Sashe 108
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita dai dama ba mutun bace mai tsoro Allah yana gani, bata da irin tsoron nan na kar ace ko kar a zageta, itafa ko zamanta da matan Docter su maman Abul bata taba jin tsoron ko daya ba, tana yawan kawar da kai a rayuwa ta yau da gobe ne dan ya roketa wannan Alfarmar ta kuma yi masa dan ya isa ta yi masan, ama ba wai dan tana tsoron daya ba, Mama kuwa tunda ta ja yarinyarta a jiki ta mayar da ita tata ta yi waje ta ajiyeta a waje mai daraja a zuciyarta, ya zamto ko Mama ta koreta zata koma ne ta likun mata dan ta riga ta yarda cewa bata da wajen zama ta ji dadi sai gefen Mama, bata da familly sama da ahalin Mama ba kuma za'a taba cutar da ita a gefen Maman ba
Sosai Mama ta sake bata lokaci a wajen Aunty amarya kafin ta biyota da suturarta da zata saka goben dan safiya zasu yi dan tafia Adu'ar arba'in din Malan, haka kuma kafin Mama ta kwonta sai da ta tabo Babangida duda dare ya yi ta sanar masa yadda suka yi, shi dinma bai yi kasa da gwuiwa ba ya shiga whatsup ya bar sakon sin ganawa da mutumen mai mutunci sannan ya koma jikin matarsa da ta samu barci ya ci gaba da shafata a hankali shima yana neman barcin
Washe gari kusan karfe tara na safe tuni mutanen da suke baki na nesa da na kusa sun wawatse daga gidan marigayi sai daidaikun da suka rage da ahalinsa da kuma SHEIKH wanda ya tara su yake masu nasiha da nuna masu zuwa yanzu gida ya zama a ragamar hannunsu, su yi kokari su rike zumunci su kuma kawar da kai a kan harkar dukiya sannan su taimaki junna domin babu abinda ya kai zumunci nauyi, ama kuma babu abinda ya kai shi dadi domin yau koda bashi da lada ka kwana da sanin kana da wani mai kaunarka mai jiranka mai iya bayar da rayuwarsa dominka mai iya yi maka fada dan ka gyara gobenka, mai kai sunnanka wajen Allah ya nema maka afuwa da aljanna, babu abinda ya kaishi dadi bale duk bawan da ya yanke zumunci ba zai shiga aljana ba...., Haka dai ya jima sannan ya fito tare da jama'arsa kafin ya dakata yana sauraron mai yi masa bayanin aiyukan ranar, da kuma tuna masa bukatar MARSHAL
A tausashe ya bada damar a tabo masa MARSHAL din dan tunda gasu a anguwarsu ai ba sai ya saka shi wahalar tarda shi wajen aiki ko gida ba
MARSHAL dinma da yake a kusa yake yana jiran a tabo shin, domin tun bayan sallar asubahi ya samu amanar sa gana da sheik din , sai ya yi zamansa a kusa tare da matasan anguwar yana shan dariyarsa yana binsu da kallo dan Sale tsakaninsa da Allah yace yana so a zauna a masu nasiha, yanzu anguwar sai rasa tsofafi masu yi masu addu'a ake yi gashi sunna sake shiriricewa sai oga bos dake gefe wanda sun sani idan har ka yi sake ka kai babarka makura ta kawoka gabansa zai maka fila fila ne ya zaneka kafin ya kaika gidan maza ko dawan makaranta, dan yanzu dai samari uku hakan ta samu gaskiya basa fata a ci gaba da tafia a haka, gwara a samu a sasanta a san menene damuwar a kuma yi maganinta dan zaman lafia ai ya fi zama dan sarki
Mikewa ya yi daga saman kujerar bayan ya samu kiran har ya nemi alfarmar idan da hali su karaso gidansu sannan ya sanarwa samarin anguwar cewa gidan maza kam yanzu ya fara kai du wanda ya yi wasa da karatunsa ya nemi aurar jagaliyancu a matsayin rayuwar da zai yi a gaban iyayensa yana hada masu gurmi da tashin hankali kala daban daban dan an haife shi, maimakun ya zamo wanda ya san ciwon kansa ya nemi na kansa ko bai ciyar da su ba a kala ya dauke masu bakinsa ya raba su da rayuwa irin ta yan kwalta ai da kyau, kawai su sasanta junna a ganewa junna a girmama manya a kuma yi takaici a nemi na kai, babu wa'inda zasu ji dadinsa irinsu......da wannan ya bar maza ana shawarar mafitar rayuwa dan kuwa sun yarda cewa maganarsa iya gaskiyarsa ya fada masu, gwara su san hanyar rikewa dan kuwa sun sani ne idan suka bijire din zai nanagi kan shege ne a gaban babarsa!
Da ladabi sosai ya dan sake rage tsayinsa a gefen motar a tausashe ya ce" Ka yi hakuri Allah ya karra maka lafiya, ka sauko mu shiga daga ciki dan maganar mai mahimmanci ce sosai"
Hankalinsa ne ya dan karra tashi, ya sani ba maganar cutar da shi a wannan gida, ama kuma maganar ya ratsa ya je har dakin uwar gidan docter ne yake ji wani iri, domin tunda yake ko balbalin gidan nan bai taba saka kafarsa ba, sai dai su hadu a makaranta ko masalaci su dauki karatu wajen Docter
Dan sauke ajiyar zuciya ya yi cike da zulumin kar dai bata da lafiya ne ko wani ne ba lafiyan da ake bukatar taimakonsa?
Bai yi gardama ba ya sauko din a nutse ya shiga bin bayansa, sai dai biyowar jama'arsa ta saka MARSHAL dakatawa yana binsu da kallo
Har ga Allah mutanen da yawa gasu darza darza gashi a falon cen Mama ta shaida masa bayan matan mutane tasama tana nan tare da su, hakan ya saka shi a hankali sosai ya dan rage tsayinsa domin wannan bawan Allah yana da kwarjini da kuma haske irin na addini ga shekaru da yake da su ba laifi sai yake ji ba zai iya yi masa magana kai tsaye kamar sa'ansa ba a tausashe ya ce" Allah gafarta Malan, dangane da NANA ne, da da hali su dakata a nan mu shige"
A zabure SHEIKH ya zuba masa ido yana sakin carbin hannunsa, sai kuma ya duka da sauri yana raruma ya kuma dagowa ya zubawa fuskr MARSHAL ido....., Tunda yake neman gudan jinninsa ba'a taba yi masa magana kai tsaye haka da ta shige zuciyarsa irin haka ba, an sha ace an ganta a waje kaza wanda ya ganta yana bukatar kudi adadin kaza ko zai nunata, kai ya kare magana harta yan fashi sun ci makudan kudi a hannunsa domin sun nuna ga yarsa a wajensu ya biya kudaden ko su kashe har yar har uwar da sharadin idan har polise ya shiga ba zai gansu ba ko gawarsu ba zai gani ba, shi kuwa ya dauki kudade ya kai wanda jin shirunsu har sai da aka fitar da shi waje dan faduwar da ya yi sakamakon hawan jini da tunanin an kashe masa gudan jinninsa da matarsa ne?...., A hankali ya jimke hannun MARSHAL yana kallonsa hawaye na cika idannuwansa ya ce" NANA?, NANA TAWA?
NANA Y'ATA?"
MARSHAL ya sakar masa tatausan murmushi dan ya kwontar masa da hankali kafin ya yi alamun a hanna jama'arsa shiga ya ja shi iya shi a hankali suka karasa falon na Mama
Ba tsaye tsaye ya idasa shiga jikinsa na rawa hakama idannuwansa yana ta baza dubansa a kan kowa a lokacin da suka ringa silalewa ya rage Mama da Aunty amarya ne sai ZAHRAh da Mama ta hanna tashi
Mama dai ya santa, Zahrah kuwa ya san a shekarun Nanansa da wahala ta tsaya a yar karama haka, sai kawai da sauri ya zuba idannuwansa cikin na wace ke tsaye idannuwanta a saman fuskarsa, idannuwan nata sun cika da hawaye sosai haka kuma jikinta na dan rawa tana ta hade hannayenta sannan tana saki
A zabure MARSHAL ya shiga kafadunsa sakamakon neman zubewa da ya yi kafafuwansa suka nemi maka shi da kasa lokaci daya yana dan nunota da yatsarsa muryarsa a rikice ya ce" NANATA?
UMANI?"
da saurin da bata shirya masa ba ta daga kaffarta ta karasa itama ta damki hannun mahaifinta suka karasashi saman kujera shi kuwa bakinsa na sake kama sunnanta ya saka hannayensa bibiyu ya rikota sosai ya janyota sosai yana ta shafa fuskarta yana duba hannayenta hawaye na tsiyayar masa ya ce" Nanata?
Kece?
Kamanin nan naki har sun bace da ni, kece Nanata?"
Kuka ta fashe da shi a hankali ta dora kanta saman cinyarsa muryarta na fita da dan kArfi ta ce" ABAH, Abahnah, papah"
Gaba daya yannayin da datijon ya nuna ya kara karya zuciyar Mama ta ringa share hawaye tana kallon ikon Allah, soyaya bayananiya, soyaya mai karfi, soyaya mai daraja, yana hawaye yana ta mata tambayoyin ina ta je ina suka tafi suka barshi ina Mamanta ina menene menene , yaushe ta zo nan, ta kuwa san irin neman da ya mata?
Ta kuwa san irin halin da ya shiga da basa nan, ta kuwa san irin yadda rayuwarsa ta dawo babu wani kwonciyar hankali saboda bai san sun mutu bane ko sunna raye?
Ina mahaifiyarta ne wai, a rashin mamanta mata uku ya aura ama har yanzu babu wace ta haihun masa, shi ya san abinda ya mata ne ya sa Allah ya kama shi ya zamto y'ar da ka haifa masa wace take kasar waje da ahalinta babu ruwanta da shi tana cen tana rayuwarta da jar fatan saurayinta da
ansu uku dan ko aure basu yi ba sai Nanarsa wace ita kuma ta bace masa a duniyar baki daya bai kuma koda samun bari ne a tare da matansa ba haka yake zaune daga su ya ki kara wani auren dan ai shi dai bai saki matarsa ba, wai dan Allah tana ina????.....
A nan ne Marshal ya yi iya yinsa ya samu suka sasauta suka yi hakuri har suka yarda zasu saurari junna da kuma hakuri da dukkan abinda zai shi kunnayen junna...wanda aka fara sheda masa dai matarsa Allah ya mata cikawa, ta rasu, hakan ua saka shi kuka tamkar yaro karami, domin kuka ya yi sosai lamar yanzu ne ta rasu a gabansa, fadi yake yi ta tafi bata yafe masa ba?