← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 110

Sashe 81

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka take ayyanawa a ranta ita ka
Babangida dake kallonta yana mamakin kamar ba ita ce ta gama mishi hauka cikin kwana ba yanzu, amma dubeta yanzu cikin wata irin fuskar salihai sai kwarara addu'o'i take duk da ba jin abinda take fa
a ba yake.

Sai dai kuma gaskiya shi bai ma yarda magagin baccinta ne haka ba, don haka ya
ara gyara zamansa murya a taushe sosai tamkar yanayin sanyin safiyar da suke ciki ya ce "Me kika ci jiya?"
A karo na ba adadi ta sake satar kallon
afafun shi cikin taushin murya sosai ta ce "Ina kwana?"
Zuba mata idanu yayi yana jiran ya ji amsar tambayarshi ta biyo bayan gaisuwar, amma sai ya ga bata da alamar hakan, na tsawon minti biyar shi bai sake cewa komai ba ita ma ba ta yi alamun za ta ce wani abun ba, kuma da ta ga shirun ya fara yawa sai ta fara tsorota da hakan, dan gaskiya zamanta a gidan nan a wannan
angaren daga ita sai shi tsorata take a kowane sakan dake shu
ewa.

Da yanayin zafi zafi don ranshi ya
ace ainun na shirun da ta masa ya ce "Ba tambayarki nake ba me kika ci jiya?"
an razane ta
aga kanta amma ba ainahin shi ta kalla ba ta ce "Ai jiya na ci abinci daga gida."
Saida yayi sakan goma yana kallonta sannan ya ta
e baki ya mi
e tsaye ya fara haurawa sama, kamar kuma an dakatar da shi sai ya tsaya ya sake juyowa, ledar da ke aje tun jiya ya nuna mata ya ce "Abun nan dake cikin leda zai iya lalacewa, da bu
atar ki duba shi."
Bai jira ta ce wani abu ba ya sake haurawa ka
an sai kuma ya tsaya kamar dai
azu ya juyo ya ce "Idan kika hau sama,
aki na biyu hannun hagunki, nan ne masaukin ki."
Nan ma ya ci gaba da tafiyarshi, saida ta ji rufowar
aki a sanyaye ta
aga kai ta kalli in da ta ji an rufe ba tare da ta tabbatar wane
akin ya shiga ba, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke, *masaukinta*?

Kamar wata ba
uwar da za ta tafi gobe?

Ko da yake duk
aya wai makafi sun yi dare.

Mi
ewa tayi gadan gadna ta fara haurawa don sai ta fara kimtsa kan ta kafin za ta iya shiga wata aba wai madafa.

Hawanta saman ke da wuya ta
idaya
aki na
aya zuwa na biyu, sai dai a
angaren dama ne madadin hagu da ya ce mata, ba wai ta yi da gangan bane, ita a lissafinta bata bambamce hagu da dama ne a sau
r har sai ta daidaita hannayenta sannan take iya ganewa, dan haka ta banka kai
akin da ba nata ba...

Cakkkkk!

Ta zabura ta tsaya gaba
aya kayan cikinta ta ji suna neman zazzagowa, tsabar firgici da tashin hankalin da ya risketa ne ya sakata
urma ihun da ta rasa da ma wanr yare ne ta sakota, amma dai tafi zaton da larabci ne ko zallar indianci dan sun fi kama.

La'ilaha illalahu Muhammad rasulillah sallalahu alaihi wa sallam!

Tsaye take fa gaban Babangida, ba tsayuwar gabansa ba ce abar dubawa, kayan da ta samu a jikinsa, Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!

Wallahi kwance ta same shi yana gym wanda ma fi aksari yana yin hakane kafin ya shiga wanka.

Shi kan shi rashin tsammanin mutum a wannan lokacin ya sa shi zabura har ya
ago da mugun sauri don gnanin wanda ya shigo.

Bai gama tamtamce me ya faru ba ya ji wannan ihun, sai kuma fuskarta da zai iya cewa ya
an hango da matu
ar tsoro fal a fuskar, sai kuma ta juya da gudun tsiya ta bar
akin ba tarz da ta rufe masa
akin ba
Sai da ya ga fitarta ne sannan ya
an sassauta kallon da yake ma
ofar kafin ya kalli kanshi, shi ne dai da kan shi ba wani ba ta gani, sai dai a kidayar kwakwaluwarsa a kusa kusan nan ko marigayiya bata cika ganninsa a haka ba daga shi sai boxer dan mitsil har sama, cinyoyinsa a bayane hakama kirjinsa, sannan wannan yannayi yakan saki jikinsa ya motsa jikinsa sosai ne...

Hannunsa ya saka yana dafe gaban goshinsa, kai, yau ya shiga uku, jiya jiyan nan a kawo yarinyar nan ya fi a irga da ta saka shi jin wani makokon malolo ya tsaye masa a wuyansa na takaici da tarin jin haushi, yanzu me ta zo yi dakinsa ba kwankwasawa ba salama kanta tsaye tana wani jan hijabi ta tatare ta dame shi a kugunta kaffafuwanta a waje wando ya tsangale kamar zata taka wuta?

Lalle ya shiga uku dole zai maida hankali ya gyara mata bangare guda ya zamto idan sun hadu dan ta bashi abinci ne ta yi tafiyarta ba sai ta cakula masa lisafin kai ba a banza a wofi!

Zahra ta fitowa ta juya ta shiga irgawa da hannunsa, gabas, yama, daya biyu....., Da sauri ta nufi dayan bangaren ta kama ta ringa salama a bayane tana fadin" Zan shigo, asalamu alaikum zan shigo" domin idannuwanta da zuciyarta sai suke fada mata idan ta afka lalle zata hadu da shi a irin na cen, hankalinta ya kasa kwonciya har sai da ta gama bin dakin da kallo ta yarda baya nan sannan ta karasa da sauri ta zauna bakin gadon tana cire hijabinta ta ringa murzar kanta tana ta astagafari tana neman Yafiyar Allah da tsari daga shi dan kuwa wannan abu da ta gani yau ya fara neman taba lafiyarta ta yarinya karama saliha wace ta rayu nesa da irin haka, in bandama a novel da take ji namiji na zama ba riga ta yiwu yau da ta summa numfashinta ya fita daga jikinta gaba daya ..... innalilahi yanzu yayansu ina ya kai kayansa ya zauna haka a dakinsa?

Da kyar ta iya mikewa dan wankan shi ta fi bukatar yi ta nufi bayi tana ta faman addu'a, ta san ba zata iya cire wannan gani nata ba, duda babu abinda ta ganin kawai rashin rigar ne ta gani, ama kuma ta san hakan ba karamin tashin hankali bane wa idannuwanta......

Wanka ta yi a bayin da shima ya matukar kayatar da ita, ta bude sabon bruch cikin bruch din dake ajiye ta yi brchng bayan ta wanke shi da ruwan dumi sannan ta dauro tawul ta fito tana sauke ajiyar zuciya rike da kayan datinta ta ajiye saman kukerar karfe tana ayanna da an jima zata kai a saka mata a washing machine na wajen Mamanta
Bude wajen tufafi ta yi, tana ta raya anyama an kawo mata sutura?

Dan aunty Luna tace za'a kawo yau, tarin kayan da akace nata ne ita din nan mai son yawan zama da dogayen rigunna na shan iska ai kayan nan ta yiwu har ta mutu bata saka wasu ba ko su yi mata kadan ko a wuce yayinsu, dan kuwa har sai da ta tsorata da ta ga saitin akwatunnanta wai lefenta ne
Ido ta dan waro, sai kuma ta saki murmushi,
Kaya kam an kawo sai dai kannanu ne na shan iska ne gasunnan Masha Allah
Daya ta janyo riga mai ruwan orange tana kallonta da aunata a jikinta
Kadewa ta yi ta saka dan rigar tafe take da gidan mama ba sai ta saka matarin dugwui dugwui ba, ta dan juya ta kara juyawa sannan ta dauki turare bonbon ta fesa sosai tana jin kanshinsa har cikin ramta, fesawa irin tata wace aka hannata a da, yau sai da ta yiwa turare fesawa ta balaki dan kuwa sai da ya yi mata baja baja a jikinta sannan ta fito daga wajen turaran ta karasa bakin gadon da yake nata ta sake zaunawa tana murmushi ta dora kafarta daya kan daya hakan ya sa tsagar jikin rigar ta bayanar da cinyarta sharrrrr ita kuma ta yi kwonce tana kallon clng lokaci guda kuma ta auka duniyar tunanine ya dace ta fuskanta dan gyaran rayuwarta?

Karfe takwas ta gota sosai ya fito ya sauka dorect ya nufi wajen diner, sai dai yana zuwa abinda ya tarar ya saka shi dan sake zubawa wajen ido, watau wayam babu abinci,
A hankali ya nufi wajen kicin din yana dan saurarawa, sai dai alamu sun nuna masa ba mutun a kicin din, da wahalama in mutun ya shiga kicin din daga jiya zuwa yau
Fitowa ya yi yana dan sake bala botr din hannun farar rigarsa yana waige waige a falon har zuwa inda ledar kajin nan suke
Wani duba na haushi ya zuba masu yana tunanin su din ne dai a nan din, kai innalilahi yanzu shi aka gama da wannan yawan maganar?

Daya daga cikin gudun auren yarinya kennan, ta sani sarai ga abinda ya dace ta yi, ta kuma san abinda bai dace ba, ama zata yi jira sai ance ta yi, idan akace din ta yinma sai kuma ta koma ta ki yi dan kawai ka zamto aku a cikin gidanka, ka zama mai aiki kala biyu kennan, ka yi a waje ka yi a cikin gida
Taka matakalar yake da dan sauri dan zuwa ya sanar mata yinwa yake ji fa, aiki zai tafi, bai saba fita haka bai karya ba, kwata kwatama shi cikinsa ne baya son wasa da shi dan yana saurin sakashi juwa idan ya yi wasa da shi, baya son da yinwa , horon dake jigatashi kennan a rayuwa zama da yinwa, shi baya fushi da abinci, kuma ko bashi da lafiya baya kin abinci
Kofar ya kama ya murda ya shiga da salamarsa
Sai dai santala santalam cinyoyin dake maiko a fili farare kal kal din nan ne suka saka shi dakatar da maganar hankalinsa na neman tashi ya ringa binta da kallo a lokacin da ta nufi wajen tufafinta ta bude ta ringa cakulawa tana neman hijabi har ta samu wajen hijaban ta janyo daya ta bude jikinta na rawa ta zumbula shi a baibai sannan ta juyo ta wani tsareshi da ido shi?

Shi ?

Rai bace ya nunata da yatsarsa ya ce" Kin ga ki kiyayeni , ke baki da aiki sai zama ba sutura a jikinki?

Menene wannan banzar dabi'ar?
Chapter 81 · 0% Book details