← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 110

Sashe 29

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukawar da zai yi kunnayensa suka jiyo masa salamar Abun Hafiz, makocinsa da yake zaune a saudiya, saukarsa kennan ya shigo masalacin shima, mutumen da suke zumunci sosai da Marshal, ya girmi marshal a shekaru ama sunna zumunci tamkar abokai, sunna zama su yi hirar rayuwa, yanzu haka karfin shigowarsa dan ya masa gaisuwar rasuwar nan ne, domin tunda aka yi hankalinsa ya yo gida yana matukar jin Marshal a zuciyarsa, hakama dansa Hafiz yana kiran Marshal dady ne, irin soyayar dake tsakanin Hafiz da Mareshal ba'a magana, sosai yake kaunar yaron haka shima yaron
Murmushi ya saki ya kama hannunsa suka yi musabaha yana amsa salamarsa
Da yar fuskar mamaki ya ce" Dama zaka shigo ba labari?"
Dariya Aban Hafiz ya saka yana nuna masa an fa fara haramar sallah, hakan ya sa da gagawa ya shiga daura alwallar suka yi alamun zasu hade bayan an fitto daga masalacin
Bayan an gama sallah a motarsa suka karasa gidansa, a bakin get suka yi salama da nufin idan sun fito sallar isha'i sa zanta
A dan gagauce ya shirya dan fitar da zai yi bayan sallar isha'in , tun daga suturar dake jikinsa, takalman dake kaffafuwansa, agogon dake hannunsa, da mansheste din dake daure a tsintsiyar hannunsa zaka fahimci ba karamin mutun bane shi , sannan zai iya shiga zuciyarka a kallo daya tak , yana da dorinar ado ta hadu da hadaden gaye ......mata na matukar wahaltuwa a kan halitar bawan Allahn nan
A nutse ya karasa wajen fara kal din motar da sergent ya fitar mai baki sidik din madubai ya bude ya shige ya kunna ya nufi wajen get
Haske Aban Hafiz ya yi tsaye sunna gaisawa shi da mai gadi tsoho kennan wanda ya zamo mai gadi na amana, wanda baya cenzawa tunda ya fara zaman gidansa na shi da iyalinsa ya ajiye shi, mutun mai adini da taka tsantsan a lamarin rayuwar yau da kulun, yana zaune ne a gidan da nasa iyalin shima ama ba zaka taba gannin wani abinda ba shi ba , yayansa uku ne dama, mazan daya na kasuwanci dayan kuwa na karatu ba ji ba gani dan soja yake marrarin zama Mareshal kuwa yace ba damuwa ama sai ya yi karatu, sai yar karama guda wace ba zata zarce shekara goma sha daya ba, ita kuma Yar amaryarsa ce dan uwar gidan a kauye take tace ba zata iya zaman birni ba
Dan murmushi ya yi bayan Aban Hafiz ya sake ba baba hannu sun gaisa ya zagayo ya bude gaban motar ya shige yana fadin " Mu je"
ya kalle shi a tausashe ya ce" Ka san inda zan je ko dukana za'a yi zaka bi ni?"
Shima murmushin ya yi ya ce" A kusa kusan nan?, Bama tunani, na fi tunanin zance zaka je wannan daukan wanka haka kana lumshewa ya'yan mutane ido, mu je nima na gani ko na kama kanwar amaryar taka...."
Wani murmushin ya yi ya daga birkin motar ta fara tafia a hankali ya ce" Yau fa bata fi wata biyu da rasuwa ba, ama sai a ringa gannin wai zan iya yin aure da gagawa kamar wani acici.....?"
Jikin aban Hafiz ne ya yi dan sanyi, a hankali ya ce" Sorry freind, Allah ya jikanta da rahama"
Murmushi ya yi shima a hankali ya ce" Amen ya Allah.........."
Sai kuma motar ta dauki shiru kadan har ya juya ya gangara wajen masalacin suka sauka suka shige cikin masalacin suka sake bin sallar isha'in
A lokacin da liman ke shafa fatiha a hankali ya shafa tasa ya lumshe idannuwansa yana dora hannunsa na dama a saman kahon zuciyarsa......................

A hankali ya lumshe idannuwansa yana sauraron tarin rikicin da take doka masa, irin bugun da take yi a duk lokacin da ya ji tana gudun jinnin dake sheda masa itama tana raye tana kuma dora lalle lale sai an yi mata abinda take so sai ta shiga bashi tsoro, so take yi ta nuna masa wannan lokacin fa ta kai wajen da bai isa ya tankwasata ba, so take yo ta nuna masa cewar ita keda shi ba shi yake da ita ba, idan tana yi masa irin bugun nan sai ya ji kamar zata sumar da shi ta fitar da shi daga hayacinsa ko ta saka shi da girmansa da darajarsa ya je ya aikata aikin da za'a ce wai BABAN GIDAN?

"Aboki?" Ya fada a hankali bayan ya dafa gefen kafadarsa ya dan matsa a hankali, domin kiran nan na uku kennan ya yi masa bai amsa shi ba har gabansa ya fadi
A hankali ya bude idannuwansa da suka yi masa ja ya sauke a saman fuskar Aban Hafiz
Damuwa a saman fuskarsa ya ce" Me yake damunka SULAIMANE?"
Idannuwan nasa ya lumshe a hankali ya mike daga zaunen da yake ya yi dan murmushi ya ce" Ba komai Yak"
Da ido ya raka shi har ya saka takalmansa sannan shima ya fito da sauri ya saka yana biye da shi har suka shiga mota suka dauki hanya Yak ya ce" Ko me yake damunka ya dace ka yi hakuri, na san ba zai wuce rasuwar iyalinka ba, ka yi hakuri abokina, ka bita da addu'a ka ji?"
"Rasuwa.......?, Tabas rasuwarta na damuwa, sanadiyar rasuwar tata nema nake neman saka wata damuwar da na dane karfi da yaji a lokacin da take nan.......ama mutuwa ai dole ce freind, nima zan mutu, ina kuma yi mata addu'ar samun rahama....

Believe me, babu abinda yake damuwa " ya fada a tausashe yana shan kwana ya dauki babar hanyar dake iya sada shi da gidan Minister
Shiru kawai ya yi, ba dan ya yarda da abinda yace ba, saima dan son gane in da gasken bashi da abinda yake damun nasa
Yar daria ya yi ya ce" Wai sai kace acici, yaushe ka shiryu ?"
Shima yar dariar ya yi ya ce" Na kula bayan kin dauko min maganar yarona da keke yi dan jarida kuma ka zama a saudiyar"
Shima yana daria zai yi magana ya ga sun dauki kwanar gidan minister na army, hakan ya saka shi dan zuba masa ido har ya ga sun karaso an bude masa get ya shiga da gudun gaske, maimakun ya karasa inda ake ajiye motar sai ya ga direct ya shige cen ciki da motarsa har sai da ya isa filin gidan ministern sannan ya ja ya tsaya a inda suke hangen Ministern, da sauran ma'aikatan tsaye
Yana juyowa dan tambayarsa ko lafia ya ga ya hade fuska ya yarda a zuciyarsa ba zuwan lafia ya yi ba, baima samu damar tambayar tasa ba ya ga ya bude ya fice bayan ya ce" Freind bani minti daya mana....."
Carbinsa ya lalubo ya zuba masa ido yana gannin yadda yake takawa da karfinsa har ya haye ya tarar da su a tsaitsayen nan
Murmushi ya yi bayan ya hau ya shiga mika masu hannu da daidaya har ya zo kan Amir wanda ya amshi hannun nasa shima hankalinsa du ba a jikinsa ba
Takardar dake aljihunsa ya lalubo a nutse ya mikawa Minister , a tausashe ya ce" Da saka hannuna, da rashinsan kunna iya daukan wannan decision din, abinda na sani shine bana ciki ba kuma zan saka ba, ya zama na karshe da za'a saka min ita cikin layina, ku saka ku hau kai sannan ku zartar bani da hurumi a ciki ba kuma zan sgiga TV na yi maganar cewa mun yarda a watsa tsiraici a kasar musulmai ba"
Minister ya amshi takardar yana kallonsa ya ce" Mareshal , ama ka san fuskarka samari suke kallo, shayinka ya sa wasu abubuwan sai dai a yi su a lungu ko?

Idan har mu muka yi haka babu yawunka a ciki ka san da wahala mu iya tsawatar masu ko?"
"Na sani" ya fada yana dubansa
Joe ya ce" Ka sani ama ba zaka saka mana hannu ba?

Ci gaba ne fa , sake wanzar da zaman lafiya ne fa Sir!"
Idannuwansa ya lumshe ya ce" A wajenka ba, ba zan saka hannu ba"
Da alamun zai kawo masa gardama da son sai ya saka shi ya amince ya ce" Ama idan ka yi haka ka fara wasa da aikinka bayan kowa na yabonka, ya dace ka gane muna cikin democratia ne, kowa nada yancin yin abinda ya ga dama, ka sakawa matasa hannu su wala da rayuwarsu kar kace zaka tauye masu hakki"
Ido ya zuba masa na yan sekwani sai kuma ya yi murmushi ya juya a tausashe ya yiwa Minister alamun girmamawa da kuma salama.....

"Mar
chal wannan ai raini ne munna magana ka juya ka barmu a nan a tsaye!" Ya fada da karfi da yannayi na hargitsi ya matso yana son riko hannun Sulaimane wanda ya bada baya zai tafiyarsa, tunda ya gama abinda ya kawo shi
Lebensa ya dantse, rai bace ya juyo ya damki hannun na Joe a hargitse ya murde masa shi har sai da ya zamto Joe ya juya bayanshi na kallon Mareshal gabanshi ya y
i kasa kasa yana zarro ido da karfi yana ambaton sunnan Marchal da tambayar ya sake shi zai karya masa hannu
A zabure mutun biyu suka karaso du sunna sallalami suka shiga kokarin kwatarsa, ama ya ki saki har sai da ya yi niya dan kansa ya hangaza shi da karfin da ya daki daya suka kusan faduwa tare
Abunka da yare ihu yake yi da dukkan karfinsa har ya zamto sojojin dake gidan da wa'inda suka masu rakiya du sula nufo hankali tashe dan a tunaninsu harbinsama aka yi
"Mar
chal me ka yi haka?

Me kennan?

Menene wannan?

Me ya yi maka?" Minister ke fada da karfi har yana cirawa daga tsayen da yake
Da karfi ya ce" Ya isa!, Na ce ya isheku haka!, Dole ne?

Na ce ba zan saka ba bani da yancin kin saka hannun ne?

Idan shi bashi da tunani a kan abinda na kiyawa ni ina da shi, yaya lafiyyar kura balatana ta yi hauka?

A yanzunma da matasan suka san ana rufe suturarma yaya aka kare da su bale an basu hanya?

Kai idan bakwa son a yi maganar adinninma ba laifi mu fuskanci maganar zamanin!
Chapter 29 · 0% Book details