← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 110

Sashe 8

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban goshinsa ya dafe, a hankali ya mike daga zaunen da yake ya dubi docter ya ce" Man, yaya jikin nata ne ?

A magangannunka ban ji ka sanar min da sauki ba,"
Docter ya ce" Alhamdulilah, in sha Allah komai zai daidaita, da sauki tunda an ga menene matsalar, ana kan shawota ne, an yi mai wuyar tunda an saka abin a kan hanya"
Gwauron ajiyar zuciya ya sauke ya sake zama yana jan carbin nan
A hankali Docter ya ce" Man kana iya tafia gida ka huta fa, ka san munada masu jinya yanzu haka mutun biyu na bar mata a dakin jinyarta, ana ganninka an san ka gaji....."
Dan murmushi ya yi yana tuna gaskiya yau ya gaji, tunda ya fita bai zauna ba, fitar karfe shida na asuba, ya zo zai kwonta din ne jikinta ya kiya
Mikewa ya yi ya mika masa hannu suka yi musabaha, sannan ya juya da carbin yana fadin" Zan shigo da safe in sha Allah, kafin nan ina fata zan ringa samunka phone....... thank you man"
Daga haka ya fice a office din, ya zagaya ya fice kwata kwata a asibitin ba tare da ya koma dakin da aka ce auntynta ta zauna ba
A hankali yake tafe yana duban gari har ya dakatar da wani dan acaba ya haye ya sanar masa anguwar da yake so ya kaishi
Shigar dare ya yiwa gidansu, hakan ya saka shi shigewa bangaren mazan gidan ya yi kwonciyarsa saman doguwar kujera yana ci gaba da jan carbinsa har barci barawo ya yi awon gaba da shi bayan ya gama tunanin ko me Amir ke yi yana kai kawo a bangaren cen?

Da asuba bayan sun fito daga sallar asubahi shi da ABAH da yan uwansa sunna tafe a tsanake ABAH na fadin" Subahanalah, baban gida bara mu karasa maza a shirya a je asibitin, Allah ya sawaka, ai da ka sanar min tun jiyanma Baban gida sai kawai ka yi shiru abinka sai yanzu?"
Dan duban wajen da kanninsa watau G
ral AMIR ke fige wata zabgegiyar bulala ta dalbejiya da ya karyo ya yi sannan ya amshi hannayen kannensa dake dukawa har kasa sunna gaishe shi da Abansu, zakakun samarin gidansu yan makaranta da zarar sun gaishe su sai bi bayan su, shi da Abansu dake tafe
A hankali Docter Ahmad SULAIMANE kasa kasa ya ce" Abahna, ka ga cen dan uwanka ya yi bangaren hajia, Allah ya sa ba cin zalin Y'ayana zai je ya yi ba"
Idriss ya yi dariya kasa kasa, dan shi ya san kwanan zancen, shi kuma Mar
chal bai bi ta kan wannan maganar ba, so yake yi ya raka mahaifinsu ciki ya dawo ya gaisar da Hajia ya wuce asibitin dan gannin yaya Manal ta tashi
Da dan sauri yake nufar bangaren Hajiar, har yanzu kayan barcin ne a jikinsa masu ruwan madara, sannan har yanzu kanshin turarensa na jiya bai bar jikinsa ba,
Yana tafe yana amsa gaisuwar ma'aikatan gidan da yan uwansa da yan amsar karatun safe har ya isa ya kama kofar dakin ya bude
Saka kafarsa ta dama ya yi daidai da saukar karar marin da Amir ya wanka mata da karfin balaki ya rintse idannuwansa, lokacu daya kuma ya bude ya sake dorawa a kanta yana kallon yadda marin ya ratsata har ya sakata kifawa daga tsugunnin rakumin da ta yi tana firi firi da idannuwanta
Gabansa ne ya kwonci kwonci ya fadi, a hankali ya bita da ido a lokacin da ta kifa din sannan ta saki wani irin sansanyan Kuka mai ratsa zuciyar koda makiyinta ne bale masoyinta, uwa ko uba, yaya ko kani...........

"Au, ni zaki yiwa tsayaya ko?, Bari ki gani! , Ba zaki sanar min uban waye shi ya fitar da ke tsakiyar dare ba?

Ki yi magana dan walahi in baki yi bayani ba sai na kakaryaki yau a gidan nan!" Amir ya fada da karfi har yana mikewa ransa na sake dugunzuma
A hankali ya dauke kansa, ya kuma dauke idannuwansa, ya cire kansa kwata kwata daga wajen ya idasa shigowa a nutse yana dan dakatawa dan jin gaba daya sun kwashi miko masa gaisuwa harda Amir din dake zane su ya sake sara masa yana furta" Morning sir" dan gaba daya yanzu Amir ya daina yi masa gaisuwa irin ta cikin gida, a ko'ina ya riga ya bi jinnin jikinsa gaisuwar nan itace yake yi masa dan girmansa karra hauhawa yake a idannuwansa
Bai iya amsawa kowa ba, sakamakon abinda ya dane masa harshe
A hankali ya furta" Hajia fa?"
Amir ya sake matsowa yanna fadin" Na'am Abah?"
SULAIMANE ya dan kalle shi gannin bai ji ba hala?

Sai kuma ya juya wajen mai bodar ihun kukan nan tamkar wata tinkiya tana ihun ta shiga uku wayo Allah ta shiga uku, ya sake juyowa inda Amir yake a hankali ya ce" Ka hannasu kuka da ihu mana, hakan na saka ciwon kai, su yi a hankali......ko ba komai ai mata ne............."
Da sauri ya juya ya ce" Ke yi a hankali mana ko meye wannan shirmen kamar na kashe ki?"
"Ka ji tsoron Allah Amir, ka ji tsoron Allah, haba dan Allah dan kawai nace ka masu abinda ka ga dama kuma kukanma hannasu zaka yi baki bude?

Zahra ba zaki fadi amsar da ake tambayarki ba ko?, Shikenan ki yi , ki ci gaba da yi Zahrah na gode.......!" Mamah ta fada muryarta na neman nuna rauninta a kan yarinyar
Hankalin FATIMA ne ya sake tashi, hankalinta tashe take girgiza kanta a rikice ta ce" Mamah, dan Allah kar ki koreni mamah, dan Allah mamah kar ki koreni, saurayina ne shine yace na zo zai ganni shi yasa na je"
Ido suka zarro gaba dayansu banda SULAIMANE dake tsaye kikam yana kallon ikon Allah
"Ji sakarci, saurayinki kike fada mana a nan?" Amir ya fada yana katseta da muguwar tsawar da ta sakata hade kanta da gwuiwa tana sake fashewa da kuka
A sanyaye Hajia ta ce" kora kuma na koreki gidan uban wa wai??

Saurayi kuma Zahrah, saurayi gareki har ya isa da ke ban sani ba?

"
Da bacin rai Amir ya ce" Da an fara yi mata fada ko duka sai tana wani abu tamkar mahaukaciya, bari ki ji Zahrah babu wanda zai kore ki a gidan nan dan gidanku ne, duka ne zaki ci tamkar jaki idan bakya jin magana babu abinda za'a yi dan haihuwarki aka yi, an isa da ke , saurayi ne ya fitar da ke a irin lokacin nan ko?

Ba ke ba shi daga yau dan ubansa kina da darajarki ba zai wulakanta mana ke ba!"
"Wayo Allahna, innalilahi wa inna ilaihi rajune, yaya dan Allah ka min rai kar ka shiga tsakanina da shi domin ina sonshi tamkar rainah yayana" Fatima ta saki maganar a tsume tana nade kanta dan ta sani ne yanzu zata ainahin daku ba dukkan dazu ba
Da sauri ya sake cira kansa ya sauke mata duba daya tak, sannan ya girgiza kansa ya juya ya karasa inda Hajia ke sallalami tana neman fashewa da kuka,
anta mata sunna tayata harda wace ta silale ta dora hannayenta biyu saman kanta tana fadin" Mun shiga uku, yau ba ke ba muma sai mun sha dukan safe innalilahi haba Zahrah me mukai maki?"
Hannun Hajia ya riko , hakan ya sa ta dube shi tana sauke ajiyar zuciya muryarta a birkice ta ce" Baban gida ka ji wani balakin ko?"
Bakinsa ya dan tabe , bai bata amsar nan ba a hankali ya ce" A asibiti Manal ta k
wana, bata da lafiya ne Hajia "
Hajia ta yi dan tsam, har a ranta ta ji babu dadi, ta kuma tausaya fiye da tunanin bawa, dan kuwa a yadda ba wani zuwa da zowa tsakaninsu da Manal din sai idan wata sabga ta tashi ta yi kokari ainun ta hanyar nuna damuwarta tana fadin" Subahanalah, aya , zazabin nan ne ko?

ALLAH ya sawaka , Baban gida kana jin me y'ar cen tace kuwa?

Ka ji zata tona min asiri ko babah? ya dace ka mara nasiha"
A hankali dan makoloton wuyansa ya yi sama kadan sannan ya yi kasa , ya lumshe idannuwansa sai kuma ya sake rike hannunta a hankali ya ce" Allah ya sanyaya mana Mamah"
Hanci kawai take ja, har ya saki hannunta ya juya bata ankara da mutuwar gwuiwarsa na rashin binsa da bata yi ba, batama lura da yannayin da yake ciki ba sam, hankalinta ya fi karkata wajen da Amir ke neman karya mata ya'ya, domin ba Zahra kadai yake jibga ba harda sauran , yace ne tabas sun san me yake faruwa suka yi shiru, yau ko shi ko su
A lokacin da ya kusan fita gaba daya daga bangaren ne Hajia karama ta karaso, wato Aunty Amarya mahaifiyar FATIMA ZAHRAH
Dan ja ya yi kadan, da girmamawa na matsayinta na matar mahaifinsa ya sake maido mata gaisuwar da take yi masa yana kokarin kore damuwar da ya kunso a ciki
Aunty Amarya da kula ta ce"
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_6_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
Aunty Amarya da kula tana dubansa ta ce" Baba asibitin zaka koma ne?
Chapter 8 · 0% Book details