← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 110

Sashe 49

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da dan sauki, sai dai gashi ita bata sanshi ba, bata taba ganninsa ba, tana amsar sakamakon aikin da ya aikata a duniya
A dan sanyaye ta ce" Zan tambayi izinin haka a wajen Mamah"
Murmushi ya yi yana jin farin ciki a zuciyarsa, yar gidan Docter ce fa, wannan labarin sai ya fi komai dadawa a zuciyar Hajia Baba, watau yayar mahaifinsa, tabbas wannan labari sai ya sakata farin ciki marar misaltuwa, idan ya samu auren yarinyar nan shima ya san ya huta, bashi da damuwa da tarbiyar ya'yansa tunda ya dauko mai tarbiya, yarinyar ga kyau ga tsari ga jan aji....gaba daya ita din ce ta dace da shi rayuwar zaman duniya......

Da wannan suka yi salama ita kuma ta mike ta saka hijjab din Mamah blue mai hannaye lafcece har kasa tana tafe tana dan dage shi ta sauko kasa a lokacin da ake fitar da kayan su Minal niki niki kaya kamar wa'inda suka zo siyyaya ba gidan rasuwa ba ana sakawa a motar da Amir ya zo da ita dan a kaisu inda zasu kwana kafin su wuce
Minal din sai Fara'a take na rikitaciyyar kyautar da aka yi mata na gudunmuwar auren
anta, tabbas ta yi farin ciki da kyautar nan har kamar ta yi kuka, ai na gado ya samu kam sai dai MARSHAL ya yi hakuri ya yi gadaje ya gama, wannan kudi ai sun fi karfin wai a kara a yi gara, garar me ?

Ita babu wata gara da take gabanta shi uban nasu ya yi garar ai an rage masa ita zata gwongwaje
anta ne su je gidan kishiyoyi a ci uban sabada ana daga kai da rantsatsun kaya, ta san
anta sai sun kece raini sai sun yi ba zata dan kuwa kayan da zata yi masu sai ta bada tsoro
Haka fai suka wuce, ita kuma ta zagaya zatta wuce kitchen suka hade da Adawiyya dake dauke da wasu rantsatsun kayan shayi a wani irin plate ruwan zeiba sai kyali yake shayin kuwa sai kamshin na'a na'a yake yi irin shayin larabawa ne ya hadu iya haduwa ta damka mata tana fadin " Zahra Mama tace wa ki je cen gadin ki kai shayin nan na aminin Babnguda ne sunna cen tare , je ki zo an kanwata in gwada maki wani cake da muka yi dazu ki gani nama rage maki rabonki"
Ido ta zaro tana tura mata tana tura mata , da karfi ta tare dan Adawiyya saki ta yi ta yi ciki da gudu ira kuma ta yi tsuru tsuru tamkar zata saki fitsari tana kallon hanyar da ta bi
Fuskarta ta takwakkwabe sosai ta juyo da plate din ta nufi inda aka aiketan a ranta tana ayanna ' sai na rama walahi sai na rama aka aike ki shine kika makala min salon ni na yi laifin ya karyani ko?

Kina gannin yadda nake kauce masa tunda ya shakeni ya daka ni zazabi da amai aman shine kika turani?

Zan rama ne sha kuruminki zan rama ne'...............

Tana zancen zucin har ta zo ta wuce ta cikin gardin din ta wuce Aban Ahmad tsaye yana amsa waya bata kula da shi ba ta je ta ajiye ta yi gagawar barin wajen domin shima yayan nasu ya tafi wajen get dan tarbo Minister da suka zo sake yi masa ta'aziya
Da dan sauri take tafe tana tatare hijabin nata kanta a kasa, hakan ya sa ta daku da gefen hannun Aban Ahmad bata kula ba
Da sauri ta dan dago ta masa kallo a dan fizge ta ce" Yi hakuri dan Allah ban kula ba"
Sannan ta wuce da gudun tsiya dan karma a samu wata matsala
Tunda ta yi magana, ta dan kallo fuskarsa ya daskare a tsaye a inda yake har ta bar wajen ya kasa koda motsa yar yatsarsa ne har sai da Huzaifa ya zo wucewa ya gaishe shi da muryarsa mai irin amon ta MARSHAL ya dawo hayacinsa a dan firgice ya sake tsurawa hanyar ido sai kuma ya juya da sauri ya koma wajen da suke zama ya mimikawa bakin hannu suka gagaisa sannan ya samu waje ya zauna ya yi shiru sam baya cikin duniyar hirar da suke dan tabawa a tsakaninsu dan ya lula duniyar damuwar da take tasa, wace ke cen kasan zuciyarsa, nasa shima mikin mai tsauri har sai da MARSHAL ya dan taba gefen kafadarsa yana masa magana ya juyo a dan firgice yana kallonsu a lokacin da minister ke fadin" Elhaji ni yanzun yayanka nawa?"
Da kyar ya iya hade dan yawun bakinsa,yana lalubar maganar da take masa nauyi MARSHAL ya ce" wai wa wannan?

Ya'yansa biyu ne , da na wajena mai sunnan Abahna da kuma kanin sa isma'ila"
Murmushi minister ya yi ya ce"
A tausashe ya ce" Hajia wani abu yake faruwa ne na ganku a tsaitsaye haka?"
Maman Abul ta ja numfashi, sannan ta fara magana ta ce" Na zata ka saurari voice note din da muka yi jiya a grup na familly Docter AHMAD?, Shi yasa ka ga yan uwanka du sun halarta dan tun jiya na yi magana kan kowa ya samu halartar a yau ko me yake yi kuwa ya bari ya zo"
Kai ya gyada yana dan shafa kansa ya ce" Ayya, na dan jima ban leka group din ba, amma Bismillah ina sauraro"
Lebenta ta dan dantse, sai kuma ta bude ta ce" Babangida ka yi hakuri, ni ban kawo maganar nan dan na ci zarafin kowa ba, sannan ni da na fadeta ba dan nice na fi kowa rashin hakuri ba, aa dan kawai dai nice na ga ba zan iya rikewar a cikina ba duba da jiya mamanmu tace tunda kwanaki sun ja tana so na je na gama takabata a gida, dan ka ga dai ni gaskiya ba zaman daki zan yi ba, ko yau miji ya fito min aure zan yi dan ibada ne"
Idannuwansa ya sada, a hankali ya ce" Haka ne"
Maman Abul ta dora da fadin" Kuma ka ga nauyi ne a saman kan Docter, ya dace ace tun satin rasuwar mamaci a sauke masa irin nauyin nan, sannan zai zamto taimako a gareni ne zan iya jan jari, dan komai arzikin gidanmu sunnana magidanciyar da na shekare a gidan miji da Y'ayana, dole sai ina dan tabuka wani abin dan na ji dadin zama da iyayena harma inda Allah zai kaini........, Har ga Allah na san suma sauran da haka a rayukansu sun dai fi gane su yi shiru ne bayan ba wani laifi aka aikata ba dan an sanar..........."
Idannuwansa ya dago ya zuba mata su, shi dai ba bagwari bane, a yarenta ya gane me take nufi, dan haka ya yi dan murmushi ya ce" Wannan gaskiya ne hajia, kuma na ji dadin da kika fada din, laifina ne da na yi nauyin baki, abinda yake faruwa na saka ne a idasa hade min kawunnan gonakin ABAH da yan daidaikun abubuwan kadararsa, a yanzu haka maganar da nake maki mun tsayar da rana da alkali da kuma Malam kan ranar da za'a yi zama a sauke nauyin nan a kan ABAH, kin san da yake kadarorin a dan warwatse suke wasun sai yanzu nema nake sannin da zamansu dan gaskiya cigiya na bada tunda dukiyar marayu ce, ku yi hakuri in sha Allah sati daya ne muka dauka mu gama hada komai sai a gabatar maku a kuma rabawa marayu......"
Gaba daya sai ta ji wani abu mai kama da nauyi da kuma kunya sun ririke mata kaffafuwa, balle da ta juyo ta kalli yaran ta ga kowa ita yake kallo, ta tabbata ba dan komai banee sai dan sun ji furucinta na aure ,
Hade fuska ta yi, dan a gaskiya ita ba zata tsaya su kashe mata buri ba, shekarunta ai ba gazawa zama da namiji suka yi ba
Murmushi Maman furera ta yi, tana girmama mutun mai wauta
gaskiya maman Abul ba dai wauta ba
Baki ta tabe ta ce" Kin dai fada hankalinki ya kwonta, sai ki koma ki yi hakuri har a baki, kina ta wani daga hankali kamar wace zata kwashi dukiya, Allah na tuba gado ko mai yawa ai bashi da wani albarka bale ki duba ki ga ya'yan dake zagaye da ke, a nan daya tak ce bata da gadon nan baki daya sauran nan kowa yana da iko da kuma gadon nan, in kin samu ashirinma da kyau......" Ta idasa tana yar dariyar rainin nan, hakan ya hasala Maman Abul ta ce" gwara ni ba munafuka bace ai, ke ai damuwarki gidan nan, bayan kin san ba gidan Docter bane ya fada a tsaye ya kuma fada a zaune cewar ba nasa bane, danma gudun rigima shi ya hanna wanda ya gina malaka masa gidan ai?"
"Au haka zaki ce?
Chapter 49 · 0% Book details