← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 110

Sashe 26

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me kike tunani ga wanda zai nuna maki iyayenki ne abokannan gabarki?????"
Hankali tashe Zahra ke girgiza kai, gaba daya sai take gannin Mamah bata gane waye Ma'awiyanta ba, kwata kwata sai take gannin a tunanin Mamah fa ma'awiya na iya cutar da ita, ita kam yaya zata fahimtar da Mamah cewa Ma'awiya shine masoyi daya tal da ba zata taba samun irinsa ba a duniya, a jiya tsabar sonta har kuka ya yi, maganar tafia da itama fa itane ta matsa masa ba shine yake so ba, ko a dazu da safe sai da ya nuna mata ba shi kam baya so ya kaita dakin aboki dan yana sonta ya fi so daga gidansu a kaita dakinsa ta nuna masa idan tana kusa da shi zai fi mayar da hankali ya gama ginnin a yi auren, haka kuma tunda take ma'awiya bai taba nuna mata lalata ba sam, ta san wani lokacin yakan dan kure mata waje da ta nuna bacin ranta sai ya matsa dan ya sanar mata shi ita yake so ba wani abu nata ba, ita sheda ce Ma'awuyanta salihi ne, makaranci ne ba zai cutar da ita ba
A sanyaye ta ce" Mamah, dan Allah ki yi hakuri, kar ki yi kuka a kaina Mamanah Dan Allah ki yi hakuri, Mamah du abinda kika gani ba fa laifin ma'awiya, shi walahi ba halinsa bane ire iren halayan macutan samarin nan, a yanzuma idan ya kaini cewa ya yi kilaceni zai yi har sai Allah ya yi mun yi aure sai mu zaunnnnnnnnn.........."
Bata idasa maganarta ba Mama ta dan matso ta make mata baki sannan ta juya ta warto mayafinta dan shine kadai abin duka a kusa ta jimke shi ta ce" Na rantse idan kika ci gaba da min magana kamar ta yan giya zan ci ubanki a dakin nan, ni sa'arki ce da zaki shigo min ki min maganar wai wani katon shege da ya ji take takenki bai tsawatar maki ba bai zo ya sanar mana ba ya zo da nufin daukanki cewa shi salihi ko me?

Ai da salihai sun ji jiki, ke bari ki ji babu mai fuska biyu irin samarin SHAHO! , Kannin ubanki ne shi da zaki ce meye meye?

Kin ga kar ki kaini makura na maki dukan tsiya ta yadda za'a kasa sheda ki, bafa na son shirme , idan wannan ya kawo ki tashi ki tafi kawai, ki tashi ki bani waje na shaki iskar duniya dan kin matse min waje da shashanci a bakinki!"
Sosai fa hankalin Zahra ya tashi, dana sani tashin hankali sun yi mata yawa, da kyar Mamah ta daina fadan sannan ta saka mayafin nan tana share hawaye a boye, ta rasa ina zata saka ranta, wani irin tunani ne ya dace ta yi da rayuwarta, shin da ace yarinyar nan ta tafi da me ta yi kennan?

Anya zata iya ba yarinyar nan tarbiya kamar yadda take tunani?

Anya zata iya rike amanar yarinyar nan kuwa??????

A hankali ta idasa rarafawa har ta karasa kusa da kafafuwan Maman
A hankali ta dora kanta a saman cinyar Maman ta rintse idannuwanta tana jin wani irin dumi na ratsa jikinta, wata irin nutsuwa na shiga cikin jinnin jikinta
A sanyaye ta ce" Mamah, dan Allah ki yafe min, a yanzu na gane cewa bani da hujar da zata sakani binshi, Mamah na shiga damuwa ne dan an tsoratar da ni cewa idan har aka wayi gari wace ta zo da ni ta kasance bata nan ko ta rasu ina zan dosa?

Mamah na kasa duba da cewa a yanzun ma da nake tunanin zamanta nake yi ba nice a gabanta ba, gaba daya kaina ya gama kulewa har nake tunanin eh lalle bani da wajen da zan rayu sama da gefensa dan shi ya nunan zai aureni kuma zai kula da ni, kuma baya kyankyamina, shine ya sa na so binsa, ama Mamah in sha Allah ba zan kuma wannan ganganci ba, dan Allah ki yafe min Mamah "
Idannuwanta dake lumshe tana sauraron Fatima har ta dire aya a hankali ta dago hannunta ta dora a saman nata tana dan dafawa a sanyaye ta ce" Fatima Zahra, zuwa yanzu ya kamata ki iya daidaita tashin hankalinki ta yadda idan kin shige shi zaki nemi mafita ba ki saka kanki a uku ba.............kamar yadda kika sani kowani bawa da irin jarabawarsa, Allah kuwa baya jarabtan bawan da ba mumuni ba..........., Inaga ya kamata ace kema kin fara yiwa kanki yaki idan kika auna a ma'auni kika ga baki da wani laifi, sannan wanda ya haliceki haka ba laifi kika yi masa ba, sai ki yi watsi da du wani mai yi maki neman fitina ki barshi da wanda ya haliceki zai bashi amsar tambayarsa a tsanake........, Kin ga zahra ita rayuwar nan idan kin kula da dan adam ba'a iya masa, baya iya zama sai yana da wanda zai muzgunawa a gefe, in ka zamo shara kowa idan ya tashi kai!.............., Ki dube ki, ki yi tsai ki dube ki, a duniya da me Allah ya rage ki?

Kina da rai, lafiya, muhali, yan uwa,, sutura, ci , sha, hankali, idannuwa....ke komai na rayuwa Allah ya baki shi Alhamdulilah, abin nan da kika rasa lalle nakasu ne a wajen Jahili ba mai ilimi ba!, Zahra ki min adalci ki fitar da ni kunya, ki yi yaki dan kanki ba dan wasu shashashai ba"
Ta saurara tana kallon Zahra da ta dago tana kallonta, wannan abu na Zahra ya riga ya zame mata jiki, ko tana jin tsoron abu ko bata ji idan ka kyautata mata ko ka muzguna mata zata zuba maka ido ne tana bin bakinka da kallo har ka dasa ayar maganarka, idan har ta ci karfinka sai dai ka katse maganar taka ka kasa idasawa
A hankali Mamah ta dora da fadin" Kar ki ce zaki ringa yiwa samari yarda kamar wasu wa'inda suka kawoki duniya, yau fa yau ce, an zo zamanin da muharaminka na iya cutar da kai dan wani dalili nasa ko kuma kadarar rayuwa......., tsakaninki da yaron nan daga yau ki kiyaye,idan auren ne bari ki ji ya fito ko a buka ne ya saka ki,matar da ba'a yi niyar kilacewa ba ake yiwa yau gobe da maganar ba'a gama gini ba, ba'a yi meye ko meye ba,namijin dake so da zuciya daya sai kin juyo ki ga ya damki dukkan wasu abubuwa da suka zame masa wajibi ya kare a kanki dan burinsa dama shine ya kilaceki ya ringa ganninki a gefensa .......ba wai wasu cikin samarinmu ba da suke bin hanyoyi dan wulakantar da mace da zarar sun samu su yi gaba........."
Kanta ta mayar ta sada,jikinta ne ke neman mutuwa har ta fara tunanin me yasa idan ta nuna masa a gidansu babu mai sonta yake sake tabatar mata ai duk duniyarma babu mai sonta sai shi daya kwal.........?

Sai kuma ta yi kokari takawar da tunanin a lokacin da zuciyarta tabata amsar yin tunani irin wannan akan ma'awiya haramun nema gaskiya, dan kuwa ai butulci ne!

"Kin yarda, zaki kamanta nuna masa ya fito,ta yadda zan hade ku ke da yan uwanki a daura maku aure ku yi tafiyarku dakunnan ku? ?????" Mamah ta fada a sanyaye ainun,a dole Zahra ta sada kanta cikeda jin kunyar amsar da Mamah ke so tabata, to ita ta ce mema a wannan maganar?

Ai bata da amsar hakan gaskiya
Mama ta sake rage muryarta tace" kin yarda Zahran Mamah?

Zaki taimakeni mu ba marada kunya?"
A sanyaye ta gyada kanta, hakan ya sa Mamah ta ci gaba da kwontar mata da hankali, cikin hikima tana sake bayyana mata cewa mace take duk rintsi ta kare mutuncin kanta,kar ta ba kowani banza damar ya rainata, domin babu abinda ke iya kawo raini da wulakanci irin a wayi gari mace ta ringa sanarwa kato damuwar cikin gidansu ......

Ko yanka ki ake yi ki iya bakinki, idan zama ya zaunu komai na iya faruwa, namijin nan na iya tunanin baki fa da wajen zuwa sai tare da shi ya mayar maki rayuwa tamkar ukuba, ya hanna maki jin dadin duniya ki ji gwarama mutuwarki da rayuwarki......ki kiyaye lamarin namiji kin ji Zahrana?"
A sanyaye take sake gyada kanta tana sake ba Maman hakuri har dai ta gamsu cewa Maman ta hakura sannan ta mike ta shiga gyaran dakin Maman da ninke ninken kayanta dan ita ke yi dama, sam Mama bata jin dadin na kowa sai nata har ta kusa gamawa Maman ta mike tana fadin" Bara na je na sa a zuba abincin yayanku na san yanzu sun gama"
Da to ta bi Maman ta ci gaba fa aikinta, a kasan zuciyarta abu uku ke dankame, tarin takaicin abinda ta so aikatawa , farin cikin jin za'a bata zabinta, da kuma tarin fargaba da tsoron kalaman bakin mutanen nan biyu da zata iya kiransu da sunnan iyaye a wajenta.....Shi dai baban gida bai ce mata ta yi ko kar ta yi ba, ya dai nuna mata za'a bata namijin ta je ta yi abinda zata yi da shi, sai tale jin dar dar a hakan kamar wani abin ya fada....., Kalaman Mama kuwa haka kawai sai ta ji gabant ya fadi a kansu, duda ta san waye Ma'awiyanta, ama bata son ta ga MAMAH ta ki abu, yawanci fadan Maman ake gani ama a kan gaskiyarta take walahi........., Da kyar ta idasa ta rufo dakin ta tafi nata dakin da ky din
Sai da ta bude ta shige gabanta ya sake faduwa, lokaci daya ta yi tunanin yanzu idan fa sun same shi ana iya dukansa kafin a masa maganar auren?

Kai da ta shiga uku ta lalace.................
Chapter 26 · 0% Book details