← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 110

Sashe 37

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai dukawa wada ba zai hanna a tashi da tsayi ba, ta san soyayarsa da babarsa ko yaya ya kula tana kyautata mata zai kamu da sonta
Dan murmushi ta yi ta ce" In ba dan ina jin kunyar gidan sirikai ba, ai da na leko na gaishe da su mamanku, da kuma sarakuwata, daga nan sai ki rakani idan mun fito sai mu shigo gidan ki ga jikin nasa ki koma ko?"
Wani irin sanyi ne ya ratsa mata zuciya, da dan sauri ta ce" Alhamdulilah auntynmu, walahi ba wani abin kunya, ai dama an fi so tsakaninka da sirikanka a samu shakuwa mai tsananin gaske, dan Allah ki zo ina jiranki, babarmu bata hannani binki koina, ki zo auntynmu na raka ki, na tabata kuwa du inda Baban Abah yake yana kusa da gida, kin san tun rasuwar matarsa baya wuni bai zo ba, yawanci yakan zo da rana ko da dare ya amshi abinci, ki zo auntynmu ina jiranki"
Murmushi ta yi cike da duniyanci ta ce" To dai, bara dai na gani ko zai yiwu, bara nima na tambaya ko za'a barni?"
Ita dai Furera bata ce komai ba suka yi salama, tana mamakin wai in an barta? ta tabbata zata zo ne, in ba abin Laraba ba yaushe ta fara tambaya dan zata fita?

To ita wama yake wani hannata fita?

Ai wannam sai su mararsa yanci, shi yasa rayuwarta ke birgeta sosai, koda yake, ance dama kana mangarin rayuwar wani yana taka ne, ita bata san Tata rayuwar bace abin so da birgewa?

A sace ta mayar da wayar sannan ta zo ta yi kwonciyarta saman kujera tana jiran tsamani , ita kuma a lokacin ta shige wanka dan burinta in ta shiga sai ta jira har ya zo din sannan su fito,, so take yi ta faragwada tata sa'ar, ta san itaa mace ce har mace, babar yarinyar da ake so sosai, babu abinda ta rasa a jikinta, ta tabata sai dai idan Baban gida bashi da lafiya ne, idanma bashi da lafiyar kar ya damu, ita ai ba nan ne damuwarta ba..........ko na komai zata zauna da shi ta rinha rayuwa ta soyaya da shi dan ya isa
______________________________________
A kadan ya dauki awa daya da minti talatin a asibitin nan a office din Abokinsa har aka sanar masa yanzu zata iya tafia gida ya bada umarnin a kaita mota
Bayan an kaitama ya dauki lokaci sunna hirarsu da likita sannan suka fito ya rako shi sunna tafe sunna zantawa zance irin na yau da gobe tsakanin wa'inda suka san junna
Sai da ya zo daf da motar ya juya suka gaisa ya dan dafa kafadar likitan ya masa hirar da su basa ji suka yi murmushi sannan ya karasa ya shige motar bayan ya bude gidan gaba direban ya daga suka fara tafia a nutse ba tare da ya juyo ko sau daya ya kalli wajen da take yin kukan munafurci da rainin wayo ba
Ya kasa yin matsaya daya a mataki daya ya ajiye tarin rashin sannin ciwon kai irin na
wannan banzar yarinyar, irin yadda kirjinsa ke tukuki ba bacin rai da ta sani motsin kirki na zata yi ba dan kar ya gane tana nan ba, sai dai kashhh, bayan abinda ta aikata , a yanzu kuka ne take masu har suka karaso gidansa direban ya silala da motar ya shige ya karasa har wajen bangarensa ya ja ya tsaya yana shirin bude motar a nutse ya budeta a haukace sakamakon tartsatsin tsawar da BABAN GIDA ya saki bayan ya juyo a yan sekwanin da basu zarce biyar ba ya shako hijabin FATIMA ZAHRA ya cirata daga zaunen da take a saman kujera ya dago hannunsa a haukace ya nufo fuskarta da mahaukacin marin da ya tabata da ace ta sha shi da ta samu silar tabuwar barin kai kennan dan ko kato ya kaftawa ana kafta balaki bale wanan yar shangalaliyar y'ar abar a ringa mata sannu du idan tana tafia dan tsabar rauninta, sai Allah ya rufa asiri yaa jimke hannun nasa ya kaima madubin motar dale gefenta duka da shi lokaci daya ya bada tartsatsatsa sannan bai yi watta wata ba , bai yi jinkiri ba ya dawo da hannun da har kwalba ta tsitsigareshi ya hade a wajen da ya damki hijabinta ya cirota ya hade goshinsa da nata da dan karfin da ya sakata ji tamkar an tsaga mata gaban goshi, hsncinsa na gugar nata idannuwansa a waje ta yadda ta rintse nata idannuwan a haukace jikinta na rawa hankalinta a tashe ya dantse lebensa, ya sake dantsewa da kyar ya saki muryarsa na fita a galabaice sannan da fada fada ya ce" Ba zaki rufe min baki na ji da abinda yake da mahinmanci ba shirmenki na?

Ba zaki rufe min baki da kukan banza da wofi ba?, Fatima zahra ba zaki ari kunya irin ta mata ba da sannin ciwon kai ki yi gumm da bakinki asirinki a rufe ba?, So kike sai kin sakani a uku na saka maki hannu a fatar jikin............a fatar jikin ki ZAHRA?" YA idasa fada a sanyaye, tamkar ba furucin karfi ya faro da shi ba,
Difffff wajen ya dauka tamkar babu su a motar
Domin kukanta tunda ya dagota ya tsaya sai barin zuciya da tashin hankali dake sakata haki idannuwanta a rintse, hannunta na dama a saman hannunsa mai dauke da gargasa wace ta mimike tsaye, dayan kuwa yana ajiye a saman kirjinsa ta danna da karfin da Allah ya bata a kokarintaa na tare shi da kare shi kar ya kasheta har shirun ya dan so yin tasiri a kwakwaluwarta ta ji ya saketa daga cirotan da ya yi ta koma da karfi ta zube a saman kujerar har ta dan zauna a kan yar kwalaben da suka zubo kadan cikin motar lokaci daya kuma ta bude idannuwanta ta sauke a bayansa a lokacin da ta ji karar rufo kofar motar da karfi tana kallonsa har ya bacewa ganninta ta juyo tana kaallon gabas da yamma kudu da arewa, tunaninta a tsaye cak, hankalinta tamkar ba nata ba, ta yi wani tsuru tamkar mahaukaciya ta rasa me ke yawo a cikin kwakwaluwarta har wani soja ya zo da tarin kwanonin mamanta ya bude gidan gaba ya ajiye ya koma jim kadan ya dawo ya bude gefen da take ya saka yar tsintsiya bai ce mata komai ba ya share kwalaben nan tassss sannan ya rufe ya shuge gidan gaba maimakun direban da ya kawo su ya tayar da motar bai ce mata ufan ba ya dauki hanya, ita kuma ta zamo tamkar gunki ta kasa ci gaba da yin kukan alhinin da take ciki dan zuciyarta ta riga ta kasu gida biyu ta kuma sanar mata idan ta yi hauka a gaban sojoji su nasu haukan mai dalili ne kuma babu wanda zai kule si, su din an riga an daure masu a kasa ana duka masu, ta riga ta yarda a yau a kaf cikin sojoji babu mai imani da tausayi da jin kai, tun daga kan Yah Amir har zuwa mai gadin Sojoji babu mai tausayi da jin kai da lalaba bayin Allah, sai aukin cin zali da son halaka bayin Allah
Aa nutse ya tukata har suka karaso gida
Sunna zuwa aka bude dan an ga motar MARSHAL ne
Karasawa wajen tsayuwar motar ya yiya tsayar yana hangen su FURERA da Laraba wa'inda ya ga sunna wani irin abu, ita Furerar tana son guduwa ita kuwa ta rikota sai wani sisine kai suke yi
A hankali ya ce " Hajia, sire yace idan kin shiga ki je a matsayin wace ya aika dan ki wanke kayan nan ki kawo"
Bayani ya yi, ama sam bata fahimce shi ba, ita dai ta san tana ta faman bude kofar ama abin ya gagara sai da ta ga ya fito ya bude mata ne ta iya gane an bude ta ziro kaffafuwanta a tare sannan ta fito daga cikin motar lokaci daya cikinta ya wani irin yamutsawa ta nufi wajen kasa dan dukawa, sai dai bata idasa ba ta kece da amai a nan ta duke jikinta har rawa yake yi yana yi mata wani irin karkarkarkar lokaci daya su FURERA sula sake wara idannuwa a kanta da mamaki da tsoro da sake son gane meye ya fitar da ita daga motar Baban gida, daga ina take?

Gannin yaronsa ya saka lokaci daya suka yanke cewa ai tare suke saurayinta ne, ama lalle an yi dan iska har ya samu wajen saka shegiya a motar Baban gida?
gannin ta fito tana aman nan kuwa ya saka a tare suka zarro idannuwa lokaci daya Balaraba ta ce" Ke amai ne kyautar gidanku ke yi?"
Itama a rikice tana kallonta ta ce" Amai?, Innalilahi amai?......."
Sai kuma ta yiwo gaba hankali tashe ta nufo inda Zahra ta gama aman sojan nan na mata sannu yana rike da kayan dake dauke a hannunsa
Tana zuwa ta tsaye ta harde hannayenta tana jifansu da wani irin kallo a dake ta ce" Daga ina kuke"
Da dan mamaki yake kallonta, a sanninsa dai ya'yan gidan nan gaskiya akoy girmama na gaba da su komai talaucinsa, hasalima zai iya cewa magana bata taba hada shi da su na tsayin lokaci ba, idanma an yi katari an aiko shi ya hadu da wata sai dai dan ya bata hanya ta shige bayan ta gaishe shi, sai yannayin maganar Furera ya saka shi dan gannin wani iri, furera ai kanwar bayansa ce gaskiya, ama kuma ta yiwu ita ta fita daban a cikin yan uwanta
Kanaa ya dauke kadan ya ce" Daga gidan Sire muke"
Sake tsatsare shi da ido ta yi Zahra kuwa ta mike tana kabe jikinta da goge jikin nata tana so ya bata kwondon ta yi ta shige dan zazabin da take ji aa jikinta tamkar zai kifar da ita
"Wani sire din?

A ina ka hadu da wannan ha
r ka kawota tana amai?

Aman me take yi ne?
Chapter 37 · 0% Book details