← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 110

Sashe 64

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai bari ka ji bama neman kai da ita, kuma ba zamu zauna mu wani bude masa sirrinta ba mu tashi mu tafi ya je ya fasa ya yi gaba yana yayatawa, tsaf zan iya tsinke masa du wani abu mai shirme a jikinsa!, Sai me idan ba zai aureta ba ai zata samu mai aurenta, yarinya shekara ashirin an wani sakota a gaba kamar wata uwar mata, wasu mazan mace mai shekara ashirin da biyarma ba mace bace a gabansu bale wai ashirin, ba za'a masa zancen ba ya kawo a daura masu auren in ya ji daga baya ya sakota ai ba dangi ta rasa ba!"
Lalle yannayin fadan na MARSHAL yana bashi mamaki, sosai yake fada da daukaka maganar kamar wanda aka yiwa laifi
Aban Ahmad ya tabe baki ya ce" Kai wai toh ni me na maka da zaka rufeni da fada, kuma kake cewa wani wai mai shekara ashirin yarinya karama a wajen wasu mazan kace dai a wajenka, kaine ba zaka iya zama da mace mai kannanun shekaru ba, lalle ina mai tabatar maka kaine baka san mace ba, in ba hukunci na ubangiji ba ai mace ka aurw abinka daga shekarun nan ku je ku yi rayuwarku har ku tsofe abinku tare, kai ka fi gane mai shekaru ai sai ka yi, wai abin takaici ka tashi daga Manal zaka koma MINAL yayarta, wani lokacin sai in rasa ina ka fi ba karfi a tunani"
Shiru kowa ya yi yana kallon dan uwansa, kallo mai kama da harrare harrare kallo dai gayanan
Kana ganni ka san sun gama shakawa junna ne
Da haushi haushi ya mike yana daukan jug din ya fice ko ka ci kanka bai kuma ce masa ba, shi kuwa ya saka dariya yana dan yin dogon wuta ya ce" Allah ya sa idan ka sha ka kasa barci"
Sarai ya ji shi ya masa banza ya tafi da jus din kuma niyarsa shi zai shanye duma wanda bata ma ba ya hadiye zuciya mana!, Maganar yarinya dai ya yanke hukunci ba zai zauna da kowa kan maganar nan ba
____________________________________
Ana fitowa daga sallar la'asar aka zauna aka shiga gabatar da rabon gado bayan an gabatar da dukiyoyin baki daya a hannun baban alkalin marigayi da manyan malamai masana adinni, sannan aka gabatar da takardun haihuwar du wani d'a malakin Marigayin dake raye ana gwadawa ana kiran sunna kana amsawa har zuwa kan matansa hudu reras dake zaune kowace aka tabatar da matarsa ce har ya rasu magana ta saki bata taba shiga tsakani ba
Cikin ilimi da koyarwa ta addinin musulunci aka gabatar da rabon gadon, kowa ya samu kasonsa dan a gadon gida biyu ne sai kadarorin da filaye da dai sauransu kowane kuma da awonsa da komai, harta kudi dake ajiye a banka komai sai da aka gabatar aka raba banda motoci na cikin gida da ake jigila wa ahalin gidan wa'inda manyan sun san na MARSHAL ne basu shiga irge ko rabo ba, hasalima sun yi mamakin dukiyar dan wasu abubuwan basu taba sannin akoysu ba sai dai kamar yadda du aka yi zato taron ahalin ya zamto abinda aka sasamun Allah san barka ne baka isa fita burgar shekara biyu da shi ba zai watse idanma ka yi wasa a shekara daya sai ka karar da shi bale a biyu
A nan fa ciki ua duri ruwa
Du wani mai dogon buri jikinsa ya fara yin sanyi
Su da kansu sun san da ace basu da yawa da sun tashi da makudan kudi duda mahaifinsu ba wai asalin shi din ne mai kashin arzikin ba, aa, d'ansa ne Allah ya ba abin a jinni kuma cikin ikon Allah ya sakarwa mahaifinsa ba ji ba gani ba tunanin ba shi kadai ya haifa ba shi dai burinsa su rayu cikin wadata da nutsuwar zuciya, a haka ya malaki abubuwan da har ake kwatance da shi, sukan manta arziki na magada ne ba na daidaiku ba, a gadon kuma da aka raba harda MARSHAL an ba dan shima d'a ne yana da rabo a gadon, bama kamar matansa ko nace maman su Furera da ruwa ya cinyeta a zaunen da take du wani dogon lisafi nata ya nemi kuncewa domin a
anta wa'inda take iya rike nasu gadon basu fi uku ba , gasu mata, mazan du sun malaki hankalin kansu kowa nasa za'a bashi ya je ya yi abinda zai fishe shi, uwa uba ba'a je ko'ina ba ta ji maganar bude account da zubawa wa'inda suke da kannanun shekaru a rufe masu har sai bukatar tabawa ta tashi ko sun kai wajen da zasu amshi abinsu sannan a basu su yi yadda suke so sai ta ji kamar du taron bakin cikinta ake yi, ita da take hangota ta zama hamsakiyar hajia ta fita da kudinta ta shiga bin kasa kasa tana kasuwanci ana sarar kaya a wajenta ta samu wani gagarumin alhaji ta yi wuff da shi ta zamto abar kwatance a cikin garin baki daya sai gata da kudaden da idan ta yi wasa tana iya lalubawa ta ji babu?

Ta afka a duniyar tunanin nan har aka shafaa fatiha yaren suka ringa watsewa kowa na nufar makwoncinsa, du wanima mai niyar tafiya yanzun ya shiga tunanin abinda zai gyara shi, gida dai yayansu yace na kowa ne, kowa yana da yancin zama a cikinsa hankali kwonce gida na familly ne, gaskiya wanda zai yi garajen barinsa a yanzu ya gama ginuwa ne, ginanun kuwa du da aurensu , mata kuwa masu aure na kusa kusa sun juya tun a yau, na nes ane sai tashin gobe in sha Allah
Aunty amarya ce ta yi tafiyar karshe bayan ta je ta kawo hotunnan dake jikin katinta da passport dinta ta koma bangarenta ta yi kwonciyarta
Dukiyarta da ta bari MAMAH ta zubawa ido, to ita yanzu yaya zata yi da dukiyar nan?

Nanaah ko ta dauka a nan ta barsu ta yi tafiyarta
Bayan ya raka bakin ya dawo yana jin tamkar an sauke masa wani nauyi a kansa mai girman gaske ya koma falon na Baba inda Mama ta dawo yanzu ya zauna yana duban kudin ya ce" Wannan fa?"
Mamah zata bashi amsa ZAHRA ta shigo da salama a bakinta
Mamah ce kawai ta amsa salamar , shi kuwa sai ya samu kansa da tunanin aa ina yarinyar nan ta shiga ana rabe Raben nan?

Murmushi ta sakarwa MAMAH dake mata sannu da dawowa
Mamah ta ce" Oh sai lumshe ido kike yi zafin kitson ne?

Mu gani?"
Da kyar ta cire hijabin tana nunawa MAMAH kitson bayan ta duka ta gaishe da yayansu
Mamah ta ce" Masha Allah, ama yauma bai wani kamu ba, kitso sama sama kuma basa iya sakawa jelar wani abu dan kar ya warware?

Wa ya dawo da ke?"
Zahra ta mayar da hijabinta tana jin zafin kitson ta ce" Abakar ne Mama, mun biya gidan auntyn bata nan ama na barawa danta sakon idan ta zo na san zai bata"
Mamah ta yi murmushi ta ce" To maza a je a yi wanka a cenza kayan nan a fito a yi girkin dare , na dira maki shinkafar sai ki yi kiyarki yau ai kece da girki ko?"
Zahra ta gyada kai ta juya ta nufi sama tana murmushin jin dadin MAMAH ta dora mata shinkafa aikin nata kennan ya ragu sosai, danma tana so sai ta yi dan hade hade dai na makulashe
Dawo da hankalinta ta yi kansa, ashe shima ita din yake kallo, fuskarsa da alamun kamar yana da tambaya ama kuma ya kasa fada
MAMAH ta yi kalar serius ta ce" Dama tunda aka ce za'a yi rabon gadon nan na fadawa mai kitsonta zata zo ta mata kitso dan bana so tana cikin gidan mun taru mu dukanmu bata cikinmu ko a taru da ita a ringa abu babu ita a ciki, Baba yaya maganar zamanka da Hasan?"
'ikon Allah' ya ayana a zuciyarsa, a bayane kuwa ya ce" Mamah, ni me zai saka a tashi a yi zama da mutumen da ba'a da tabacin zai auretan?

Inace har yanzu bamu ga manyansa ba?"
Mama ta ce" Wani irin bamu ga manyansa ba, to ba sai an zauna da shi an tsayar da magana ba kafin ya sako manyan nasa a ciki?, Ni na fi so a sanar masa ne dan a ji me yake tunani a kai, in zai iya mu bashi in ba zai iya ba tun wuro ya janye ba sai ya saka yarinya ta kamu da sonsa ba ya juya mata baya!"
"So kuma?" Ya fada kamar wanda kalmar ta bashi mamaki
Mammah ta zuba masa ido, har sai da ya ankara sannan ya sake fadin" Zan bincika in sha Allah "
Mamah ta yi gagawar fadin" Ka bincika me Baba?, Ka ga fa lokacin auren
an gidan nan ya matso, kuma so nake yi a wanketa a masu aurensu tare, me zaka bincika?

Ko dai yaron na yanada wani hali ne da ban sani ba?"
A hankali ya girgiza kai, ya ce" Mamah, bashi da wani hali, a yanzu kam ban sani ba dan ban yi binciken haka ba, gani ne na yi kamar ana gagawa da maganarta"
"Wace gagawa jama'a?

Kai dai kake nawa a kan komai baba, ka ga baka mana maganar shirye shiryen yaren nan ba, mazanma baka san yaya sun tanadi muhalin saka iyalinsu ne ko yayane?

Kawai kai bakama zauna ba wai me kake yi ne haka?
Chapter 64 · 0% Book details