← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 110

Sashe 66

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah Allah nake yi na malakeki, Furena ni na san idan muka kule a daka sai dai wasu za'a gani a kwana kusa ba mu ba"
Da kunyar karya tana sasada kai tana rufe fuska ta zauna tana jin pant dinta a jike ama bata cire ba batama yi gagawar mikewa ba dan ba yau ya fara zuba mata abu a sama ba, ta dai dan hade cinyoyinta ta ja sket dinta sosai tana jin matsananciyar kauna a ranta da fatan gannin wannan rana da Sahabi yake kwadaita mata, kai itama ta san a yadda sahabinta ya iya soyaya sai ya summar da ita dan dadi, inda Sahabinta yake birgeta shi ba dan iska bane, soyayarsa domin Allah ne, bai taba taba mutuncinta ba, watau budurcinta, shi dai yana son shafa mamanta da sauransu bayanshi baya wucewa ko'ina
Jakar da ta dukunkunne ta janyo yar baka madaidaiciya ta bude ta shiga warwarewa
Kudaden da suka zubo daga ciki ya saka shi zarro ido ya zabura ya zauna har jikinsa na rawa yana kallon kudin yana kallonta
Da tarin soyaya ta miko masa daurin kudin ta ce" Ka ga shi yasa yau na yi wuri na dauko kudin nan, a cikin gadon Mamanmu ne na dauko na ce zan baka ka fara neman sana'ar da ta dace, ka ga kana fara sana'a sai a yi maganar aurenmu dan Yayanmu baya yarda da maganar namijin da ba sana'a, shi ba damuwarsa kudi ba, aa, mutun dai ace yana nema, ka ga kudaden nan da yawa komaima kana iya gwadawa ko yaya?"
Wani shegen yawu ya hadiye mai santsi a wuyansa, da sauri ya ringa gyada kansa cike da zumudi ya makale murya ya ringa yaba mata, yana mata addu'a irin manya manyan nan, ringa saka mata albarka yana jadada mata kaunarsa, ya sake tsumata ya sake sakata fadawa a soyayarsa , sannan ta mike tana gyara jikinta cikin dabara ta cire pant din nan ta ajiye a nan tana boye fuska dan kar ya gane , pant din ya fara mata kaikayi ne kuma sai take ji kamar wari warin abin Sahabi kar ta koma gida a gane
Da kyar ya barta ta fito, sai da ta sanar masa bata so a fara neman kudon bata nan sannan ya barta ta fito
Tana fitowa gabanta ya yanke ya fadi sanadiyar gannin LARABA a tsaye tana kallonta tana murmushi
Ido ta ringa kikiftawa ta nemi kidimewa, Laraba ta yi gagawar batar mata da tunaninta ta ce
Ka ga yan soyaya, shine a shigo a shige ba'a ko nemana, tunda Uma tace yaya bai farka ba na tsatsamci hajiarsa na ciki, sai wani shining kike kin ga masoyi ko?"
Ajiyar zuciya ta sauke, a tunaninta bata ji komai ba, bata kuma gane komai ba, dan haka ta fito da kyau kasa kasa ta ce" Aunty Umma hala ta san ina shiga nan dakin?"
LARABA ta dan doke kafadarta suka karasa ciki suka zauna ta ce" Le kuwa, ko ta sani waye ya isa ya shiga tsakanin soyayarku da Sahabinki, ai babu, ki saki jikinki in fada maki gidan sirikanki kike , kanwata wai na ji kishi kishin an raba maku gado?"
Nan fa Furera ta saki baki ta ringa sanar mata dukka kaf abinda ya faru, rabon gadon, abinda maza suka samu, abinda su mata suka samu, abinda iyaye suka samu, kai abu dai gayanan kamar na sakaken mahaukaci LARABA na mamaki tana gyada kai ta ce" Lalle iyaye masu kudima rahama ne, yanzu ke din nan rikakiyar hajia ce gaki a ganana, gaskiya kun ji dadinku ku kam, kin ga bara na tashi na raka ki yau kam zan shiga wajen Mamah na duka na roketa ta aura min danta kar na mutu da sonsa, dan na riga na san shine duniyata , kaf gidan za'a kankaro wulakanci ne idan na tuna lahaula wala kuwata bari na sako hijabin Mamanmu"
Furera na murmushi tana jiranta ta dauko hijabin ta fito suka rankaya, da zata fita sai da ta fada dakin yayanta a gagauce ta ce Walahi ta san kudi aka kawo masa ya bata ko yayane ko ta sanarwa su Umma su amshe, yana masifa ya yanka mata ta totse ta bi bayan Furera da gudu
Sosai gidan ake dan haba haba, dan rana har ta yi masu aiki na aikinsu tukuru, masu kallo na yi, dukkan wani mai uzuri yana yin abinsa hankali Kwonce
Ratsawa suka yi suka wuce suka zo bi ta wajen da yan matan gidan ke yin zance, nan suka ga bakon ZAHRAH , watau Hasan hakimce saman kujera yana dan latsa waya, ga dukkan alamu ita yake jira
Kasa kasa furera ta ce" Kin ga manemin auren shegiyar gidanmu nan, shi da bashi da mafada"
A zabure LARABA ta waiga ta sake zuba masa ido, muryarta har tana rawa ta ce" Kina nufin wancen hamshakin ne zai auri marar uba?"
Furera ta tabatar mata, LARABA ta ce" Kuma ya sani ko dai rufeshi za'a yi?"
Furera ta dage kafadu ta ce" Wa ya sanin masu, ta yiwu a rufe za'a bashi kashi sai ya bude ya ji wari"
Laraba zata yi magana suka ji muryar Rukaya a dake ta dan daga muryarta ta ce" Ke FURERA zo nan"
Furera ta juya da sauri dan tsoro ta ji kar dai aje tana kusa da su suke maganar, sai ta ga nesama take da su sosai kuma tare suke da ZAHRA ga dukkan alamu wajen bakin zasu je, ta sha wata doguwar riga ruwan goro sai haska wajen take yi ita ga mai kyau
Karasowa ta yi ta yi wani kikam ta ce" Gani "
Rai bace Aunty Rukaya ta ce" ke daga ina kike?"
Furera ta kalleta da dan mamaki ta ce" Aunty ban gane daga ina nake ba?"
Aunty Rukaya ta zarro idannuwanta da masifa madaukakiya fiye da ta fureran ta ce" amsa zaki bani ko raini zaki kawo min na babala maki mari a wajen nan ke yar rainin hankali?

"
Dan matsawa ta yi tana fadin" Daga, daga gidan su Aunty LARABA nake"
Rai bace Aunty Rukaya ta ce" Ke kam an yi shashasha, Larabar sa'arki ce da zaki ringa zuwa wajenta ko kawarki ce?

Bayan kina soyaya da yayanta sai ki ringa kwasar jiki kina shigar masu gida kamar wace kika fita daga tsatson mahaukata?

Ke ki kiyayi duniya da abinda yake cikinta, na kula kanki hayaki yake yi sosai ki guji harkar namiji, ko kannen mamanki ne ki guji harkarshi bale sindirkin kato wai Sahabi ko me?, Ki kiyaye mutunci daya ne kwal idan ya zube baya kwasuwa na fada maki!"
Daga haka ta ja tsaki ta kama hannun ZAHRA ta ce" Ke kuwa maza ki je ku gaisa ki dawo min yanzu kin wani ja kin tsaya mutun na zaune tun dazu kin kasa zuwa wai mutane a gidan"
Da sauri Zahra ta tafi, ita kuma ta juya bayan ta saukewa Laraba harara ta koma ciki tana jan tsaki, kwata kwata Larabar nan bata yi mata ba, kana ganninta ka ga mai tsagen munafukai da duniyanci a fuskarta, ko ita ba zata iya kawance da ita ba ama ita Furera ta samu kawar yi, Allah ya wadaran naka ya lalace
Rai Bace Furera ta dawo tana fadin" Sai dai ki nemi ginshikirin kato a wanda zaki aura ba dai Sahabi ba, banza mai fadan masifa irin na uwarta, ku an nuna maku wauta kun kama yar iska kun mayar abin ado har wani rakata kike zance, ya dai kwakuleta ya gudu irin na sauran me zai yi da marar uba, sakarcin banza sakarcin wofi kadan take jira ta nemi dukan mutun, gwara a maki auren ki tafi in bararaje ni da sahabi kuma nan gani nan bari inma sonsa kike sai dai ki mutu walahi!"
LARABA ta ja tsaki tana sauraronta, ta harde hannayenta ta kalli nan ta kalli cen, saka da warwara take yi, wani kululun bakin ciki ya tsaye mata a zuciya
Rai bace ta ce" Kin ga, zan shiga idan na gama wani abu, ki je kawai bara na je nima na yi wani abin"
Furera ta kalleta da mamaki ta ce" Ke kam Aunty yauma ba zaki shiga ba kuma?"
LARABA ta ce" Ba zaki gane ba, ba saboda wancen nunar ranar aka zageki ba?

Zan je na sanar masa wacece ita sai na ga ta tsiya, in dai yanada magaya me zai yi da mace irin wannan?, Wuce ki yi tafiyarki ina zuwa"
Wani irin farin ciki ne ya ratsata da jin dadi ta ce" Ni na tabata basu sanar masa ba Aunty, dan Allah ina cen ina jiranki na ji yaya kuka yi da shi Aunty, dan walahi sam mutum mai kamala haka bai dace da yarinyar cen ba"
Murmushi LARABA ta yi ta juya ta nufi hanyar fita
Ta zo daf da fita daga karamin get aka bude gidan mota biyu ta shigo mahaukatan motocin MARSHAL bakake sidik suka shige a guje
Da ido ta rakasu tana dafe kirjinta a hankali ta furta" Allah ka malaka min bawan nan naka, Allah ina sonshi, ya hadu ta ko'ina kuma da ni ya dace, nice na dace da zama a gefensa idan ana tuka mu muna tafe ne kamar sarki da sarauniyarsa....., MARSHAL Ina sonka............."
Sai da ta gama surutunta a tsaye sannan ta fice ta tsaya tana jiran gannin an bude get, dan ta yi niya dan acaba ko sahu sai ta shiga ta bi shi har inda zai je ta masa bayani, ita fa bakin cikin yarinyar ne take yi kamar me, yarinya ba shafe shafe ba komai ama ta fita haske ita da take kwailin, du ta bi ta kwace samarin anguwa kowa so yake ta yi mu'amala da shi, sai dai ta kare a karuwar ysn anguwa ba dai sama fa haka ba!
Chapter 66 · 0% Book details