← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 110

Sashe 93

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ina bin bayanta sai ta saka na dawo, haba nima fa zuwana biyu fa muna zaunawa da ita, yaushema aka tafi har zata wani dagawa kanta hankali, kuma nima sai da nace na yankar masu su tafi mana tunda akoy wajen zama da abubuwan bukata ta nuna ita kawai inda aunty take ne ba zata je ba, gwara ta sanyaya kanta dan inma bata sani ba ta sani mijinta a kan Aunty tsaf sai ya manta da ita, tana da dama sai wasa take son yiwa mutane, kyaleta ta ga in tana iya zama ta neme mu da kanta"
Aban Ahmad da kwarin gwuiwa ya ce" Yauwa, nima haka nace in ta ga dama ta yi tunani a kai sai a zauna a yi magana, tun banma nuna mata komai ba tana neman rikita min lisafi ina dalilin wani abin, ka ga yanzu ka fada min me zan saka, kuma idan na je tsugunawa zan yi im bata hakuri?"
MARSHAL ya wani gyara zamansa yana kada kafa ya ce" Ba inda zaka tsuguna, sak zaka dubeta ta dubeka, hakurinma an ki ba'a badawa ba mun bata hakurin ba?

Ko bamu bata ba?"
Aban Ahmad ya yi tsai yana sauraro, cen ya ce" Kai ko dai ramawar da kace zaka yi ne kake son yi?, To kace maman Ahmad a yi banza da ita, kuma itama maman ZAHRAN ?, Ko na maka wani laifi ne da safiyar nan?"
MARSHAL ya yi murmushi zai yi magana ZAHRA ta bude ta fito daga bayi, hakan ya sa ya rage murya sosai ya ce" Freind, zan yi kiranka, ka je ka shirya ka tafi, idan ka shiga kar ka ce zaka dagawa kanka hankali, ka fuskanceta kawai ku yi magana, in sha Allah zai je daidai"
Tun kafin ya bashi amsa ya katse kiran ya ajiye yana mika hannunsa ya janyota gabansa ta tsaya kanta a kasa tana wasa da yan yatsunta
A hankali ya ce" Yaya jikinki?"
Kai ta sake sinewa ta kasa bashi amsa, ita gaishe shi ta yi ya ki amsawa yana tambayarta jikinta, ita kam me zata ce masa ne da maganar yaya jikinta?

Murmushi ya yi ya gyara mata hijab din da kyau, a hankali ya ce" Bara na je na yi sallar nima, me zaki ci?"
Nanma shirun ta yi, bayan cikinta dake ta faman yi mata kidan yinwa
Kanta a kasa har ya fita a dakin, sai a lokacin ta dago kan nata da kyar ta karasa saman darduma ta zauna ta tada sallah sai matse ido take yi, ita kadai ta san irin zafin da take ji a jikinta , fatanta Allah ya sa ya yi sauki ,
Da kyar ta karasa sallar ta ja carbinta sosai sannan ta tashi da kyar ta ringa takawa ta sauko kasa
Tana saukowa ta hangi fitarsa a falon, sai ta rasa tsayawa zata yi ko aikin zata kamanta?

Tana gwada dukawa sai mikewa ta yi jiki ba karfi ta zauna ta dan karkace tana matsar kwallah ......................
____________________________________
Mama dake ta faman gyara yankan fruits din da Auta ta yi ne ta dan dago ta sake kallonsa sau daya sannan ta sake dauke kanta ta ci gaba da gyarawa, tunda ya zo ya gaisheta yake binta da kallo ya ki ya yi magana sai dai kallonta da yake yi riiiii nan, riiiii cen
Baki ta sake tabewa ta ki tanka shi, ta tabata in dai maganar da ya zo da ita na damunsa zai maganta da kansa ne
Auta ce ta dawo, mamanta ta ce ta kwashe fruits din ta kai frij
A hankali ya ce" Mamah, a debama ZAHRA, ta yiwu idan ta ci ta dan ji sauki......"
Mamah ta dago ta kafe shi da ido, ta ce" Baba wai zazabi ne ke damunta ko menene?, Ni tun jiya nake bin kanka sai kace min da sauki, gashi ban ga yarinya ba, kuma ban san yaya take ba, ZAHRA fa bata da hakurin ciwo a kawo min ita nan in ba dama in kaita asibiti gaskiya"
A hankali ya dan ringa sosa keyarsa, kansa a sade , ya shiga dan inda inda ya ce" Mamah, da saukinma ba laifi, jikin ne dai da dan wahala, kuma da saukinma dai zan ce"
Idannuwa MAMAH tke budewa a kansa, ya salam madaukakin mamaki da tsoro na darsun mata, wayo Allahna yar amanarta yar tamumuwar y'arta,
Da sauri ta dan mike ta dauki hijabinta ta zumbula sannan ta dauki fruits din tana kallon Auta ta ce" Ki je ki ce da Habi a hada abinci ki kawo bangaren yayanku ina zuwa"
Bata kuma bi ta kansa ba bayan ya mike yana kallonta da son karin bayani ta yi gaba, ina ba zata iya ba, kar aje an farke mata ya, innalilahi wayo Allah zahranta, ba tare da ra kula shi ba ta fice ta kama hanya da niyar nufar bangaren suka hade da maman Furera da ta taho da nufin son gannin Babangidan
Da kula take tambayar Maman ina zuwa haka?

Ai kam Mama ta ce" Zan je wajen Zahra ne bata da lafiya na ga jikin"
Da mamaki ta ce" Lah kuma da kanki Mamah du gamu?

Ki koma kawai ni na je, kuma ga yayansu na sanma ai zai kira mata likita, ciwon kan nata ne ko?"
Mamah ta girgiza kai ta ce" Aa, mu je dai tare da ke din, idan za'a fita asibiti sai ku tafi kawai"
Bin nasun kuwa ta yi, dan tana son shiga dinma da kuma son gannin kwaf , ciwo?

Ciwo ko karya har wani ciwoma take yi?

Hummmm!

Tunda suka shigo falon take kokarin mikewa
Da dan sauri MAMAH ta karasa ta zauna tana riketa, a hankali ta karkato ta dora kanta saman cinyar maman a sanyaye ta saki hawayen dake cikin idannuwanta tana lumshe ido, wanda hakan ya saka shi zubawa fuskar nata ido wani irin fargaba na neman ziyartarsa
Kiran da ya shigo masa waya daga wajen aiki ya saka shi fita dan amsawa
A hankali MAMAH ta ce" Zahrana, yaya jikinki?"
Da kyar Zahra ta iya amsa MAMAH a hankali tana dan rike maganar dan bata so Maman ta gane abinda aka yi kennan har ta ji rauni
MAMAH ta kalli Maman Furera da ta zubawa Zahra ido, ita bata zauna ba, ita bata yi mata ya jiki ba,
Da kula ta ce" Maman FURERA ko zaki taimaka min da relief a bangarenki?

Ni bani da shi ta sha na gani , ni tsorona kar aje ta karu"
Da gaya MAMAH ta yi maganar, dan Maman Furerar ta fahimci ainahin da gaske maganar da ake yi kennan, du kuwa da irin yadda kunya ta hanna y'ar tata motsin kirki sai langewa take yi a jikinta, ama a haka ita ta yi watsi da kunyar dan ta sani idan bata kula ba, babu mai kular mata, yayantama da aka kai sun samu kulawa daga Aunty Lubabatu ne, yanzu kuwa da Lubar bata nan bata da mai kular mata, ita zata kula da y'arta daidai gwargwadon iyawarta
Ai kam ta fahimtar, har ta ji tamkar zuciyarta zata daina aiki ne na wucin gadi, kallon Maman take yi tamkar idannuwanta zasu fito su ballo daga gurbinsu su fado kasa nan da nan idannuwanta suka rufe, ko ufan bata iya furtawa ba ta juya ta bar dakin tana jin wani kuka mai daci na tukota da wata irin juwa
Mamah ta yi murmushi tana dauke kanta daga inda Maman furera ta fita a ranta tana ayana'kema kika iya salo salo na wulakanci bale ni da na tsofe ki a duniya ?, Ana kawar da kai ne dan kunya, tunda baki santa ba ni ba zaki hanna ni aikin lada ba da kuma kula da ahalina ba!'
A bayane kuwa, a tausashe tana dan son dago da y'ar tata, ama ita kuwa sai sake sine kai take yi kirjinta na dokawa, Maman ta ce" Kin kuwa yi anfani da ruwan zafi?"
ZAHRA ta sake lumshe idannuwanta ta gaza cewa komai,shin ina zata kai kayan kunyar nan?

Idan ta yi tsai tana tunanin irin abinda ta gani dangane da tafiyar nan bakinta ba zai furta komai ba sai addu'a da fatiha, to ita abin kamar wace ta sha kayan maye?

Har yanzu ta gaza yarda wai itace ta dauki hannunta tana kallon idannuwan yayanta tamkar ya sha yaji, bakinsa ya kara daukan ja, yana ta hucin tarin jaraba ta cire wandonta?

Kai innalilahi ina zata kai kayan kunyar nan?

Yaya za'a yi ita ZAHRAH ta iya dubbansa?, Babu ko dan jan ajin nan na amare ta mika wuya?

Lalle itama ta yarda ta yiwu wNi abin take sha ko?

To ama me?

Banda maganin wankin ciki na wajen aunty da take sakawa ta sha bata shan komai, lalle zata zagine ta daure tsatso ta fito filin da ake kiran mata mata ba muna mata ba, dole zata koyi menene jan ajin nan duda mutumen nan na gudu a cikin jinnin jikinta, kasa cewa Mama komai ta yi, sai dai wata kwallah da ta sake dauro mata a gurbin idannuwanta hakan ya sa Mamah sake yin murmushi ta ce" To tashi mu tafiyarmu cen na kula da ke tashi maza "
Tana kokarin jan hijabinta dan ta rufe da kyau dan ta samu ta tashin ya dawo da wayar a hannunsa ya zauna saman kujera yayansu ba ko kunyar MAMAH ya dan zubawa Maman ido yana sauraron tana sake maimaita kalmar Tashi yi a hankali .......

Idannuwansa ya dora kan Zahra, wace ta samu ta mike tsayen tana lumshe idannuwanta dan shanye radadin dake dan taso mata
Mama ta dube shi tana sake dauke kanta ta ce" Zamu je cen bangarena Babangida "
Har ga Allah sai da ya ji wani irin abu a cen kasan zuciyarsa mai dan kama da damuwa, yana duban Maman da kula ya ce" Mamah, me yasa?"
Mamah ta juyo da dan sauri ta kalle shi, haka itama ZAHRAN sai ta samu kanta da dan satar kallonsa duda nauyin da hakan ke mata
Mamah ta ce" Kamar yaya me yasa?
Chapter 93 · 0% Book details