← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 110

Sashe 68

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Matar Abanmu ta zo da ita, bayan wannan ba jinninmu ba..........................................."
"Kai Mahfuz fitar da yarinyar nan!" Hasan ya katseta rai bace yana nuni da mai gadi ya fitar da ita, ransa har wani tukuki yake yi, hankalinsa a mugun tashe, wannan magana da aka yita a gaban Hajia Baba ji yake yi dama bai nufo gidan a yanzu ba, dan ya san an riga an jika masa aiki sai gyaran Allah
Mai gadi na korarta tamkar wata barauniya tana tirjewa har ya fitar da ita daga gidan ba mutunci ba daraja bata san maganar da ta yi aj saurareta ko ba'a saurareta ba ta ringa tafiya tana dame hijab dinta, dan ta san in ba matayi ta samu ba da wahala ta iya mayar da kanta gida, bata da ko sisi a hannunta, a gidanma kuma bata ajiye ba
Tunda ta fita Hajia Baba ta tsatsare shi da ido tana masa kallon da yake ji tamkar zai fashe da kuka dan rikicewar zuciya
A tausashe, sai
dai kana jin amon muryarta ka san abin ya tabata ta ce" Hasan, dama yarinyar da ka sa muke shige da fice muna shiri muna murna muna jira ace mu zo haka ne bata da tarbiya?"
Har jikinsa rawa yake yi dan rasa madafa, a rikice ya ce" Hajia, dan ta zama marar uba ai ba yana nufin bata da tarbiya ba, Hajia walahi yarinyar nan tana da tarbiya, tunda muke tsayawa bata cikaken minti ashirin da ni take komawa, a gidanmu Mamanta na tsaye a kansu, ko sakon da na kai na wajen Mamah hannasu amsa aka yi, Hajia tana shiga mai kamala, tana da kunya, tana daraja mutane, dan Allah hakan da aka fada ki dauka wani mataki ne na son ruguza farin cikinta, ta yiwu wannan din tana da yar tsama da ita, ama koda haka din ce Hajia ai ba haramun bane ko?

Dan Allah kar haka ya daga maki hankali"
Hajia ta yi murmushin takaici tana girgiza kanta, a nutse ta ce" Wato yaro yaro ne, nawa suke shigar kirkin sunna nuna kunyar da tarbiyar sai an zo lokacin kunya a ji kunya?

Ai mace ta girmi tunaninka Hasan, kuma da kake cewa ba haramun bane eh lalle ba haramun bane, ama ni na yiwa zaman aure fasarar da ya zarce tunaninka, zaman aure aka ce ba rudin soyayar titi ba, soyayar nan ta dan lokaci ce, idan kuka zauna a nan hali zai bilo , yaya kake tunanin tarbiyar yanyanka?, .........an fada maka zaman na dan lokaci ne?"
Hasan ya ringa kallonta ba ko kifta ido
Hajia ta dan matsa ta dan bubuga gefen hannunsa a tausashe ta ce" Mata wata yauma aka haifeta my son, ka sake zurfafa bincike plz"
Daga hala ta yi tafiyarta ko maman tasa bata tsaya sun gama salama ba, dan an kunsa mata kuma ba zata taba dauka ba, lalle zata je da kanta ta bincika a cikin sirri, in dai haka ne ba zai yiwu ba, ita ba tana zagin yaronya bane da haka, aa, tana tsaftace tsatsonta ne da fatan samawa yayanta da yayan yan uwanta mace ta gari, a haka kuwa gaskiya bara ga mace ta gari ba, sai dai a yi hakuri
Hankali tashe ya karasa wajen mahaifiyarsa, kansa har yana sarawa, maganar ZAHRA na safiyar nan da tace tana son masa magana a kan NASABARTA ya ringa dawo masa.... innalilahi wa inna ilaihi raj'une
A raunane ya kalli mahaifiyarsa, hawayen dake cikin idannuwansa sunna neman zubowa ya ce" Mamah, kar ki bari ta rabani da yarinyar nan, dan ina sonta, koda itace ta haihun ina sonta, bale haihuwarta aka yi, menene laifinta?

Hajiama tana da ya'ya mata, ya dace ta ringa sasauta wasu abubuwan, mu zamu zauna da zabinmu, a barmu idanma me zasu mana a barmu da su, ni ba zan taba yarda da zabinta ba, walahi ina iya bara mata garon!"
Hankali tashe mahaifiyarsa ta bishi da kallo bayan ya gama ya shige da mugun sauri yana share hawayensa
Hankali tashe ta juya ta bi hayanshi cikin dakin tana fadin"
Hankali tashe ta juya ta bi bayanshi har cikin dakinsa
Budewa ta yi ta shiga ta same shi zaune ya dafe kansa da hannayensa bibiyu
Karasawa ta yi inda yake zaunen ta zauna dan kujeru biyu ne haka yan madaidaita na zama ta saka hannunta tana janye hannayen nasa , hakan ya sa ya dago ya zubawa fuskarta ido
Murmushi ta yi a sanyaye ta ce" Oh su Hasan dina soyayar ce ta yi karfi haka?

Kuka fa kake yi?"
Idannuwansa ya rintse hawayensa suka yi karfi sosai, ya sani ne ta riga ta faru ta kare, mahaifiyarsa bata da ikon sakawa ko hannawa, ba wai mahaifiyarsa kadai ba, baki daya matan gidan sirikan basu da iko da
ansu, Hajia Baba itace kadai ta isa da
an kowa, sai ta amince da matar da zaka aura sannan mahaifinka ya daura maka, ba ruwanta da koda y'ar uwar mamanka ce in dai ta yi tsantsamin tarbiyarta ko nasabarta tsaf zata kiya kuma a yi mata biyaya, ta kasa gane zamani ya cenza, ta kasa fahimtar wani namijin yama fi sin yarinyar marar jin magana dan ya tsani mace salo salo da ita kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, Hajia ta kasa gane soyayar da take yiwa kallon ta dan lokaci ce eh an san da haka ama dalilin kai ka gani ka zabo abinka ko me yarinyar zata yi maka a zamantakewar zaka jure ka yi zamanka ka daidaita abinka a daki ba kamar irin rayuwar da take fuskanta kulun tana rabiyar fadan ya'yan nata da matayensu ba, dan kuwa ai yawanci ita ta kananage ta zaba sai ta gyara zaman ko?

Ya sani ne mahaifiyarsa ta fi kowa jin ciwonsa a duniya, a yanzu haka da zata iya yin wani abu da ta yi tun kafin Hajia ta bar gidan domin bata hada bukatarsa da soyayarsa da komai a rayuwa, shi din daban yake a duniyarta tana kuma kaunar dukkan abinda yake kauna
A sanyaye mamansa ta sake sakar masa murmushi ta ce" Ka ga Hasan dina, tunda ka kawo min maganar ZAHRA nake sanarwa ubangiji, ka san Allah gagara misali ne, shi ya halici Hajia, ka dauka a ranka in ka ga baka auri Zahrah ba to fa Allah ne ya kadarto ba matarka bace ka ji?, Kar ka saka damuwar nan a ranka, ka kwontar da hankalinka kaima ka yi ta fadawa ubangijinka, in sha Allah ko menene alkhairinsa zamu gani ba sharinsa ba, ka ga komai son da kake yiwa ZAHRA idan ba alkhairinka bace sai ka ga ta zamo gagarumin shari a rayuwarka da dana sani, ni kam baki da matsala da Nasabarta, na san kadara na iya hawa kan kowani bawa, maganar tarbiya kuwa wannan zamani ai ka yi fatan shiriya wa kowa, dan kuwa iyaye ai sunna yi bakin kokarinsu, zamanin ne ya cenza salon kida a dole rawa ta cenza, sai ka cencani
an danka na tsayin shekaru, ka fitar da shi dan saka shi makaranta islamiya ko ta boko, sai ka ga ya hadu da malaminsa wanda ya fika karfi watau abokin banza ya juyar maka da yaro, haka ake tafe ba ji ba gani, Adu'a ake yawaitawa ana fadawa Allah ana kuma yin nasiha, a hankali sai ka ga zuwa gaba an dace, duniyar dake cike da ababen tsoro, ababen wartar farin ciki da nutsuwar yaro?

Sai hakuri, Ama Hasan ka share hawayenka haka ka ji?, Maza tashi ka shirya ka wuce masalaci sallar magariba, kuma ko ita kar ka nuna mata komai ka ji ko?
Chapter 68 · 0% Book details