← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 110

Sashe 55

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka kawai ya ji ba zai iya ci gaba fa rike ainahin abinda yake tunani da yarinyar ba, gwara ya fadi gaskiya sai idan kallon mahaukaci za'a yi masa a yi masa
Idannuwa kawai MARSHAL ya lumshe ya jinginar da kansa a jikin kujerar nan kirjinsa na bugawa
Murya a raunane Aban Ahmad ya ce" Na yi nadamar lalata rayuwar y'ar mutane, na yi nadamar fada marainiyar Allah, sanadiyar fitowar cikinta mahaifiyarta ta fadi ta mutu, ban duba wannan ba na sake nuna ba nawa bane dan kawai kar a kore ni daga kauye, ni na fi kowani azalumi iya zalunci dan ina kallo aka koreta aka tsangwameta ta bar kauyan, daga shi ban kuma jin labarinta ba, ban kuma haduwa da ko me kama da ita ba, kauyukan makota du na duba babu ita, yanzu kuma sai kawai na ga yarinyar nan, tunda na ganta na nemi nutsuwar zuciyata na rasa, tunaninta na raina ba dare ba rana, ni kuwa idan wani abu ne bayan wanda nake tunani ai na yi wauta da yawa, ina mai tabatar maka abinda nake ji ba halaka da wanda ka yi tunani Marshal......"
"Y'ar Aunty amarya ce ita, wace ta shigo ranar da muke zaune, ina ce ka ganta?" MARSHAL ya fada a hankali yana dan bude idannuwansa
Hannayensa ya saka yana murza gaban goshinsa, a hankali ya ce" Eh to, ban ga fuskarta ba, dan a ranar in ka kula ko gaishemu matar bata yi ba ta haye sama, da ace zan ganta yau din dai sai na tuna ko na gane ko zargina gaskiya ne?"
Iska mai dan zafi ya fitar daga bakinsa sannan ya kunna motar ya nufi anguwarsu da shi a hankali ya ce" Ba yau ba, ka bari na fara sannin me yake faruwa, ka bani dan lokaci please"
A dole ya yi gum da bakinsa, sai dai ba dan zai iya daukan wani lokaci da damuwar nan ba, ya dai yi shirun ne dan ya kula MARSHAL ya gama maganar kennan, ama shi idan ya ga ya ki bashi damar zuwan zai nemi izini a wajen Mamah, zai je ya ga wannan Aunty amaryar, fatansa Allah ya sa itace wace yake nema, ya duka ya nemi gafararta tun kafin ya koma ga ubangijinsa
A cikin dakin Mamah kuwa , tunda Mamah ta sanarwa Amir dalilin kiransa sai ya kafeta da ido harta bakinsa a sake yana kallonta da son gane wai da gaske take ko mene?

Har sai da ta kufula ta ce" Kai ka min magana mana ka wani zuba min ido baka sanni bane?"
Hannayensa ya saka ya talabe habarsa, a hankali ya ce" Mamah maganar ce na ga wata iri, abin ne babu hadi ko daya ai Mamah"
Da mamaki Mamah ta ce" A kan wani dalili fa ka ce haka?"
Amir ya sauke ajiyar zuciya, to shi yaya zai fito ya cewa Mamah zabin yayansa fa zabi ne irin na ginaniyar mace, wace ta san menene kula da namiji ta iya tatalin namiji ta iya bashi kula, wace zata iya daukan dawainiyarsa uwa uba shi din da kansa, ba wai lokacin koyawa mace komai yake da shi ba, gaskiya idn ya zamto mace sai ya koya mata wani abin hakan na iya zamowa damuwa a gareshi, maganar da Mamah take yi kuwa ko shi baban kannin Baban gida da wahala tashi daya ya dauki yar yarinyar, yarinya ce mana sosai ga sangarta da shakuwa da uwa
A tausashe ya ce" Ni dai, zan fi so ki yi masa addu'a a kan zabinsa Mamah"
Mama a dan hasale ta ce" Bari ka ji, da kai da shi din baki daya babu maganar zabinsa, dan zabinsa a matsayin hauka nake kallonsa, sam ba hadin biri da kada, in dai ni na haife shi ba dai da wannan yarinyar ba, dan ni ba makauniya bace sarai na san mw take nufi , koda zai aureta ka ji da kyau sai dai a zuwa ta biyu, ama ba dai wai ta zamto matarsa kwalin kwal ba!, Tashi ka bani waje kawai tunda ba za'a iya maganar kirki da kai ba Amir"
Ido ya dan zarro, sai kuma ya sada idannuwan dan hararar da maman ke watsa masa mai zafi
Dan murmushi ya yi yana sosa geyarsa da ky dinsa a hankali ya ce" Ki yi hakuri Mamanmu, kar ki bata rai kin ji?

In sha Allah Allah zai masa zabi na alkhairi "
Mama dai bata kuma cewa komai ba, ta riga ta hau sama , a dole ya mike jiki ba kwari ya yi mata salama ya tafi
MAMAH ta hade hannayenta tana dan kada kafarta, sai kuma ta ji idannuwanta na neman cika da kwallah ba dan komai ba sai dan tunanin amininta, yanzu da uban gidanta na kusa zata je ne ta baje kaffafuwa ta tafka rigima tace ba fa zai yiwu ba ya rabata da Y'ayansa, ya kuwa dauka ya yi maganin
an nasa tare da rarashinta da mata kirarinta tana tafe tana bubudewa, gashi tun yana fada mata ta fa koyi abinda ake nufi da jajircewa tana fada masa ba gashi ba an wayi gari baya nan din , yakan ce mata kar ta ringa aiki da shi, ana iya wayar gari sai ita sai yayanta, sai tace masa in sha Allah yana nan har su tsufa su tsofe
Kwalar da ta gangaro mata mai zafi ta sake saka hannunta ta dauke ta mike ta nufi bayi dan wanke fuskarta sannan ta tarda Aunty amarya, tana da magana da ita dan ta ji ta bakinta, duda ba wani abu tsakaninsu ama ta san a yanzu ita kadai ce zata iya nufa da maganar nan
Jiki ba karfi ta sauko ta nufi kicin tana fadin abinda zasu dafa sannan ta kalli Auta ta ce" Ke Auta maza ki je ki cewa Zahra a hada nawama kayan dan mu fara kai kayan namu cen tun yau da dare"
Auta ta amsa ta fito ta nufi dakin Zahran ita kuma Mamah ta fice ta nufi bangaren Aunty amarya
Da wuri Mamah ta fito daga bangaren Aunty amarya ranta na nunin alamun bacin rai ta nufi bangarenta
Har ta kusa shiga Laraba da Furera suka dan tsayar da ita suna gaisheta, Larabar ta zubawa ido kadan sai kuma ta dauke ta shige bayan ta amsa su da kula
Laraba ta nemi waje kusa da fulawowin gidan ta zauna tana dafe kanta dake sara mata, tunda Furera ta fada mata abin da aka tatauna a zaman nan ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta san magana ce mai kama da ta wanda ya fada a cikin halin ciwo da wahala su dauki abin da mahimmanci, amma kuma tana tsoron su daukan dan in har suka dauki maganar nan da mahimmanci to ita kam ta barin gari ta sameta, ina zata tsoma ranta ne?

Yaya za ta yi ne?

Furera ta sake kallonta ta ce" Aunty Laraba ina gannin abin nan bai ma dame ki ba, soyayar nan da kike fadi bata maki rikon da nake tunanin ta maki ba, in ba wannan ba ga ki ga wacce zaki sanarwa ta share maki kukanki amma sai ki wani kasa?

Wallahi na fada maki ki fa yi da gaske dan ni yanzu na fara tsanar matar cen , dan in fada maki ranar da aka yi maganar dan kawai babarmu ta nuna shegiyar
za'a aura masa?

Baki ga kallon da babarta ke yi ba, kar aje matar cen tana son y'arta munafurci take yi dan duniya ta so ta tana nuna bata damu da ita ba, kar aje yanzu da ta ji maganar nan ta fito da niyarta kina gani dai karfi da yaji yadda ta shiga tsakanin Babanmu da iyayenmu sai ita kawai ko menen e marigayi baya duba kowa sai ita bayan babu abin da ta fi namu iyayen!"
Wata ajiyar zuciyar ta sake saukewa ta ce" ba wai tsoron sanar mata bane na ke yi, gaba daya kwarjini ne matar ke min, ba fa yau ba na so kwatanta mata, ita ma irin girmamatan da nake yi ai ya ci ace ta fahimceni wani abin, amma sai ta yi kamar bata san komai ba, Ni yanzu idan na sanar mata abin nan ta sanar masa ya hallakani fa?

Kin san tsoron da nake masa bai san da haka ba ina tsoron ya sani ya ga ko na raina shi ko makamancin hakan kin fa san babu abin da ba zai iya faruwa ba"
Furera ta gyada kai tana sake rike kofar ta ce" Duk wahalar da zai ba ki ba za ta kai wace zuciyarki za ta baki idan ki ka hana mata abin da take so ba, ko ni nawa soyayar daban ne?

Ko sabani muka samu da yaya fa bana iya barci, hankalina a kansa sai mun shirya, gaskiya ki kwatarwa kanki idan kuma ki ka yi sake shi ke nan"
Laraba ta sake jan numfashi ta daurarwa kanta aniyar gobe za ta dawo in sha Allah, dan yanzu yamma sai yi take sake yi bata so wani ya zo ya sameta da Maman suna magana shi ko Amir dukkansu tsoronsu take ji, zuciya cema da kai bawa inda Allah bai kai shi ba ta saka shi a uku.

Tashi ta yi ta yi tafiyarta gidansu tana ta sake saken abin da ta fi tunanin zai fisheta.

Da dare bayan kowa ya haye sama ya kwanta Mamah kuwa tan zaune a falo tana jiran MARSHAL da ya sanar mata cewar zai zo bangarenta kafin ya shige bangaren samarin gidan da yake kwana.

Tunda ya shigo bangaren nata ya zauna ya gaishe da ita a tausashe ya sanar mata maganar ACn da suka yi da Amir da decision din da ya dauka a kan lamarin, sannan ya dora da yi mata bayanin karatun hudu daga cikin kannen nasa maza da yake son fitarwa makarantar da ya yi karatu , zai fara nema masu hanyyar sannan ya tura su, sai kuma ya yi dan shiru yana kallon Maman da fahimtar kamar a cikin damuwa take.
Chapter 55 · 0% Book details