← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 110

Sashe 21

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daga Aunty karama har zuwa aunty j ku zauna da ita da zuciya daya, kar ku daura fitina a kanta ku rayu hankali yadda kuke so, itama ku barta rayu hankali kwonce kamr sauran ya'ya a gidan nan, yadda zan kare hakin Rukaya haka zan kare nata, idan ta samu miji a aurar da ita ta yi tafiyarta dakinta, bana son a kan maganar nan a sake saka ABAHNA a gaba ko mu sake irin zaman nan da ku, ko ba komau ai iyayena ne ku ba zamu yi haka ba, sai dai ku fahinta bana son na sake tsayuwa a kan lamarin nan da ku daga babarku har karama...................... *ITAMA Y'A CE, KUMA MAI YANCI CE* baku san wa zai talafeku gobe ba, baku san wacece ita Allah ya baku ba.......so ku mutunta ko ku zuba mata ido shi nake umarta!"
Daga haka ya juya wajen Abansa da ya zuba masa ido yana sauke ajiyar zuciya yana kallonsa nutsuwa na ratsa shi da kwonciyar hankali, ya riga ya sani ne ko yau ya fadi ya mutu yana da tsayaye a cikin ahalinsa
A sanyaye ya furta" A huta lafiya, in sha Allah satin gaba zamu fita harkar
afafuwan nan, a fara shiryawa"
Nanma bai tsaya ya ji jayayar Abah a kan maganar ba ya fice a falon gaba daya ya nufi wajen motarsa ya shige domin tuni an bude masa ya yi tsai yana kallon hannunsa dake jimke yana jiran fitowar Mamah
Tsuru tsuru suka yi a falon, kowa na kallon kowa har sai da Hajia ta gama yarda Baban gida wanke su ne ya yi tasss ya yi tafiyarsa, ta ja numfashi ta mike ta nufi wajen wayar Fatima ta dauka ta kalli Docter ta ce" Allah ya tashe mu lafia Aban Baba"
Murmushi ya yi yana sauke ajiyar zuciya, ya zata zata ce kana kallo ya mana tasss kaa kyale shi?

Sai ya ga bata yi mitar haka ba, hasalima murmushi ke boye a ni'imtaciyar fuskarta tana kallonsa
A sanyaye ya ce" To uman Sulaimana sai da safe in sha Allah zamu yi safiya mu zo mu ga Baiwar Allah, Allah ya bata lafiya yar gidan Ahmadu"
Da amen ta amsa ta yi gaba ta barsu a nan,
Da mamaki matarsa ta ce" Yanzu docter kana kallo Baban gida ya ja mana warning ya mana ihu a kai baka ce komai ba?"
Ido ya dan zarro ya ce" In ba abinki ba nima baki ga cewa ya yi maza a shirya ya kaini gannin likita ba?, Idan kuwa da magana Nana ta daukon wayata na kira maku shi ku zanta....."
Kumburo baki ta yi ta cire kanta bata bashi amsa ba, shi kuma ya yi murnushi ya dora da yi masu nasiha da sake jaddada masu a yanzu ba ruwansa idan sunna so su ci gaba ko su daina su da Baban gida, kuma walahi kar su yarda su ga fuskarsa dake boye, wace basu sanshi da ita ba, hakan ba zai masu da dadi ba
Su din kansu wani irin shaku da tsoro da tunanin me zai same su idan sun aikata ya ji labari suke
Ai kam kowace ta dauri niyar koda zata muzgunawa yarinyar to fa a boye ba dai a bayane ba, ita din kanta mahaifiyarta ta yi niyar ba zata kuma yi mata abu mai zafin haka ba, zata kiyaye dan irrin yadda yake gannin mutincinsu ba zata so su dawo yar tsama ba, da wannan dai du suka mike suka barshi da wace ke kwana a bangarensa yau
___________
Shiru, shi ya fi yawa a cikin motar har suka karaso asibitin
A hankali Mamah ta fito daga motar bayan an bude mata ta yi tsaye ta ga ya fito shima sannan ya tsaya yana magana da wani mutun dan Kasuwa da ya zo yana g
aisar da su harda Maman
Gaba ta fara yi ta karasa kofar dakin da Fatima ke kwonce
A hankali ta dakata da bude kofar da take son yi tana sauraron muryar Amir dake magana a nutse ya ce" Fatimah, dan ba lafiya sai ki ringa hawaye?, Ki daina kuka mana ki yi addu'a sai ki ji sanyi na ciwon kin ji ko yar gidan mamanta?"
Dan murmushi Mama ta saki ta murda zata shiga ta ji muryar Fatima tana hawaye, da kyar ta iya budar bakinta ta ce" Cewa suka yi wai idan aunty amarya ta bar gidan ABAH ko ta rasu ko Aban ya rasu shikenan tawa ta kare sai dai na koma na kama daki wai, kuma da na je auntyn ta sanar min inda mahaifina yake sai ta koroni tace bata son sake ganina a ind....

A inda take wai"
Amir a hankali ya dakatar da maganar da yake yi ta whatsup ya dubeta da duba irin na tsanaki,
A lokacin da zai yi magana, magana irin ta sanyayar nata da zuciya, da sanar mata cewa kar ta saki ta dauki haka a matsayin damuwa da sauransu Marechal ya karaso yana fadin" Mama baki shiga ba?"
A dole Mama ta bude dakin ta shiga da salama muryarta na fita a sanyaye tana kokarin kawar da damuwarta ta dubi wajen da Amir ke zaune nesa da gadon Fatima sosai, sannan ta kalli Fatiman tana karkaro murmushi ta ce" Zahra kin farka?"
Amir muryarsa a sanyaye ya ce" Ta farka mama, da saukina ko Zahran mamanta?"
Fatima ta lumshe idannuwanta ta kasa cewa komai dan dodonsu ya shigo dakin ya yi wani kikam yana kallonta bai kuma ce komai ba
Baki ya tabe ya ce" Ta tashi mu je gida, ba zaki kwana a nan ba Mamah"
Da mamaki Mama dake ciro mata madara mai sanyi daga frij ta dago ta dube shi ta ce"
*ALHAMDULILAH, DAGA NAN NA TSAYAR DA FEEE BOOK, NEMI NAKI HAJIATA KI SIYA MU PANTAMA MU MORE TARE......., AKOY CAKWAKIYA A TAFIYAR NAN MAI ZAFIN GASKE...., TO WAI ABINDA ZAI FARU A DAKIKA BIYAR DIN YA FARU KO A GABA?

MENENE SHI?

MEYE MA'ANAR HAKAN?

ME DAKIKA BIYAR KE IYA HAIFARWA?, MUN SANI NE
AKIKA BIYAR NA IYA TARWATSA BAUTA TA SHEKARA DARI, KAMAR YADDA TAKE IYA SAKA BAUTA , TABA IYA LALATAWA KO DAIDAITAWA, TANA IYA WANZAR DA ZAZAFAR SOYAYA KO TA KASHETA.......A
AKIKA BIYAR KOMAI NA IYA FARUWA, .......KU ZO MU JE MU JI LABARIN NAN DA SOYAYARSA A ZUCIYARMU DA SHAUKI
, taku ce yar mutan NIJAR SAJIDA*
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_13_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
Gyara zama ta yi fuskarta ta hade sosai ta ce" Docter, a yau, a kuma yanzu ina so matar cen ta budi baki ta sanar min, shin ta bani FATIMA Zahra duniya da kiyama ko bata bani ba?"
Gaba dayansu ido suka zuba mata, bama irin iyayen su Furera da mamaki da gannin karfin halinta, sai dai basu gama wannan tunanin ba ta dora da fadin" Idan har ta ce ta bani ina so ka zama sheda da kai da d'anka, walahi walahi walahi ba zan kuma daukan cin zali da wulakanci daga gareta ko daga wajen abokannan zamanta wa ZAHRA ba, wannan lamari ya isheni haka, na gaji Docter!

Kiyayar ta yi yawa, ita daya da ranta kowa ke wawusa?

Da ku zan ji, yayanku kuwa wannan zai ji da su ( ta fada tana nuna Baban gida), na rantse in dai ni na haifeka ka ja masu kunne du wanda ya saki ya sake cin zalinta ba da laifinta ba ina mai tabatar maka kai zan sabawa idan baka saba masa ba ko waye!, Ku kuma ina iya maka mutun a kotu a kan yarinyar nan!

Kun ji na fada maku!"
Hankalinsa ne ya tashi, ya kure Aunty Amarya da kallon tuhuma, wace nan da nan hawaye suka bale mata kanta a sade sunna diga a jikin hijabinta
Dubansa ya maido kan Hajia ya ce" Me ya faru?

Auta ke ce min kun je asibiti na zata ko ciwon nan nata na mara ne dake kaiku lokaci zuwa lokaci?"
Rai bace Hajia ta ce" Babu ciwon mara, abinda ya ainahin faru na san ba zamu taba sani ba sai a lahira, dan ita ba zata fada min takamaiman me aka yi mata ba, abinda na sani shine ta je wajenta ita kuma ta hankadota daga kofa wajen matatakala ta mulmulo ta fado a summe, yanzu haka maganar da nake yi maka likita yace sai mun kwana zuwa gobe dan bugawar zuciyarta ya ki daidaita, a cikin barcima haka take sauke ajiyar zuciya, wannan wani irin masifa ne, a kanki aka fara samun y'a haka ne?

Menene laifinta ita?

Ko menene matsalar ne?
Chapter 21 · 0% Book details