← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 110

Sashe 51

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ban ce wai na san mutuwata ba dan babu bawan da ya san gaibu, sharar fage nake yi idan ta kasance da ni ba zan tafi da magangannun da nake son sanar maka ba ko?........., babana ka yi hakuri dan Allah ka saurareni, ka bani damata ka ji?,"
A dole ya yi shiru da son katse ABAH, shi kuma ya dora da fadin" Gida dai iyalina sun san naka ne, na ki ka saka sunnana dan malakinka ne, zufarka ce, karshe dai sai da ka saka da Hajaju ikon Allah kai dole dai gida na danginka ne, ba laifi hakanma alkhairi ne, ka ga kuwa hakan zai min dadi sosai, domin bana so nan da nan wata ta fitar min da Y'ayana, idan har na rasu daya a cikinsu ta gaza zama har ta samu wani mijin ko ta rike
anta Babana ka salameta sannan ka talafa mata da abinda Allah ya hore maka, amma ta bara min yarana a hannun Hajiata, na tabata zata rike min da zuciya daya amma dole a karo yan aiki saboda kar su sakata yawan magana ko Baba?, Maganar zama a dakina kuwa ka zauna ka kare, ai baka da wajen zaman da ya wuce nan, a nan zaka zauna kai da iyalinka , idan kuwa ka fi so iyalin naka su zauna a wani wajen ba a dakin nawa ba to sai ka tambaya maganar gidan makocina Aliyu da yake son rabawa ya siyar da rabi ka siya ka bude garun a yiwa iyalinka bangarenta ka fahimta?

In ba wannan ba ni kam zan iya cewa umarnina a gareka ku yi zamanku a bangaren nawa, a hankali idan ka hayayafa ka ga sai a san na yi, na tabata zuwa lokacin ai an aurar da yan matana an dan samu ragowar firgicin zuciyar ko Babana?"
Shi kam bai bashi amsa ba, Mamah ce dake dan share idannuwanta ta iya dan gyada masa kai, duba da a vip suke zaune kujeru wadatatu ne ya saka suka zauna kusa suke tataunawar
Abah ya yi murmushi aka ci gaba da kama sunnayen ya'yansa, du wanda aka kama sunnansa na dakin Mamah sai ya fadi halinsa ya kuma yi nasiha sannan ya saka albarka, hakan ya saka yaran sake tsumuwa hawaye wani na korar wani har Mama ta kusan zuwa kan Auta sai ta ce FATIMA ZAHRAH
Aba ya kalleta ya kama baki ya saka yar dariya ya ce" Kwace dai ya tabata, ke Hajiar docter kin iya rigima ki yi sama da fadi da d'a sukutum?,"
Mamanma a dole ta yi murmushi ta ce" Ba kwace na yi ba, dama tawa ce ai Docter"
ABAH ya yi murmushi ya ce" Kwarai kuwa taki ce, duniya da kiyama, nima tawa ce yar yata yar albarka, Zuwai kin kuwa san na so ace daurin auren nan da y'ar nan?

Kai fa na yi farin cikin hakan, sai dai kashhhh da wahala inaga duda na yi ta tunani har kamar kaina zai fashe a cikin ya'yan nan nawa maza wa zan ba wanda zai rike min da zuciya daya ya ririta min ya guji aikata sabo irin na wasu mararsa ilimin da suke yi, ya fuskanta ya bada daraja ya so?, Du sai tunanina ya ringa tarewa a kan Babangida
A zabure kusan du wani mai sauraro ya dago ya zuba idannuwansa a kan Babangidan da kuma Zahra da murmushin kan fuskarta ya dauke lokaci daya ta yi kamar zata summa , kamar zata tafka a dubun lamba dan idannuwan da suka yi mata riiiiiii a kai, shi kuwa idannuwansa kawai ya lums
he ya yi tamkar baya wajen a lokacin ne kuma aka sake saka masa wani daukan dan wancen ya katse ya ci gaba da maganarsa hankali kwance ya ce"
30000000000000000000000000
A zabure kusan du wani mai sauraro ya dago ya zuba idannuwansa a kan Baban gidan, da kuma Zahra da murmushin kan fuskarta ya dauke lokaci daya ta yi kamar zata summa , kamar zata tafka a dubun lamba dan idannuwan da suka yi mata riiiiiii a kai, shi kuwa idannuwansa kawai ya lumshe ya yi tamkar baya wajen a lokacin ne kuma aka sake saka masa wani daukan dan wancen ya katse ya ci gaba da maganarsa hankali kwonce ya ce" Uhum, wani lokacin idan ya tsareni da ido kamar mai hararena kamar kuma mai son fada min wani zance a hakan, Allah dai ya kare maza, kina ji Zuwai na yi tunanin Amir, na zo na yi a kan Abdul Baki, na yi a kan Fahad, na yi a kan Usmanu,ke dai na karkare maki zance har kan Huzaifa nawa na yi, ama maganar sai ta fi dawo min kan Babana,.............."
Kit maganar ta dauke sanadiyar daneta da ya yi ya bude jajayen idannuwansa ya sauke a kan fuskar Mama dake fadin ya sakar mata magana ta karasa fita
A hankali ya ce" Mama ba sun ji abinda ya dace su ji ba?"
Mama ta daure fuska ta ce" Kai ka sakar min magana ka ji?

Abinda ya dace su jin me, ka bari su gama ji dan mai dauka ya dauka, wanda baya dauka kuma na sani tun yanzu"
Maman Furera da take ji har kamar ciwon hawan jini zai harbeta muryarta a hargitse ta ce" Babangida ka yiwa Allah ka sakar mana mu ji maganar zafin ciwon da Docter ya yi, dan kuwa idan har ya saki ya yi umarni a kan wannan maganar ina mai tabatar maka zafin ciwo ne ya saka shi aikata haka ba komai ba!"
Da mamaki Mama ta kalleta ta ce" Me kike nufi?"
Maman Furera ta juyar da kanta tana girgizawa ta ce" Haba Mama, haba dai, har an min tambayar me nake nufi bayan an san waye Baban gida?

Ai kam zamu jajirce mu ringa tsayuwar dare kan ALLAH ya bashi mace ta gari kawai....ba wai mu zuba ido mu hadu da hawan jinni ba....hada jinima da abinda ba shikenan ba ai ba wani armashi!"
Ido kawai Aunty Amarya ta zubawa Maman Furera....., For the first time da aka dauko maganar da ta shafi wancen yarinyar ta ji maganar har a cikin zuciyarta, ido ta zuba mata da kallo irin na kurular nan da son gane me take nufi....ko kuma son karantar wani abu ne?

Allahu a'alamu, ....a hankali ta sake sauke duban nata a kan Mama, irin kallon da ta ga Maman na yiwa Maman Furera ya sakata mayar da idannuwanta ruf ta rufe tana dane zuciyarta da wani bakon yannayi dake son bijiro mata, yannayin da a da ta san tana da shi, watau yin fito na fito ne ko taka mai takata ne?

Ita dai abin mintsininta yake yi a yanzu har take jin kamar zata budi baki ta yi magana dan an ce haka da wancen yar!

MARSHAL kuwa, wani irin daci ke ziyartar harshensa na mabambantan halayan iyayen nasa, ya zama wajibi fa ya fuskance su ya dan nuna masu cewar yana iya gwada hali na marar jin magana koma yace kamar dai halaya na yan iska ta hanyar kirta abinda ba zai saka su farfado da wuri ba a kan maganar da ya yi a tsaye ya yi a zaune kan ita wancen yarinyar!, Wai wannan waxe irin masifa ce?

Shikenan dan an haifeka ta wannan hanyar sai a sakoka a gaba a fitineka a hanna maka wali?

Wai ina ilin al'uma ne?, Ina iliminsu ne?.......ko ita ta yi yin farko an kire shi da uzuri, na biyu zuwa sama ne ganganci, idan kuwa an tsago hakan zaka tara ya'yan akoy wanda zai hanna ne?
Chapter 51 · 0% Book details