
Ai kam ta ga ta saki dan murmushi tana sada kanta, a hankali ta ce" In sha Allah Ummi, na gode"
Itama murmushin ta sake yi ta juya ta tafi da katon hijabinta kamar zai taketa ta fadi
Har sauri take yi wajen bude abincin
Da dan sauri ta zuba ta tankwashw kaffafuwanta ta yi Bismillah ta ringa ci tana sauke ajiyar zuciya har sai da ta ji cikinta ya cika daidia misali sannan ta kwashe ta kilace sauran da niyar shi zata loda da dare domin girkin tai mata dadi a bakinta ko dan tana jin yinwa ne?
Chapter 13 · 0% Book details