Sashe 30
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikinku nan waye bashi da y'a mace?
Idanma baka da ita kana da uwa kana da kanwa ko yaya!, A zamanin da ya zamto baa baba ba yaro kowa burinsa ya kai ga mutuncin ahalinmu bayan muna kafa kafa muna bi da adu'arma bale mun barsu fitowa tsirara?
Tsirara mana tunda har zasu iya fitowa da yar shiga su je inda suke so, me zamu iya hannawa ko me zamu rika dan kare kawunnanmu?, A hakama duniya ta cika da fyade da abubuwa kala kala bale an sake rikewa shedan ganga?..........
Wani namiji ne lafiyaye zai ga macen da take irin ra'ayinsa bai ji yana son kadaicewa da ita ba?
Daidaiku ne Allah ke tsarewa da afkawa matan a yanzu haka, bale an sake kawatawa?
Bari ku ji baki dayanku, da farko niyata ba zan saka hannu ba kawai ku je ku yi abinku shikenan ku kuka sani ku da conscience din ku da kuma gobenku, ama a yanzu na kula abin harda rainin hankali da shiga hurumin ubangiji, babu wanda zai buga mana wannan a cikin gari, wanda ya shirya yi kuwa ya fito mu je, babu wanda ya isa ya buga mana irin haka koda a kafaffen yada labarai ne, taya bera bari ne!, Yin hakan bude kofa ne da sake rike masu wando su yada manufarsu!, Ka yi hakuri sire ama haka din sam ba mafita bace idan ka tuna abinda kake ciki da su Salima zaka gane inda na dosa"
Daga haka ya juya ya fice rai bace ya karasa wajen motarsa ya shiga ya wani irin figeta ya juya ya bar masu gidan
Sai a lokacin Joe ya sake tada tasa harzomar , fadi yake yi ba zai iya kyale wannan abin ba, ba zai taba iya hakuri da wannan cin zalin ba, sai ya kai kararsa kotu an bi masa hakinsa, dan yana ogansa a wajen aiki ba yana nufin ya isa ya wulakanta shi haka ba!
Da kyar Minister ya samu ya hanna su yawan magana da bakunnansu, jikinsa du ya yi sanyi da maganar nan, bama da ya tuna masa abinda yake ciki da yarsadaya cilo mace wato Salima da kuma yan uwanta, tabas Salima idan har ta ga wannan abin ya shiga ukunsa, ya tabata har ta yi yawo tsirara in an yi magana tace su suka halata mata, a dole ya ce da su zasu yi wani zama zuwa gobe dan yana so kowa ya je ya huce ya yi tunani sannan su sake dawowa, ya riga ya dauki niyar in sha Allah in dai sun dawo din shima ba zai saka hannun ba, zaima yi kokarin fin karfin su Joe, dama sunne masu maganar da kuma irin kudin da hakan zai iya kawowa ya saka shi ya yarda.....da wannan du suka rarabu kowa ya kama hanyarsa
____________________________________
"Na kawo maki maganar nan ne, dan ki karra zama ki yiwa kanki karatun ta nutsu ki dubi yarinyar nan, koda baki jata a jiki ba ki dan ringa sasauta mata kina nuna mata tana da daraja a idannuwanki Nana" Mamah ya fada a nutse bayan sun zauna a cikin falon Aunty amarya
Sosai zuciyarta ke dokawa, mene?
Ta dauki kaya zata bi kato?
Ya Allah, a hankali hawaye ya shiga neman bale mata, tana ta kokarin sharewa ama abin ya nemi cin tura har sai da ya samu fitowa sosai, muryarta cikin kuka ta ce" Dama me za'a yi jira fa y'a irinta?
Idan kin ga zata tona maki asiri kema ki barta ta bi shi kawai, ita a cikin shegunma nata mai tsauri ne, babu yadda za'a yi sai ta aikata masha'ar ai, idan halin ubanta ne haka ai dole Allah ya rama a kanta dan a sanina ita daya kwal ya malaka a duniya har na baro kauye da cikinta!"
Mama ta sada kanta, zuciyarta na dokawa, ranta na sake bacewa,
Ta dago tana dubanta rai bace, a cikin muryarta ta ce" A kauyen na Kudus?"
A zabure ta dago tana kallonta, jin ta ambaci sunnan kauyansu, bayan a sanninta ta san babu inda ta ambaci sunnan kauyen nan ko da wasa
Mama ta girgiza kanta da takaici ta ce" Tabas ke din ba mai godiyar Allah bace, ba kuma irin matan dake duban tashin hankali da fuskar fahimta bace!, Ke kin gudo dan kin tashi kin ga mutin an ce uncle dinki ne ko?
To bari ki ji abinda baki sani ba, mutumen da kike kira uncle ua zo gari da mahaifiyarki da ke ya kuma sheda cewa ke mahaifiyarki kanwarsa ce ke kuma y'arta ce wace sula hada uba daya, uban da ba'a san wane ne ba, tana zaune a gidansa ne ya bata muhali, abinda ya kasheta daban, ta yiwu ba dan uncle dinki ya haike maki ba, ta yiwu bama uncle din naki bane.....domin da wuya a wayi gari dan halak ya aikata irin haka, du inda kika tsinci haka ki yi dogon bincike zaki ga wajen da ya samu tawaya, Nana idan baki sani ba ki sani mai gari ne da kansa ya amsa kirana, dan na dauki Zahra da mahinmanci, ya sanar min cewa lalle ba uncle dinki bane, mahaifiyarki ta baro gidan mahaifinki ba rasuwa ya yi ba bisa wani dalilinta, mahaifin naki shine ya zo kauye yana nemanki aka nuna masa uncle dinki, yanzu haka uncle dinki ya gudu ba labarinsa dan asirinsa da ya nemi fitowa da kansa ya bar kauyen, Malan kuwa shi ya sanar min sunnan kauyenku!, Mai garin yace mahaifinki sanane ne , dan gari ne kuma ya bar sakon idan an ganki ko an ji labarin inda za'a same ki a sanar masa.........sai ki sake daurar aniyar muzguna mata, idan Allah ya tashi saka mata sai ya saka mata da kyau, abinda nake iya tuna maki shine ki yi kokari ki nemi mahaifinki ki bincike shi, ta yiwu abinda kike gudun a jikinsa yake , wanda ya haike maki kuwa har kike neman kashe kanki da baiwar Allah ba jinnin mahaifiyarki bane!
Tana gama fada ta mike ta juya ta fita tana mako mata kofarta, makowar da ya saka Aunty Amarya mikewa tsaye gabanta na faduwa, hankalinta tashe ta daga kafarta ta............
Tana gama fada ta mike ta juya rai bace ta fita a falon ta maro mata kofar da karfin da ya dawo da Aunty amarya daga mutuwar zaunen da ta yi
Hankali tashe ta mike ta daga kafarta da mugun sauri ta bi bayan Mamah har tana harde tafiyarta ta fito daga bangaren nata ta nufi bangaren Maman ta bude ta shiga idannuwanta har sunna rufewa a sanyaye ta yi salama tana kallon Maman da bakin dake zaune, ama ta kasa budar baki ta gaishe su saima zagayewa da ta yi ta kama hawa matatakalar bangaren na Mamah ta nufi sama, shi kuma Aban Hafeez ya samu kansa da binta da kallo a zuciyarsa yana tambayar kansa wannan din kuwa wacece?
Baban gida ya dan sake zubawa yannayin Maman ido gannin itama karfin hali ne kawai take yi tana gaisawa da bakonsa ya saka shi mikewa yana fadin" Aboki, mu je ku gaisa da Aba na kireshi yace yana falonsa"
Mikewar ya yi shima dan sarai ya fahimci akoy damuwa ya yiwa Mamah salama suka fice yana fadin kafin ya koma zai dawo su zanta
Bayan fitarsu Mama ta koma sama, duda tana jiran dawowar Zahra da Auta da ta aika bangaren Maman sufiyanu amso mata man zafi, ama ta tabata wadda ta haye saman cen tana cen kamar zata mutu, dan haka ta haye saman ta bude kofarta ta shiga da salama
Turus ta yi tana kallon Aunty Amarya, wace ta cire hijabin jikinta, ta barbaza gashin kanta tana rusa kuka, a zaune a kasa ta tataro kaffafuwanta ta dora gwuiwoyin hannayenta sai kukan take yi harda tari hankalinta du a tashe
Sallalami maman ke yi a hankali tana kallonta
Dagowa ta yi tana kukan ta ce" Maman Baban gida dan Allah ki sanar min me maganarki take nufi, na roke ki ki sanar min abinda binciken nan ya kawo maki, na tabata in dai Baban gida ko Amir ne suka yi zasu kawo shi yadda ya dace dan kuwa sai dai in ba'a basu sunnan mutun da garinsa ba, Mamah me kike nufi da cewa wanda ya samar min cikin wannan yarinyar ba ya'yan mahaifiyata bane?
Shin mamah *NI CE SHEGIYAR?* nake kyamatar wata ko ubanmu daya da yarinyar nan?
Ina nufin mahaifina ne ya........"
"Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, ke kam bakinki bashi da albarka ne ko wace irin masifa ce wannan kike janyowa kanki ido rufe?
Mahaifinki kike nufin ya samar maki cikin yarinyar nan?
Subahanalah, subahanalah, Allah ka raba mu da mutanen da basa tauna magana kafin su fadeta, ke wai me kika tara banda bakin hali ne?????