Sashe 75
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Rai bace ya nufi get din tamkar wani mayinwacin zaki ya shiga ya nufi inda sojawan da aka zuba dan wunin yau din suka fi yawa kasa kasa ya ce" Ku salami kowa, ba da hayaniya ko wulakanci ba, ku yi masu alkhairi ku salame su"
Daga haka ya ringa ratsa mutanen har ya nufi bangaren MAMAH, ransa na sake bacewa irin yadda wajen ya dauki mutane nan da nan kowa hankalinsa ya yi nan, kowa ya zo abin haushin kallo ne suke yi ba rabawa ba, mata sai zubewa ake yi wai iskokansu sun tashi, abokanan zaman MAMAH da nasu dangin suma sun taho sunna dibar albarka ama danginsu sun kasa tsawatar masu
Ba tare da ya tsaya wata wata ba ya ratsa ya karasa daf da kofar inda LARABA ta cuje daurin dan kwalin matar oga da ta kafa tana ta ihu tamkar sabon kamu tana durawa ZAHRA ashar tana fadin asiri ta yi ta auri SIR kuma sai ta karya dan ubanta dan kuwa shi din ba mijin shegiya bane, abu dai na wanda yake daf da samun tabin hankali dan abu ya shige shi bai shirya ba, abu dai gayanan, kallonta ake yi ana kuma kama masu zubewa ana jerasu a falon Mamah, du an bi ana neman dagawa mutane hankali da son zuciya kala kala,
Yana karasowa ya damki hannunta,
Tana kallon wajen kofar MAMAH ne ita a dole a bata Zahra ta koya mata hankali, hakan ya sa ya juyota da karfi har ta nemi gwarun masa a kirji ya rike hannunta da wani irin karfin da ya sakata zarro idannuwa jikinta ya dauki rawa tana wara idannuwanta da suka sha karin gashin ido hankali tashe tana dadage dan jan hannun nata ta budi baki da karfi ta yi maganar da ta ankarar da kowa ya zo wajen a lokacin da ta ce" Innalilahi MARSHAL!"........a lokacin ne shi kuwa idannuwansa da suka yi ja ya iya bude mata su a kausashe da kuma dan karfi ya ce" Wacece ke?, Kika iya shigowa kofar mahaifiyata kina daga murya?
I said who are you?....."
Ya idasa da karfi lokaci daya kuma ya kauda mata wani busashen marin da ya sakata sakarkarcewa sannan ta yi bazagar daga tsayen nan watau ta lauje kaffafuwanta suka gaza daukarta ta so fado masa a jiki, shi kuma ya ki yarda da hakan hasalima da hannun nata ya tureta ta fadi kasa hancinta na neman zubar da habo dan har ya fara, duniyarta ta dauke tamkar an dauke azaba a jikin mutun, komai nata na hadewa kama daga tunani har kwakwaluwa sannan ta iya kai hannayenta tana yamutsa karin gashin da ta yi sakamakon jin ya mata nauyi kamar an dora mata duniya a saman kai, sai kuma ta nemi bude idannuwanta da suka yi mata nauyi kamar an watsa mata barkono kuwa haka suke zogi, lokacin ta ji kunnayenta na jiyo mata maganarsa sama sama bayan ya bude falon Mamah ya yi tsaye daga dokin kofar da kuma ciki ciki ya ce " DU wace ke son kanta, ko y'arta ta hanzarya tatarawa ta bani waje, in ba haka ba takalmina zan cire na fitar da ita, ku kuwa......."
Ya nuna su Maman Furera a kausashe ya ce" ku shiga ciki!"
Daga haka ya yi shiru zuciyarsa na tafarfasa ya shiga bale takalman nasa
Ai fa, wwaye wai zai jira mamansa ta dauke shi, du a cikin masu sumar nan daya tak ce bata motsa ba, wace ita kuwa an santa da du ba maganar karya, yar gidan Maman Abul, dan kuwa zaman auren kansa a rabi da rabi yake damuwa saboda lalurarsu, hayaniya ke tayar mata da su, hayaniyar nan kuwa ta isa ta tayar da su din, ta yi sheme sheme baiwar Allah bata cikin hayacinta, a haka kuwa sai ta yi sati guda cirrr bata san inda kanta yake ba
Rututu mutane suke kama gabansu
LARABA, da kyar kawarta ta iya jijibarta ta mikar da ita, irin yadda tale zarar ido kai kace ta haukace ne, a haka dai ta samu ta fitar da ita sojawan nan suka kama mata ta fitar da ita daga gidan.....
, Dangin amaren kuwa kowace ta koma bangaren yar uwarta ta labe ana kama baki, kai wannan mari ya firgita su, kau din har saka wasu zabura yake yi, yarinyar kuwa ta yiwu ta kurumce dan kuwa irin kallon da take yiwa mutane zaka fahimci bata jin komai bata gane komai
Dakin ya mayar ya rufe ya karasa ya masu tsaye , a kausashe ya ce' Lafia?
Menene?"
A gaskiya basu zaci bama tambayar da zai yi kennan ba, sun zaci zai zazagesu ne, to irin wannan fushi haka bale yanzu babu idon wanda ya ajiye su ai ko zane su akace ya yi sai dai ace Allah shi kyauta, zamanin ai babu abinda ba zala gani ba in dai da ranka, shi yasa a yanzu a tsaitsayen da suke kowace ta kasa furta komai, sai Mamah dake sharar hawaye, bata taba tunanin rashin mutuncinsu ya kai haka ba, menene wannan aiki kamar na wa'inda basu da ilimin adini bale na boko?
Me suke tunani? , Menene suke tunani?
Hannunta na kan ZAHRA dake jikinta a labe jikinta na rawa, ita ta rasa a wani hali ciki, ita dai LARABA ta shakota a cikin yan matan amarya ta wanka mata mari, shikenan hayaniya ta tashi sunna fadin magana kamar ta mahaukata, Furera ta tayata suka fara dukanta a dole Rukaya ta saka ihu tana neman kwatarta a nan ne su Auta suka shiga, da gaske fa aka shiga dukan junna hakan ya janyo hankalin mutanen waje, har Aunty yayar marigayiya ta ji me ake fada ta fita ta yi kiran wama ya sani shikenan ta fara kuka hannayenta saman kanta ta nufi bangaren Mamah shine ta fadi wai aljannunta sun tashi, daga nan abin ya sake rikicewa da aka ji wai ko an aura mata Babangida?,
Kukanta take sha kasa kasa tana sakin ajiyar zuciya na dukan da aka yi mata, bayanshi ta san sauran zancen shirme sunnansa, to in ba shirme ba meye wannan magana kamar ta mahaukata?
Hum lalle kiyaya kawai dai kiyaya ce, bayan haka bata san amsar karawa a maganarta ba
Gannin sun kasa yin magana ya saka budar bakinta ta ce" A gaskiya na gaji, na gaji Baba, wannan wace irin fitina ce?
Yau har ta kai inda za'a mana taro ana kallonmu muna raba aiki irin ma rashin ilimi dan babu DOCTER?, ni na rasa wannan fitina fa me ta yi kama, na rasa wannan balakin da me ya yi kama, ina dalili ina dan mafari ?
Ina anfanin wannan shirmen Fisabililahi?, Haba dan Allah, na gaji ba zan iya wannan rayuwa kamar ta jakai ba, babu ruwanka fa gashin wance ama ka iya irga kitsonta?, Haba jama'a meye wai kiyayar?
A da na yi zaton kiyayar dan gaba dayanmu muna tunanin ta rabamu da miji ne, da kunnayenku a gabanku a gabanta yace ita din nan baima san kalarta ba, ko karya na yi?
Dan tashin hankali kun sako y'arta a gaba kun hannata motsi ku a tunaninku ta haka zaku muzguna mata ko?
A yanzuma da wanda ya hada ya rasu ba zaku yi hankali ku gane cewar yardarku da rashinta uwa daya uba daya ne a nan ama sai kunna abu kamar wasu da basu da ilimi?, Gaskiya ba zai yiwu ba!"
"Ama maman Auta me yasa zaki ringa magana kamar baki gane me muke nufi ba?
Matar da zata kasance tasa burinmi ta zamto yar baban gida yar mutunci yar daraja, wace zamu yi tutiya da tinkaho da kasancewarta a cikinmu dan hakan na nufin uwa ga y'ayanmu, kuma mu din nan da kanmu abokiyar shawarmu wace ta isa ta tankwasa mana shi koda wani abu ya tashi ya kiya?
Wace muke da yakinin ko mun mutu tana nan wa y'ayanmu?
Shikenan ba labari ba shawara ba komai sai dai mu ji a bakunnan cikin gida ana tsaka da fada wai an aura masa wannan yarinyar?
Menene soyayarki da yar kishiya?, Menene soyayarki wai da shegiya ne Mamah?" Maman Furera ta fada har hawaye na zubowa daga cikin idannuwanta, dan gaskiya abin nan sai tace tashin hankalinsa daidai yake da mutuwar Docter, kai karma ta zua ne a mata wani kallo sai tace ya fi gigitata a kan mutuwar Docter dan kuwa ai sun jima da yarda cewa Docter fa lokaci ya yi dan kuwa da kansa tun basa yarda da cewa ciwonsa ya yi tsanani har sai da ya saka masu yarda da hakan a zukatansu suka dangana da komai suka barawa Allah komai, shikenan sai yanzu kuma a fito masu da haka?
Summa ba zasu yarda ba
Bai sasauta dubansa a kanta ba ya ce" Dama, akoy mai hurumin zaba min mace a cikinku ne?"
Maganar ta zo masu wata iri, har ga Allah maganar sai ta masu tsauri, nan da nan suka fara tunanin ama ai shi din dansu ne ko?
Sunna da wannan damar, wasi wasi ya fara shigarsu, kowace ta fara tsareshi da ido dan kaushinsa na yau wani iri ne mai fitinanen karfin tsiya
Idannuwansa ya mayar gefen da yayar marigayiya ta zuba masa ido ya yi mata wani kallo da ya saka cikinta durar ruwa, hankalinta ya nemi tashi fiye da da, dan kallon kamar na wanda yake mata gargadi ne ko menene?