← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 110

Sashe 28

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

A gabansa yana haka dan ya san ya masa laifi, ina a gaban wanda ya halice shi?,
Da yan yatsunsa ya yiwa Amir nunin ya matsa daga kansa ko zai fahimci yarensa dan baya so yana magana shi kuma yana wannan abin kamar ya zauce
Ikon Allah kennan, shi kuma ya iya yaudara, wannan din shine aikinsa
Kai ya girgiza a nutse ya ce" Ina so ka cire du wani raini, karya, kame kame a zamana da kai a nan, dan ina so ka gane kafin mu zauna da mai laifi sai mun binciki waye shi, dan gudun shiga hakin mutun ko?????, Na san wanene kai, babar taka da kake magana a kai yau watanka hudu rabonka da ita, mahaifinka kuwa kunna haduwa a kasuwa in hanya ta hadoka da shi............, Du wannan ba damuwata bane, haka ka zaba da rayuwarka ....gobenka ce!, Abinda nake son sani shine shin zaka nutsu a tsakaninka da kanwata ko zaka ci gaba da aiki da irin taka baiwar har sai ka wulakantar da ita?"
Wannan shine kare kukanka, wannan shi ake kira ya tafi tsai ba kwana kwana abinsa, shi kam daga jiya zuwa yau ya dauko launin masifa kala kala sai fatan Allah ya fitar da shi
Wata rantsuwar ya so dauka, ama ya tare shi ta hanyar yi masa kallo daya tak da ya bambance masa hargagin Kawo naushi da kallon dake iya kisa ta hanyar harare
Kai ya sada, muryarsa a sanyaye ya ce" Tabas ni din kasurgumin dan iska ne da nake yawon biye biyen mata, ama oga na rantse maka ita kam babu abinda na yi mata kuma ba zan taba yi mata ba, a yafe min Oga in sha Allahu daga nan idan na tashi zan ketara na bar kasar baki daya danma ka yarda ba ni ba ita"
Amir ya gyada kai yana auna masa ashar a zuciyarsa
Shi kuma ya koma ya zauna a saman kujera yana kallon agogon bangon office din
Amir ya kalla ya ce" Ka amso masa wata suturar mana ka ga wannan ai ta yi dati ga kuma magariba na matsowa kar sallah ta kama shi a haka, Ma'awiy ai kana sallah ko????...."
Da sauri ya gyada kansa yana fadin" Walahi harda shafa'i da wuturi nake yi Oga"
Kai ya gyada yana fadin" Tana da kyau sosai, ka ringa yi a kan lokaci ka ji?"
Yanzuma amsawa ya yi yana sake risinawa
Amir kam tamkar zai jadiye zuciya dan haushi, Sam bai so aka kore shi ba, so yake yi a yi komai a gabansa, hakan ya sa ya fice da gudu ya sanarwa sakatariyarsa cewa a samowa bakon sutura in ji oga sannan ya dawo a lokacin da Baban gida ke cikin magana, da kula ya ce" Zaka yi mata mana abinda kace baka taba yi mata ba, tunda aurenta zaka yi, ka san ai kana da halin kawo maganar auren nata, kawai ka je ka shirya, duda ban so ace halayanka sun zamto uban
anta ba, ama kai din ta zaba............, Zamu hada ku da addu'ar zaman lafiya, na saka daurin auren kanaina nan da wata daya da kwana goma sha uku, ka je ka shirya da iyayenka a zo neman auren ka ji?"
Kai jama'a, sai ya rasa me yake ciki a irin wannan lokacin, an bincika an san waye shi farin sani ma kuwa kuma ance ya zo ya amshi y'ar, sai yake tunanin ko wani ramin aka haka masa ne?

Shi kam ya yi dana sannin shiga hurumin yan mata, da ya san haka ne da daya tal ta ishe shi rayuwa , yau ya shigo duhun da bai san karshensa ba, gaba daya garinma ya fice masa a rai bale matan, karara yake gannin wannan ya dame Amir ya shanye a iya keta, ama kuma yana masa magana a sanyaye, hankalinsa ya kasa kwonciya walahi
"Na turo magabatana Oga?" Ya fada a sanyaye yana kallonsa
Kai ya gyada yana mikewa ya ce" Ka turo, ka je ka tsaftace jikinka ka samu sallah a kan lokaci, sannan ka daina gannin budurwar nan taka, ka san mata da kishi bana so ita ta zo tana kukan harda budurwa gareka , kwata kwatama kukanta dafi ne a zuciyatahhhhhhh"
Da sauri Amir ya kalle shi, shi kuma ya sake hade fuskarsa ya ce" Idan ta yi kuka Mama ke yi, ni kuma a kan Mama din ne bani da wayo ka ji?"
Ikon mai sama'u sarkin sarakunna, wannan shine shege ga babanka, a hankali kwonce ya gama mamaye zuciyarsa da tsoronsa mai zafin balaki, a irin wannan lokacin idan ya yi wani motsi mai karfi to na godiya ne da nunin cewa ba sai an kawo masa kaya ba zai tafi da kansa gida ya cenza kuma zai fara shirye shiryen tun yau, sannan in sha Allahu ba shi ba kowace mace sai ta aljana sai ko Fatima zahra, a kasan zuciyarsa kuwa shi ya san me ya kitsima wanda ko iyayensa sai dai daga baya sa ji
Da wannan suka fito, yana gaba sai rike wando yake yana zarre ido hamatarsa kuwa rike da kayan da bai san yaya aka yi aka samo su a dan kankanin lokaci ba su kuwa sunna dan bin bayansa har suka fito wajen motocin shi kuma wajen babur dinsa inda Amir yace masa yana nan wajen
Sunna tsaye gaban motar Baban gidan sunna kallonsa ya gurgura mashin dinsa a kafa yana tura mashin din ya fita da gudu gudu yana waigensa har ya bacewa ganninsu sannan Amir ya dubi Baban gida , zuciyarsa fal mamakin abinda ya yi, me kennan?

Yana nufin zai aura mata wannan fajiri alzalumin dan kawai tana sonsa?

A sanyaye ya ce" Yayanmu, wannan din fa bai cencenci auren yar gidanmu ba"
Dan tsai ya yi yana kallonsa, sai kuma ya yi murmushi ya dan dafa kafadar Amir din ya ce" Na sani!

Amir Kai baka da kirki, sirikinka ne ka wulakanta haka?"
Amir ya ja wani numfashi yana kallon yayan nasu, yana son yin magana bakinsa ya yi nauyi a kan hukuncin yayan nasu, ya ce ya sani, ya kuma kirayi shegen da sirikinsa wai, yayama za'a yi haka?

Gaskiya ba zai taba iya bari a yi haka ba, gidansu ba'a ba dan banza y'a ko wacece!

Sai da ya shiga wajen matuki da kansa, sannan ya leko a dan dake ya ce" Sai mun hadu wajen minister kan rigimar bada gudunmuwar sake lalacewar zamaninmu ko?"
Har ya kunna motar ya sake sauke madubin ya ce" Yauwa, ka yi kokari ka sake baza min mota hudu wajen zamansa, ina so harta tsuntsun majalisarsa a sake kamo min, su kwana a hannun maza kar su zauna ko na second daya.............

Kafin na sake zama da shi!"
Ido Amir yake ta zarrowa, abubuwa biyu sun dake shi a lokaci daya
Lalle sai yanzu ya yarda wancen mutumen ya cirowa kansa masifa da kansa,
Sai kuma maganar zuwa kan maganar takardar nan, zai karasa ya yi masa bayani kan maganar ya ga ya ja marfin motar ya rufe sannan ya tayar ya ja ya bar masa wajen
Hankali Tashe Amir ya juya dan zuwa ofishin lieutenant a kan maganar, zasu tafi wajen minister a kan maganar?

To shi dai ba da shi ba, dan walahi bai shirya tarban balaki ba, ba zai je ba, tap lallema so suke yi a darza masifar da karamin ruwa ba zai kasheta ba?

Babu abinda zai kai shi, in su sun haukace shi da tunaninsa, haka kawai a saura dan lokaci ya shige daga ciki su saka a hada shi da jan tsatso bayan dogon gwauroncin da ya buga?

Ba zai yarda da wannan hali na bakin ciki ba sam!
chal kuwa gudu ya falfala da motarsa har ya karasa wajen masalacin gidansa
Sauka ya yi ya shige yana nade hannayen rigarsa dan daura alwallah a lokacin da ake kiran sallah
Dukawar da zai yi a bakin pampo ya........
Chapter 28 · 0% Book details