← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 110

Sashe 31

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mtsssssss" mama ta fada da karfi tana jan tsaki sannan ta karasa cen karkashin dirowarta wace take kulewa da ky ta saka makulin ta bude ta zaro wata akwati ta budeta itama ta ciro wasu takardu da hotunna a tare da su ta zo inda take zaune ta ajiye mata hoton wata budurwa mai kama da ita sosai da kuma na wani datijo wanda tana iya cewa kamar ta sanshi kamar kuma bata san shi ba, fuskarshi dai ta fi tsaye mata a rai sosai
Dagowa ta yi tana kallon Mamah dan bata ga alakar wadinnan mutanen masu kudi da alamun hutu a tatare da su da maganarta ba
Mamah ta zauna tana fuskantarta ta ce" kamar yadda na fada maki, mahaifinki bai rasu ba, a yadda Baban gida ya kawo min binciken da na saka a min tun daren da kika fadi cewa ya'yan mahaifiyarki ne ya fada maki kika samu cikin Zahra hankalina ya tashi, na samu malan na yi ta magiyar sunnan garinku ama ya ki ya sanar min, sai da Baban gida ya yi kiransa a waya gannin ina kuka ya tambaye shi ya sanarwa baban gidan ba tare da jan maganar ba, shine ya tashi baban lauyansa ya tura shi garin ya je ya gana da mai garin garin, a nan ne fa aka samu bayanan nan cewa ashe mutumen nan da ya sama maki cikin Zahra ba dan uwanku bane, baku da hadi da shi, shi din mutun ne kawai mai zuwa birni saide saide da aikace aikace, ya taimakawa mamanki ne a lokacin da ta yi fushin zuciya sakamakon abinda mijinta ya aikata, wannan da kike ganni a hoto shine mijin nata, kuma shine mahaifinki, ya yi taraya da y'ar aikin mahaifiyarki ne har ta samu ciki ita kuma Maman naki ta yi fushi ta gudo da ke y'arsa daya tal ta sunna a lokacin kina kankanuwa ta shiga duniya, shi mutumen nan ya ce zai taimaketa da sharadin zata yarda su je a matsayin kanwarsa, dan ba kowa ya san mahaifinsa ba a kauyensu, ba zasu san wacece ita ba, an je da ke kina rayuwa a tare da su ne mahaifiyarki kuwa na jinya a boye dan abin ya taba mata zuciya domin bata taba tunanin mijinta abin kaunarta zai aikata mata haka ba, sai kuma ga maganarki ta faru, mutumen da ya ajiye ku a gidansa ashe yana da boyayan halin da ya hanna shi zama da mata, watau ya fiya fade fade, shine ya yi maki fyaden nan kika samu cikin nan, da maganar ta bilo ta hadewa mahaifiyarki ta daki zuciyarta har ciwonta ya ci karfi ta rasu..............., Nana ita rigimar da kike yi da tsawalawa bakima san ainahin wacece y'arki ba dan a tunaninki bafanki ne ya maki cikinta bayan zindirkin dan duniya ne kawai, yau koda a yadda kike tunani kika haifeta bana tunanin zaki ringa wulakantata irin haka, y'a mace take fa, kar ki manta da haka tana da rauni Nana"
Hoton take kallo, tunaninta ya kasa tsayawa waje daya, ta rasa me zata yi tunani a kai, ba maganar Fatima da Maman ta bige da ita ke mata yawo a kai ba irin maganar hoton dake hannunta wai mahaifinta, lalle duniya an ci gaban da bawa zai sha mamakin ci gaban, shekarunta nawa a cikin tunanin nan gashi rana daya tak zuwa ta biyu mai damar sannin abinda ake cikin ya sani kai tsaye?

Muryarta na rawa kuma a shake ta ce" Wannan din kamar na sanshi Maman Baban gida?

Fuskarsa kama ana haskota a TV"
Mamah ta sauke numfashi, muryarta a raunane ta ce" Sanane ne, baban mutun ne, tabas kin san shi, shine dai wanda ake haskowar"
Sake zuba masa ido ta yi a hankali ta dago tana kallon Maman , idannuwanta na sake cikowa da kwallah ta ce" A yanzu da ya rasa wasu ya'yan ne yake nemana har ya je kauyanmu ko me nadamar cin amana ce ta same shi bayan wace ya sani tana kasan kasa?"
Mama ta sake dubanta ta ce" Ban san wannan ba, abinda mai garin yace min shine mutumen yace idan har aka ji labarinki, ko a ina kike a taimake shi a sanar masa , shi kuwa zai bada gagarumar kyauta, domin ke kadai kika rage a cikar farin cikinsa da mahaifiyarki, tunda ta rasu zai neme ki a duk inda kike, na ce masa idan na sanar maki in da dama zan sanar masa a nemi mutumen, baki ga yadda yake neman ganninki ba muka kiya"
Da sauri ta ringa jimke hoton da takardar dake hannunta tana kausasa fuskarta
Muryarta a kausashe ta ce" Abinda ya aikata ne aka aikata min har nima na haifi y'ar gaba da fatihar....., shi kuma ya dauki y'ar so dinsa ya cencana ya rike ya nunawa soyaya , ni kuma da uwata ko oho......

Walahi Mama babu wanda za'a nema , dan ba zan taba dubansa daidai da second daya ba , ko wanene shi , shine silar shigata kunci, kuma shi ya kashe min uwata!"
Daga haka ta mike ta yayumi hijab din da ba nata ba ta zurma ta yi waje, ta bar Mama tsaye baki sake tana mamaki da al'ajabin wannan mata da tunanin wannan zuciya tata kamar aminiyar fir'auna?

Tsaki ta ja ta tatare ta mayar da komai sannan ta boye Ky din ta fito itama
Fitarta kawai suka ganni ta tsakiyar falo sunna gyara abincin Baban gida
Sai da gabanta ya yanke ya fadi bayan ta shaki kanshin turarenta ta tabata itace, sai kuma aikin da take yi da kaza kazar ya dawo yi a hankali a hankali har sai da Mamah ta sauko dan gannin ko sun shigo , ta same su sun gama jerawa sun rufe da abin rufewa
Da kula, muryarta da yar damuwa ta ce" Yauwa maza ku kai bangaren babanku ku dawo yanzun nan ina jiranku , sunna cen sai su wuce da shi dan ni kwonciya zan yi, ina sakon nawa ne Fati?"
Zahra ce ta dauko abin murza jikin ta mika mata tana fadin" Mamah ta ce wannan na dari biyar ne, dayan kuwa karami ne dari biyu da hamsin ne"
Maman ta amsa tana fadin" Ya yi kyau ai, idan kika murza min jikin nan nawa da shi ina mikewa sai na ji garas sallar nafila a tsaye nake yi ba ciwace ciwacen jiki, zanma kaiwa babanku shi a gwada a kafar nan tasa mai sundumewa tamkar turmi ko a dace"
Auta ta yi yar dariya ta ce" Mamah ABAH fa baya son magannin hausa"
Mamar ma ta yi dariar ta ce" Ai shi na turawanma baya so, gashi Docter"
Da wannan dai suka dauki kayan abincin, Zahra na rike da kwondom, auta kuwa na rike da jug din suka karasa bangaren ABAH
Sun dan jima a kofar sunna sake duduba yannayin hijabinsu, shin ya sauka har kasa?

Ya rufe jikinsu sosai bai mane masu a jiki ba?

Auta dai ta ki sanarwa Zagra ne dan karta ce sai ta koma ta cenzo hijab ama gaskiya hijabinta yana mane mata a jiki, gani ta yi ai baki ne kuma ai dare ne ta yiwu har su shiga su fito bai san da zuwansu ba dan idan Yayah baba na gaban ABAH baya kula kowa abinsa
Dan jan bakin leben Auta ta goge tasss sannan suka ja doguwar salama a nutse suka dakata dan jira a basu izinin shiga
Muryar Abah da Aban Hafeez ne suka daki kunnayensu wajen amsa salamar, shima ya amsa din ama bai daga muryarsa sosai ba ya dai amsa din ne sannan ya ci gaba da murmushin hirar Aban Hafeez da ABAH
Auta ce a gaba , dan haka ita ta fara gaishe su tana kokarin karasawa dan ajiye sakon, itama ta duka ta gaishe su sannan ta nemi bin bayan autar da nata kwondon tana dan satar kallon baban yaya da tunanin dayan kuwa waye shi?

Shin wai yaya maganar Ma'awiya ne?

A hankali ya dago dubansa jin kanshin turaran da suka shigo da shi ya zarta misalin yadda ya dace ace sunna anfani da shi ya sauke dubansa a kanta, domin idan bai manta ba itace mai son saka turare da yawa har ya ringa zama daram a hancin mutane , ya san haka ne dan Mamah na yawan mitar turaren Zahra idan zata sa a kawoma yan matan turaruka sai tace kar a kawowa zahra mai karfi, koda yake sai ta saka da yawan da za'a jiyo shi tun daga nesa, sai ta saka Amir yayi mata shegen dukan da zata daina yiwa jikinta barin turare, idan zata fita ko zaman gida ta yiwu zuba shi sosai take yi kamar ruwa a jikinta har kafarta, shi din kansa Amir din ya sha masu mitar nan yana ce masu su rage anfani da turare mai yawa, tun daga gida ake sabo kar sai sun yi aure ya zamo masu matsala, ita kuwa Zahra basu san cewa ta riga ta sakawa ranta a gaskiya sai dai su yi hakuri domin mace sai da kanshi, ba ruwanta da wani wai idan ta yi aure meye meye ai yanzun sunnanta ba kazar kowa ba, dan haka dole ta ba ranta abinda yake so tunda Mamah ta siya mata
Kafe idannuwansa ya yi a saman fuskarta tunda ya kalli hijabin jikinta sau daya tak ya dauke dubansa daga jikin nata yanai mata kallon da ya dace ace ta fahimci inda ya dosa , ama sai ya ga girim girim karasowa take yi hankali Kwonce bata ko jin kunyar baki a wajen jikinta a fili, dan hijabin nan shi da babu du daya, wannan ai rashin kunya ne da raina manya da rashin sannin ciwon kai! a lokacin da Abah ke fadin" Ga auta jaja manya ga Fatin Abanta, me na samu ne daga mamanmu?"
Yar dariya Auta ta yi tana fadin" Abah na baba ne fa"
ABAH ya tabe baki ya ce" Haka fa, na kusa masa aure dai ya je ya karata da matarsa da girkin gidansa, an ce kulun sai ya sakan mata aikin girki?
Chapter 31 · 0% Book details