← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 110

Sashe 78

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaima ko ka samu ka shige da wuri, wannan lamari fa ba'a son tsaiko da bata lokaci, tunda dai yanzu an daina cika dare daukan amare, suma da kansu angwayen a basu iyalansu su je su adana ko
an nan?"
Ta kasa kasa yake kallonsa, yau shi ya shiga uku ya lalace jama'a so ake yi karfi da yaji sai an saka shi a uku?, Yanzu ba dai zai barshi ya shaki iskar duniya daidai ba ko?

Haka an bashi abincinsa zai ci a nutse sai gannin hannu ya yi a cikin plate dinsa, kuma mutumen nan ya ringa hira magana ta sako da sako yana kakaba dariya abinsa, ya sa aka yi ta masu hoto ana ba'a taba gannin sirikai aminai ba sai a kansu, har wani kuncinsa yake tabawa shi kuwa wancen shegen RHISA dama gayacen ya rantse sai ya kai amarya, ba laifi in dai RHISA ne?

In sha Allahu dajin karshen watan nan da shi za'a je, yo in baima turashi daji ba ai har an dasa ayar tambaya a kansa
Hannunsa ya janye yana girgiza kai ya nufi hanyar masalacin, Amir da Aban Ahmad suka saka dariya kasa kasa Amir ya karaso yana fadin" Yaya gaskiya yau an sako mana Oga a gaba, kana gannin sai kumbura yake yi, so yake ya rama ama na rasa me ya rike harshen"
Shima yana dariya ya ce" Kai me zai rike harshensa, ban dai kaishi karshe bane har yanzu, ina dai fatan in an jima na kaishi karshen, yaya maganar kajin ka hado da ni?"
Amir ya gyada kai yana kyakyata dariya, ya ce" Ai harda kai aka hada a list Yaya"
Baban Ahmad ya ce" Ya yi dan albarka mu je masalaci ka ji an fara, mu je mu fito ka ga mu shiga aiki"
Da wannan du aka yi masalaci dan gabatar da sallar magariba
Ana fitowa aka shiga raraba jama'ar kamar yadda aka saba, dan ba aikin sai an yi na wannan a yi na wancen bane
Babangida na tsaka da daidaitawa MAMAH ta yi kiransa take fada masa sun fa sun gama komai, sannan ta tambayeshi yaya yana da nasihar da zai yiwa yaren ne?

Shiru ya yi na lokaci mai dan tsayi, kafin ya ce" Aa Mamah, zan je gidan kowace na hadata da mijinta na basu hakurin zaman yau da gobe in sha Allah, a shiryasu kawai yanzu haka kowace an zo daukanta ai, idan an tafi da amaren muma sai mu je daukan na wajenmu, kin ga muma mun sanar a shirya da wuri dan bamu da wani event kawai za'a kai kowace gidanta, kin ga kafin su gama da salamar yan kawo amarya dare ya yi sosai, a shiryasu kawai , shin iyayen kun raraba kowace mai yin rakiyar?"
Mamah ta ce" Eh mun yi ai Baba, maman Furera ce dai bata da lafiya wai ba zata samu kai amarya ba, sai Luba ta maye gurbinta, kuma ka ga ka yiwa kanwarka magana dan kuwa tarda ita ta yi ta mata sumul, ka ga ta iya rigima ni wanda aka yima ta isa, bana so a yi ta yawo da abin ga gida cike da mutane ka ji Baba?"
Kasa kasa kawai ya iya cewa "Uhum, a fitar da su"
Sannan ya juya bangaren mutane suka karasa kimtsa komai
Cikin aminci da yardar Allah aka shiga sada yan matan da gidajensu, sannan summa mazan suka dauki hanya kowani ango da taron abokansa da kuma daya daga cikin yan uwansa maza sai dangin mahaifiyarsa sun je daukan amaryarsa, Amir ne kawai ya zamto abokan daya ne du yan wajen aiki ne, sojawan ne tafiyarsu dole ta zo daya da baban yaya aka dauki tasa amaryar aka kaita gidanta madaidaici mai kyan gaske, gida mai dauke da dakuna hudu da kicin madatace da bayi biyu daya ta daki daya ta waje, masha Allah gida dai ya ginnu dan ya ci bulo ya kuma ci gilashi sai san barka
Daga nan fa aka nemi watsewa sai dai RHISA ya ce to ai ba'a kai ta OGA ba
Nan fa aka fara ja in ja, yana ai a cikin gidan ne sunna ai ya dace su rakata har bangarenta itama, itacema ya dace a yiwa haka
Da kyar da jibin goshi Amir ya samu ya raba rikicin ya raba su da ja in jar sannan ya sa Yayansa a motarsa da Baban Ahmad da ya kasa ya tsare suka nufi gida bayan ya ba Baban Ahmad sakonsa na gashi
Tuki Baban Ahmad din yake yi hankali Kwonce ya saka kida a motar yana dan karkace kai ya dan gyada kai sai kuma ya dawo da dubansa bakin titi ya ce" Allah mun gode maka dai da ka gwad mana mun aurar da yaya"
Shi dai bai amsa ba, bai kuma ce ya yi shiru ba, har suka iso gidan ya tuka shi har cen kusa da bangaren Mamah ya taka birki yana fadin" Allah ya kawo mu fito na raka ka"
A zabure ya bude idannuwansa ya sauke a kansa, duba yake masa irin na dan Allah ka rufan asiri mana?

Shi kuwa ya kankance ido ya ce" Kai bude idonka kana wani kanen ido ,
an nan me kake nufi ba zan raka ka ba?"
Hannunsa ya miko ya rike nasa, a hankali ya ce" Ka bari mana freind dan Allah na tuba ka ji?, Ka ga wajen MAMAH nema zan shiga kai kuwa ai yanzu dare ya yi ba zaka shiga ba cen ko?"
Karra kankance idon ya yi sai kuma ya saki murmurshi yana dafe gaban goshi ya ce" Kai Allah na gode maka da ka mamayeni da zuciyar tausayi, gaba daya ka ga zuciyata ta karaya, ungo to maganin nan ka je da shi sai gobe in sha Allahu zan zo da sasafe ka ji ko?"
Har sai da ya sauke ajiyar zuciya ta samun rabuwa da Aban Ahmad, ba da gardama ba ba da komai ba ya amshi ledar, kuma kwata kwata hancinsa ya kasa jiyo masa kanshin abin cikin ledar da komaima, hasalima kawai amsa ya yi ya bude ya fita yana daga masa hannu shi kuwa har jinjina masa yake sannan ya kunna motar ya tafi zuciyarsa cike da begen son gannin NANA ama kuma ya yiwa MAMAH alkawarin ba zai je inda take ba kwata kwata sai an gama taron nan, yana cikin harkar fitar da ita nema waje dan ya amshe ragamar abin daga hannun Babangida yace a barshi ya yi dan Allah
A gajiye ya bude kofar falon ya shiga da salama kasa kasa a bakinsa
Dif salamar ta katse, sandiyar ikon Allahn da ya sauka a idannuwansa
Su uku ne a falon, Luba, Mamah sai wannan yarinyar
Bara ku ji, yarinyar nan sanye take da wando dogo baki irin mai lafewa a jikin nan fa tana shafawa Mama wani abu a kai o meyema oho, kuma salamarsa bai sa ta nemi abu ta rufe jikinta ba, saima kallon Luba da ta yi bai ga hararen da lubar ta sakar mata ba, ya dai ga ta sada kanta tana jan rigar wandon wace ita dinma bakinta tsayin jikin bawa ba zata rufa maka asiri daga awon da akai mata wajen yinta ba ta karra yin kasa
Mama ta yi iya yinta ta hadiye murmushi dake tukarta tana ayana' Eh lalle Lubabatu na barki, ga lafayar yarinya da hijabinta kin ce da wannan zata zauna kuma ba mai rakata shi da ita zasu tafi?, To Allah ya kiyaye ni kam yaren zamani tsoro kuke bani'
A bayane kuwa ta ce" Yauwa Baba, sannu, sannu da zuwa, kai yau an sha gajiya walahi, ke ZAHRA maza dauko hijabin naki ku tafi kawai bama sai ka zauna ba ka ji Babana?, Je ki dauko hijabin naki mana ke kuwa Fatina?"
ZAHRA ta hadiye hawayenta, ta juya tana hade tafiyarta sumui sumui ta nufi sama dan dauko hijabin nata
BABANGIDA bai dauke dubansa a kanta ba sai da ta bacewa ganninsa ya shigo da dan sauri yana galawa Luba harara dan baya son yin maganar a gaban yara ya ce" MAMAH, wani irin ta dauko hijab ta bini, kuma ana kallonmu sai mu fita da ni da wannan y'ar mu je cen?

Haba MAMAH to in a cen kika so ta koma yau me ya hanna ita a rakatan?"
Luba ta yi saurin fadin" Lah yaya sai kace ba matarka ba wai ana kallonku?

To yanzu yayanmu ai ko an kalleku na fatan alkhair.........."
Dif ta yi dan hararen da ya zabga mata, ta mike sumui sumui ta yi kicin dan da idannuwansa ya mata alamar ta bar masa wajen, sai tura baki take yi tana satar kallon gasasun kajin dake leda dan kuwa kanshinsu ai shi ya sanar da wanzuwarsu a ledar
Mamah ta hade gira ta ce" Ban gane ba, to gaka gata sai kawai mu raka yarinya mu barta ita daya kwal a wancen mamakeken ginin da ka tafka a barota?

Ka san dai babu wace zan hadata ta yi mata zaman daki, ni kuma ai uwa ce ba zuwa zan yi in zauna mata ba ko Baba?"
Zai yi magana ta sauko, sanye da dogon hijab har kasa, ama walahi hijabin gaba dayansa shara shara ne, gashi dai baki ne ama ana iya gane wando ne a jikin yarinyar nan Allah kuwa sai dai in mutun makaho ne
Hadiye maganarsa ya yi da mamaki yana kallonta , sosai yake son rufeta da fadan wannan iya shegen na son yawo tsirara, ama yana gudun a yi masa wata fasara, kuma yana hangen Luba leke take yi daga kicin din cen, shi baima san yaushe ta rainashi ba walahi!

A saukake ya mike yana yin gana ya bar ledar nan a nan
Mamaj ba da tunanin komai ba ta ce" Ka bar ledar fa, ka ga har mai ya zube min a cafet , Lubabatu dan Allah karo masa leda wannan ai kafin ya isa man kajin nan du ya kare a hanya!"
Wani irin birki ya ja ya juyo a haukace ya kalli ledar
Kallo na son fahimtar yaren Mamah....., ka me?
Chapter 78 · 0% Book details