← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 110

Sashe 74

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kuka yana kuka, sunna ba zasu iya rayuwa babu junna ba......."
Wani irin tukuki ya tare masa wuya, shi ya san nemansa Aban Ahmad yake yi idl rufe, in sha Allah shi kuwa zai bashi kunya dan ba zai biye masa ba,
Mikewa ya yi ya shiga haurawa sama, shi kuma ya yi murmushi ya dan daga murya ya ce" Zan wuce dan ban gama rabo na, zamu hade kuma gobe mu shirya yaya tsare tsaren ina nema na bakan zai kasance tunda uban amaryar ne zai yi wuf da ita dole dan karere zai daura, a huta lafiya d'an nan"
Ya gama fada yana murmushinsa da shafa gemu ya mike ya fice, dan kuwa zasu zauna da matarsa a kan maganar shirye shiryen auren, yana so ranar taro ta yi taronta a gidansa, yana so kowama ya ji ya kuma gani, baya kunya baya tsoron wani dan tahliki a kan maganar, baya jura wani ya bashi, tunda har ya sabawa mahalicinsa a kan haka to kuwa shirye yake ya amshi abinsa ya kuma tarairaya ba gudu ba ja da baya
MARSHAL kam hayewarsa ya yi, idan ya tanka masa, tabas dakinma ya tanka masa, kyale shi ya yi ya yi shigewarsa ya barshi da halinsa, tunda haka yake ai ba zai biyashi ba su hadu su raba hali, in dai halinsa sai ya yi ta yi
A haka kwanaki biyu suka shige, ya zamto yau a kwana na uku ana gobe daurin aure yau yan matan suka yi dan shiri nasu suka gayaci kawayensu aka yi masu girke girke dan daidai misali , ya kasance kawayen nasu basu da wani yawa sannan ba masu kwaramniya ba, su furera nema suka kawo kawaye masu dan rawar kai domin ko a lokacin da masu kunshi suka zo dan yiwa amare Mamah ta umarci a fara yiwa ZAHRA, bayan MAMAH ta tafi kawar Furera da Zahran ke birgeta ta ce" Kawata, wannan y'ar uwar taki du ta fiku kyau, kina gani lafayar nan tata irin ta amaren yadda ta fito da ita?

Kai ama mijinta ya dace gaskiya shi za'a yiwa barka"
Da haushi haushi kasa ta ce" Ke bafa wata amarya bace, waye zai auri shegiya?

Kawai iya yi ne na marikiyarta, ta wani sa an mata kitso ke inaga harta gyaran amaren nan na bangaren nan tare take masu, kamar wace zata aurar bayan saurayin ya gudu da ya ji shegiya ce"
Da mamaki kawar ta ce" Shegiya kuma?, Ba yar uwarki bace?"
"Ba dangi iya ba na Aba, matar babanmu ta zo da ita y'ar gaba da fatiha ce, kin san su dama shegen kyau ne da su ai" ta karashe tana gyatsine da sake jin haushin haduwar da ZAHRA ta yi, dan ba karya harta pos din dake hannun ZAHRAN mai manyan kudade ne da ita dai ba zata iya siyawa kanta ba, tunda mahaifiyarsu ta sanar masu waye uban Zahran bakin ciki yake damunsu, wani irin wai uncle Aban Mai sunnan Docto?

Har yanzu su sun san karya ne sunna dai jiran ta fashe ne, an ga kamili atajiri za'a lakaba masa tsiya
Mamah kuwa a bangarenta tana cike da mamakin zuwan yayar Marigayiya,
Sau uku tana son ta dan tambayeta shin sun yi magana da MARSHAL kuwa?

Sai wani abin ya bige mata hankali, karshema sai ta saka a ranta ai kawai ta sani ne ta yiwu ta hakura ko kuma tana tunanin zai karrata a ta biyu ne oho, ko a harkar girkin amaren itace ta kasa ta tsare ta yi babakere da komai ta shirya komai, ita dai in dai tsabar zumunci ne da yarinyar lalle zata iya yin zumuncin da ita, gaskiya ai ba laifi mutumen da zai zo gidanka ya tayaka murna?

A yanzu ta fi mayar da hankalinta kan harkar lefen Zahrah da kuma baki, lefen yana boye ne a bangaren Aunty, lefe har kamar ba ya daya aka hadawa ba, lefen na gani na fada ne ko makiyi ya kyasa, irin rikicin da suka kwasa da aunty amarya kuwa sai wanda ya gani, dan kuwa tunda Aban Ahmad ya zamo mai naci sai tace Mamah ta daina sonta, sai fa suke yar tsamarsu ko a kan maganar ajiye kayan sai da MAMAH ta yi mata jan ido tace in dai ta kori kayan ya tabata ita ta haifi ZAHRAH sannan ta barsu a inda suke, ita Aunty amaryarma mamaki ne a ranta, Marshal zai auri Zahrah, sai kuma wani abu mai kama da salama da ya mamaye zuciyarta ama bata nunawa kowa ba, bata kuma bari kowa ya fahimta ba, daga nesa take hangenta, bata shiga harkarta sai idan waje ya matse masu, ta daina ce mata mama sai dai Aunty, wannan ya sa itama yanzun bata zaginta ta kuma daina yi mata bakin nan, ita dai kawai dai ba ruwanta da ita ne..

A haka aka cinye daren karshe na daurin aure har yan matan suka watse ya rage na bangaren Mamah inda suka tare a dakin aunty Rukaya sunna ta firarsu da dariya da yayunsu da suka zo da
ansu, fira suke yi na zumunci ba kyarar kowa ba hantarar kowa
___________________________________
Mawaki yace, ranar muke jira yau gata ta zo
Haka din ne, kwarai kuwa haka din ne, ranar muke jira muma sai gata ta zo......dukkan wani kwai da kwarkwata na ahalin gidan, abokanan arziki, dangi na nesa da ba kusa sun samu halarta baban daurin aure, daurin aure na farko bayan rasuwar DOCTER, daurin auren da baban dansa BABANGIDA zai jagoranta tare da manyan malamai da manyan aminan arziki tsifagi datijai da yara na anguwa da kewayenta sun samu halarta a wannan taro da ya dauki dumbin jama'a saman kujeru ne da saman tabarmu, abin dai sai hamdallah kawai domin lamarin ya kayatu sosai
A hankali BABANGIDA dake jin tamkar abin ya fi karfinsa, tamkar ba zai iya aikatawa ba, dumbin jama'ar nan yana ji tamkar ya fashe da kuka idan ya duba babu mahaifinsa ya matso kusa da baban amini datijo limamin masalacin juma'a ya dan saurara yana jin tambayoyin da yake karra yi masa bisa sunnayen da aka bayar, wanda na farko ya fara tambayar Nasa Shi da na yarinyar nan har zuwa na ta karshen, ya jinjina masa kai yana sake tambayarsa ya tabata iyayen amaren du sun amince da daurin auren a nan?

Ya kuma jadada masa kwarai sun amince domin baki daya da kansa ya je ya nemi alfarmar a daura a masalacin kuma sun amince babu wanda ya kawo masu matsala a haka sannan ya dan koma gefen Hamad watau ABAN AHMAD ya sada kansa yana jin jawabai da haramar daurin auren, yana kuma kallon Aban Ahmad din ya matsa kunnayensa na jiyo masa dukan masayar kalamai na ana nema da an bada har aka gabatar da daurin aurensa shi SULAIMANE AHMAD SULAIMANE da FATIMA ZAHRAH HAMAD da sadakinta a hannun mahaifinta a hankali ya lumshe idannuwansa yana jin ana fadi a lasifika daga waje dan yan waje su shaida domin wajen ya cika dole wasu a waje suka zauna .............

A hankali ya bude idannuwansa da kirjinsa dake dokawa ya zuba dubansa a kan Aban Ahmad da yake sanar masa ya matsa ya nemi auren mazan dan shine alwalinsu.....................hakan ya daka shi hadiye yawu da kyar ya matsa din ya shiga gabatarwa manya na gefensa sunna taya shi dukka har aka gama daure dauren auren da ya dauki lokaci sannan aka shiga rabon goro da sauransu, hakan ya sa ya fito da yar wayarsa dake ta tsuwa ya fita da dan sauri ya daga domin misss calll ne birjik a wayar, sai dai na Mama kawai ya iya dagawa a tausashe ya ce" Asalamu alaikum Mama?"
Mama dake ta kiyaye iface iface da koke koke a dan rikice ta ce" Wa alaika salam Baba, an gama daurin auren ne?"
Da dan gagawa ya amsa dan yana iya tsinkayo hayaniyar wajen kamar ta yi yawa da tunaninsa....

Mama ta ce" Alhamdulilah, ka ga ko za'a samu a salami mutanen nen ne, ban san wa ya yi kira ya sanar da maganar daurin auren naka ba dai, wancen marar hankalin ta fara zage ,zage da fadin ba zai yiwu ba, zancen dai ya bazu, ka ga harda yayar marigayiya gatacen wai ko aljannunta sun tashi sai ihu take ana ririketa, ga itama yar gidan malan nan makota sai ihu take tana kuka da fadin sai ta kashe Zahra, zahran da kyar muka samu muka shige da ita ni dai abin ya fara rikitani kawai a salami kowa Allah ya bada lada ya isa halanan, ka ga iyayenkuma sai balaki suke yi, abin dai yana nema ya fi karfina.........."
Yana sauraro yana nufar motarsa ne, sabuwa dal din motar da ya fitar yau yau masu tsaron lafiyarsa na binsa da sauri, direbansa kuwa ya bude yana sara masa ya shige yana badfa umarnin su nufi gida a hankali ya cr" GANI NAN "
Wayar ya katse zuciyarsa na turiri, lalle yau zai fitowa kowa a mutun a gidan nan, baya son wulakanci, a me suka dauke shi ne?

Watau so ake yi tale taken rainin ya kai har haka?

Lalle yau zai je ya aikata abinda yake wakawa ya kasa aikatawa..... za'a ware mai hankali da mai asalin aljannu tsakaninsu shi da su baki daya!

Motar na tsayawa ya sabe babar rigar dake saman tufafin sa , ya waiga yana gannin kannensa na biye da shi da sauran jama'a, kasa kasa ya ce" BANDA ahalin cikin gidan nan kar a bar kowa shigowa....ina zuwa....."
Rai bace ya nufi get din tamkar wani mahinmancin zaki ya shiga ya
.........
Chapter 74 · 0% Book details