← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 110

Sashe 18

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan girman Allah ki sanar min waye mahaifina..................?"
Juyowa ta yi a harzuke har tana taka kwalbar dake zube a hanyarta ta karaso da sauri da abin goge table din cin abinci ta daga shi ta shiga maka mata shi da dayan hannunta kuwa ta shiga hangazata tana turata tana sake turata ita kuma tana tirjewa tana hade hannayenta biyu tana dukawa hadi da fashewa da kuka tana neman riko hijabin mahaifiyar tata har ta karaso da ita wajen kofar shigowar ta saka dukkan karfinta ta hangazata da Hannayenta biyu hakan ya sa ta fito waje kafarta ta gurde wajen matatakala ta yi baya gaba dayanta hijabinta ya kwasheta ya makata da matatakalar nan ta ringa mulmulowa har ta fado kasa sannan ta lumshe idannuwanta tana fatan Allah ya amshi ranta a irin wannan lokacin tana kuma jiyo magangannun ma'aikatan da suka nufota a guje sunna kiran sunnanta cike da tausayawa da taimakawa suka suka kamata suka cicibeta suka nufi bangaren Hajia da ita wasunsu masu rauni na kuka, wasu na alhinin wannan lamari suka shiga suka tarar a lokacin Hajiar na kwasarta na matar Docter wace ta zo takanas tana fada mata cewar tana so a yi zama a cenza tsarin kwana bibiyu a mayar daidaya dan bata so, ba zai yiwu ace sai ta kwana shida kulun ta ga mijinta ha, gashi yanzu Docter ya kai wajen da yake gajiyawa da hidimar iyali dan tsufa ya zo shekaru sun ja sai a hankali ita rabonta da mijinta wata hudu kennan yanzu, shine hajia ke salalami ta rasa ina zata saka ranta dan kunya da tashin hankali har take ce mata ke yanzu me kike nema dama a waje Docter ?

Ku ba jaraba ba ku tashi ku aure tsofafi da karfinku da komai su auna maku cikunna su barku da wahalar ya'ya a lokacin da kuka zo ganiyar son sasabawa da su ba?

Ki je ku yi maganarku da sauran yadda kuka tsara daidai ne a wajen Zawaira dan yanzu kam ana ta kai wa yake ta kafa............

A irin wannan lokacin ne aka shigo mata da Fatima ZAHRA ranga ranga tamkar a summe
Hannu Hajia ta dora a kanta tana rungumo Fatima jikinta hankali tashe ta dubi wannan ta dubi wancen ta ce" Mota ce ta kadeta?

Kai menene ya sameta?

Daga makarantar aka dawo da ita ne?

Yanzu fa ta tafi makaranta innalilahi ke Zahra, Zahrah "
Hankali tashe aka sanar mata abinda ya faru cewar daga bangaren Aunty amarya ne aka hankadota ta fado daga saman matakala
Kishiyar Mama sai leke take yi tana tabe baki tana son gannin kwaf
Mama kuwa hankalinta ne ya sake tashi, a rikice take ainun ta ce" Dan Allah ku fita, ku fita ku duka ku bani waje, ke salamatu idan kin fita ki saka a fito da mota a kaimu asibiti, Hajia kema ki je na gama magana kawai du yadda kuka yi daidai ne!"
Tana fada tana sake tarro Fatima a jikinta har aka sanar mata an kawi motar, a dole ta yarda aka kama mata suka dauketa suka saka a mota ta aika Ummi sanarwa Aba a wajen masalaci dan ya fita tuni
An amsheta an kuma bata kulawar da ta dace ta farfado aka yi mata allurar barci bayan an gyara mata gocewar da ta yi a kafarta ta yi wani irin sharrr da ita tana barci dogon karan hancinta ya yi zuwat da shi , dan siririn bakinta kuwa ya yi tsuwat da shi ya karra ja , sai ajiyar zuciya da take saukewa lokaci zuwa lokaci a cikin barcinta
Mama na zaune ta zuba mata ido, wani irin tukuki zuciyarta ke yi na balakin dake tafarfasarta
Ta yi kiran numbar Amir da Baban gida su kadai take jira a wajen nan, Amir ya zauna mata da Yarinyar nan babban gida kuwa ya bi bayanta su tarda ubansa da matansa ta ja masu kunne kwonsu da kwarkwatarsu, bata son rashin mutunci, idan aka shiga aikin nan da ita babu wanda zai ji dadinta, tana kiyaye shiga harkar yara dan gudun raini, to fa yara su kiyayeta walahi!

A kalla ta dauki minti talatin bayan an yi sallar magariba an kuma yi ta isha'i sannan sukka karaso
Docter Hajara ce ke yi masu jagora har dakin da marar lafiyar take suka shigo bayan sun nemi izini suka sauke dubansu a kan Mamah da ta mike tana gyara hijabinta daga saman salayar da Direba ya miko mata fuskar nan a hade sosai.

Amir ne ya yi karfin Halin budar bakinsa a hankali ya ce" Subahanalah mama harda karaya ba?, Me ya sameta ne?"
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_12_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
Da kyar Hajia ta iya budar bakinta ta dube shi ta ce" Amir ka zauna min kadan bara na je na dawo, Baban gida mu je gida mu dawo a nan zamu kwana dan bugawar zuciyarta ne likita tace a hatsari"
Sai a lokacin ya kai dubansa inda take kwonce
Kallo daya tak ya mata ya dauke dubansa ya juya ya fara yin gaba har hajia ta sake barawa Amir salahun idan ta farka ya tsoratar da ita ita da shi ne, shi kuma ya yi murmushi kawai ya zauna cen nesa yana chating da wayarsa da amaryarsa jifa jifa yana kallon yar cikin zuciyar Hajia sannan ya maida dubansa kan wayarsa
A cikin motarsa kanshinsa ne ya cike ko'ina, tuki direba ke yi, su kuwa sun yi shiru a bayan motar a zaune
Du a tunaninsa wani abin hajia zata dauko in sun je gidan, shi yasa ya dan yi tsai yana tunanin yadda zai shawo kanta ta yi kwonciyarta a gida idan ya so nurse sa kula da y'ar tata har suka karaso gidan yana nazarin haka...........

Hajia na fitowa ta dube shi ta ce" Ka wuce mu je bangaren ubanka!"
Da sauri ya juyo ya dan zuba mata ido, sai a lokacin ya ga banda halin damuwa na rashin lafiyar y'arta akoy rikici a tatare da Hajiar
A ransa ya ayanna' Ya rab, Docter me kuma ka yiwa Hajia yau ne ?'
A fili kuwa da hannunsa ya yiwa sojawa biyun dake gefe alamar sunna iya tafia sannan ya shiga bin bayan hajiar da har ta kusa shiga bangaren Abah
Salama ta yi kasa kasa tana son yin kiran numbobin matansa da wayar Fatimah dake hannunta , sai ta ja turus tana kallonsu su ukun a zaune kowace na nuna isa irin na mace a gaban mijinta sunna zantawa ama babu Doctern a wajen ta yiwu bai shigo ba ko yana ciki
Bakinta ta bude ta sake yin salama a bayane tana karasawa ta ce" Au ashe kunna nan, masha Allah ya fadi kan kari ba sai na kirayeku ba"
Amsawa suke yi, sannan sunna gaisheta da mutuntawa harda wace bata cika yi mata irin gaisuwar nan mai daraja ba, domin wanda ke bayanta a tsaye ya gaje gaba daya kofar shigowar da shiga irin ta swuit ruwan toka a jikinsa ama farar rigar ta ciki ce kadai babu ta saman a jikinsa, dukkan wata kira da tsarin karfi na jikinsa ana iya ganewa, da dan sanyayan murmushi a saman lebensa mai alamu da jira yake su gama gaisawa da mahaifiyarsa sannan shi ya gaishe su, daya daga cikin halayansa da mahaifinsa ke alfahari da su kennan, girmama matan da ya kawo matsayin kishiyoyin mahaifiyarsa ciki harda wace ya girma ko zasu yi sa'ani da junna
Karar bude kofarsa ya saka du suka waiga hanyar da zai fito
Da dan sauri Mar
chal ya karasa inda mahaifinsa yake sannan ya tausasa tafiyarsa ya kuma dan rage tsayinsa ya kama hannunsa daya da bashi da sanda ya rike ta hanyar rike dukkan karfinsa a jikinsa yana sake kallon kaffafuwan mahaifin nasa da suke hayewa kamar baya shan maganinsa suka nufo falon ya kaishi wajen zamansa ya zaunar da shi sannan ya duka yana cire masa slifas dinsa da ya ga sun shiga kumburin kaffafuwan ya mike da su a hannunsa ya nufi dakinsa ya mayar ya dauko safa ya dawo ya duka ya sake kamo kaffafuwan ya dora saman cinyarsa da ya yi zaman rakumi ya saka masa safar sannan ya mike ya ciro wayarsa ya yi gaba da su kadan ya dannawa docter kira, hakan ya saka Aba dan cuno baki yana kallonsu ya ce" Yanzu zai hadani da likita a zo a yi ta jagulata shi dai bai yarda ubansa ya kai wajen da ciwuka sai dai a yi hakuri da su har rai ya yi halinsa ba, karfi da yaji shi sai Ahmadu ya yi lafiya bayan tsufa labari in ji hausawa"
Kusan kowace sai da ta ji ba dadi a ranta, a bayane kuwa suka ringa yi masa addu'a shi kuwa yana amsawa fuskarsa dauke da murmushi mai sanyaya zuciyar dukkan mai kallonsa
A nutse ya ce" Yau dai ga Hajiata da kannenta, Allah ya sa ba laifi na yi aka hadu a zane ni ba?"
Kai Aunty amarya ta sada, ita lamarin nan kunyar da yake bata Allah kadai ya sani, wannan wani irin kayan kunya ne matan Docter suka zo da shi?
Chapter 18 · 0% Book details