← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 110

Sashe 104

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rabonsa da murmushinta tunda suka fara karyawa, baima san ko ta ci wani abin tun daga lokacin ba ko bata ci komai ba, gata ita dama ba damuwa ta cika yi da abincin bama, sai ya zo yake sakata a gaba fa ta dan tataba
Shigowar AMIR da dukawarsa yana gaishe shi ya saka shi dawo da dubansa kansa yana amsawa da dan sakin fuska har ya tambayeshi iyali, nan yake sanar masa ai gobe in sha Allah zata zo su wuni tare da dangi , nan shima ya zauna, Mama kuwa ta kuma kiran Zahrah a waya kan ta kawo wani plate da cokali Amir ya zo shima, nanma ta dauko plate din ta saka hijabinta ta dauko da goran ruwa ta sake dawowa ta duka kamar yadda suka saba dan gaisar da Amir sai ta ga da sauri yana fadin" Kai, rufan asiri babar yaya tashi dan Allah Mama ji fa, tashi kin ga rufa min asiri kin ji?"
Mama na daria ta ce" Ke yanzu ai babar yaya kike ko zanewa ta kama ai inaga yanzun kam ba za'a hada da ita ko kuwa Amir?"
Amir ya gyada kai yana dariar shima ya ce" Wane mutun inji mutuwa, yanzun bulala sai dai ta hau kan Auta kuma"
Mama ta gyada kai tana amsar ruwan da ZAHRAh ta kawo mata sai sada kai take yi dan ita kunyar maganar take ji ta ce" Autana baiwar Allah, in sha Allah bama zata yi abin a daketa ba, ai su Zahra su suka daku, ita da rukaya da Adawiya?

Sun yi yayinsu daidai gwargwado"
"Kin ci abincin rana ne?" Ya fada a sanyaye yana kallonta a lokacin da ta juya fa nufin komawa wajen masu aikin
Daga Mama har Amir din shi suka kalla, lokaci daya Maman ta kawar da dubanta tana danne murmushinta, dan yannayin da fuskarsa ta bada zata iya rantsewa ta jima rabonta da gannin irin haka, fuska ne ta rarashi, ta neman kai, ko mema zata ce?

Wani irin laushi da sanyi a saman fuskar abin ba'a cewa komai, kai Alhamdulilah wai Allah?

Haba alhamdulilah, yanzu ta san yaro ya yi aure, ya auri daidai da zamaninsa, ta yadda zai san duniyar mace kala kala, ta fahimci da dan damuwa tsakaninsu ama nata ido ne ba zata taba tankasu ba sai idan ta ga abu zai rikice bi'izinillah
Dan dakawata ta yi daga tafiar, dan ta tabata da ita yake maganar nan ta dan juyo kadan ta dan kalli fuskarsa tana hanna kanta kallonsa ido cikin ido dan walahi wani irin missing dinsa da take yi tamkar ta shekare bata shiga kirjinsa ba, ji take yi du babu dadi, ji take yi kamar ta jima sosai bata kwonta a saman kirjinsa ba
A hankali ta ce" Na koshi"
Sannan ta wuce ba tare da ta kuma saurrarawa ba
Idon da ya tsurawa wajen, da karra sanyayar da dubansa da ya yi ya saka Amir kiris ya hanna ya kwala ihu daga zaunen da yake
Da sauri ya mike ya nufi hawa sama yana hade matatakalar hawan har ya haye sannan ya ringa fadin" Yes, yes yes, hahahaha kai subahanalah, haba sai yau na fita a shaku, duda na riga na yarda ama sai yau na idasa yarda, lalle yayanmu kai din mutun ne mai matukar hadiye bukatarsa, kana ji kana gani wani shege ya nemi baudar maka da ita?

Kana ji kana gani take zance?, Tap gaskiya yayanmu wani kawar da kanma ai cutar da kai ne, yo ni yayama zan iya wannan aiki danye?, Lalle kana zaune nake zaneta ?

Shi yasa idan suka yi laifi kake zama a zane su kana zaune?

Kuma yayanmu ai sai ka ja abinka ka adana zaka bari a dakar maka, kai soyayar manya ba dai saka shauki ba Alkur'an " shi kadai ya gama shan dariyarsa sannan ya dawo yana kama kansa ya zauna a lokacin Maman ta mike ta tafi ta saka su zuba abinci su ci, domin a raunane yace da Maman na safema bata ci ba, bai sani ba ko bata da lafia ne?

Ita din da kanta sai ta gaza zaman ta mike tana fadin bara ta sa su dakata su ci abinci hakanan su sai son aiki har a manta ciki ana aiki...., Sai da ya ji wannan ya iya sauke ajiyar zuciya harma shima ya zuba abincin ya shiga ci , nan Amir ya zauna shima ya zuba din dan babu wanda ya ci na rana sunna cen wajen makokin
Tunda ya fita sallar magariba kuma ba shi ya dawo gidan ba sai kusan sha biyu na dare, ya dawo ne da waya kange a kunnensa sunna magana shi da Aban AHMAD, a haka ya ringa haurawa da dan sauri ya shige dakinta ya kunna fitila
Ganninta lulube cikin bargo ya saka shi zuba mata ido cike da wani mamakin, idan bai manta ba akoy fitar da ya yi ya kai kusan karfe dayan dare kafin su dawo, a falo ya samu ZAHRA tana jiransa, sai da ya zo ya yi wanka ya ci abinci sannan suka kwonta, ama yau ZAHRAh har ta yi barci ta kyale shi?

Yanzun kam ya yarda ya mata laifi kuma dai zai ji ko menene
A hankali ya ce" Wai in tambayeka, kana iya tashi da mace lafiyar Allah kunna cim abinci kana iya yi mata wani laifi ne?"
Aban Ahmad dake cike da farin cikin an samu da kyar Maman ZAHRA ta yarda zasu shiga jirgi tare zasu dawo tare, a jirginma ta yarda zasu yi zama na kusa da kusa ne a haka Doctern kuwa ya kwatanta masa aikin sake shiga rayuwarta ya rage nasa, a hankali a hankali yanzun yana iya birgeta kamar yadda wani namijin ke iya birgeta ne ya saka shi farin ciki mai girman gaske har yake sanar masa
Ban Ahmad ya ce" Kamar yaya kunna cin abinci?"
MARSHAL ya dan yi tsai kafin ya ce" Yo kana ji, lafiya fa muka zauna muna cin abincinmu, komai dai a sanina yadda muka saba ne fa, sai kawai dai aka yi kirana ta bani wayar ta yi tafiyarta, tun daga shi maganar kirki wannan bata hadani da Zahrah ba, harya abinci sai mama ne ta sakata ta ci, yanzu kuma ta yi barci na tabata na darenma bata ci ba fa"
Aban Ahmad ya surbi lipton yana murmushi yana kada kafa ya ce" To ko kiran naka ne da aka yi bata so ba d'an nan?"
MARSHAL ya yi tsai yana tunani, kiran nasa?

Ama ai an saba kiran nasa a haka kuma ita din dai ke bashi ko?

Marshal ya yi dan tsai yana tunani, kiran nasa?

Ama ai an saba kiran nasa a waya kuma ita din dai ke bashi ko?

Wace ta yi kiran nasama ai ta sha kiransa ita Zahran idan tana kusa ta bashi wayar normal su gaisa ko?

Me yasa wannan zai bata mata rai?

A sanyaye ya zauna yana fadin" Kiran nawa fa yayar marigayiya ne ta yi, kuma ai ta saba yi ko?"
Aban Ahmad ya saki murmurshi ya ce" to dai inaga yanzun abin ya kaita makura ne ko?

Kaima ka san fa mata basa son ire iren haka, idanma soyaya kake yi da matar nan ka yi a waje in aurenta kuma zaka yi sai ka yi kowama ya huta ko?"
A sanyaye sosai MARSHAL ya ce" Ni bama ko daya, ka ga maganartama fa an gama dan kiran da ta min dinma na ta ga samaci ne kuma da sunnana, shine fa take min rantse rantsen ita bata da ruwa da tsaki a mutuwar, kai dai karshema an gane mai siyar da abubuwan nan itane ta basu abin basu san menene ba suka yi anfani da shi har ya yi ajalin marigayiya, ni nama sanar mata to wannan shine dalilin kusancina da ita, tunda an je an gano menene gabanan kira in dai ba na abinda aka san ina iya bada wani talafi a ciki ba ta yi hakuri ta daina, ni yanzun freind yan matanma ai bana yi kwata kwata fa"
A hankali Aban AHMAD ke tikar dariyarsa har yana shawagi a wajen da yake tsaye, kasa kasa ya ce" Kai, kar fa ka yarda yar shila ta shiga gabanka fa, yan mata ai dolema ka yi su, ka fa dage ka zare mata ido kar ta nemi fin karfinka fa......"
Shiru ya yi a kadan na minti daya , kasa kasa ya ce" Abinda zaka ce min kennan?"
Aban Ahmad ya tabe baki yana dage kafadu ya ce" ni me ka ce min ranar?

To kowa ya yi ta kansa!"
MARSHAL ya shaka sosai , a kausashe ya ce" Ba laifi, zaka zo ka neme ni ne ina nan, kuma babu zare matan da zan yi!"
Daga haka ya kashe kiran ya ajiye wayar sannan ya zuba tagumi yana kallonta da tunanin to in banda Zahrah menene na su yin fushin a nan kuma?

A hankali ya mike ya shiga tubewa ya dauki tawul dinta ya nufi bayin dakinta dan yin wanka
Wankan ya yi ya gama ya fito da tawul din daure a kugunsa ya haye saman gadon a hankali
Bargon ya yaye gaba daya, wanda sai da ya yi dana sanin yaye shi, domin y'ar gidan Mama a jikinta sutura mai sunnan sutura pant ne kawai, shima rabi ya shige barin abin rabi ya rufe barin, ta yi wani irin kwonciya na fitina da neman fitina , kai innalilahi wa inna ilaihi raj'une wayo jama'a, a rikice ya rufeta ya kwonta a jikinta ya tiketa sosai a cikin kirjinsa riko na runguma mai kyan gaske wanda hakan ya sakata sake rintse ido da karfi tana fatan Allah ya sa kar ta gaza rike kan nata domin a motsinsa babu wanda baya kunnenta, yayama zata iya yin barci bai shigo ya sakata a jikinsa ya ringa shafa gadon bayanta ba?

Yayama zata iya barci bata ji shi a tsakanin kirjinta yana sauke zazafan hucin dake dukan kwakwaluwarta ba?
Chapter 104 · 0% Book details