Sashe 54
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zo maza ki duba shayin idan ya dahu ki juyo masu ni walaha zan shige kar lokaci ya shige"
Rukaya Mamah ke kira, Zahra ce ta sauko Rukayar waje ta yi tana saukowa
Jiki babu karfi take nufo inda suke tana ta addu'a a kasan zuciyarta
Kanshin turaranta wanda Mamah ta bata kwaya dayan nan ne ya yi masu salama, kanshi mai yawan gaske domin bayan ta yi wankan nan na asubahi ta yiwa jikinta wanka da shi da hijabinta sannan ta gabatar da sallah, kasancewar baban turare ne bai fita daga jikinta ba, baima ragu ba gaskiya ita dai da yake jikinta ne ba lalle ta ji shi sosai ba bale ita din mutun ce mai son kanshi ta fi so ta ji shi har kanta
Ido take ta cicirawa bayan ta duka ta gaishe su baki daya, kanta a kasa daga inda take ta kasa aikata wani motsin kirki
MAMAH ta hadiye maganar turaran da ta so yi dan bata so ta siyawa y'ar dukan safe daga Amir ko harare harare daga Babangida, saima ta sakata yin aikin dubo shayin tana dubanta ta ce" Yauwa zahra akoy shayin Yayanku a kicin je maza idan ya yi ki juyo ko kawo, Amir taso mu je ina son ganninka....."
Mamah na gama fada ta yi gaba, Amir ya mike yana bin bayanta da dan sauri, hakan ya sa da sauri itama Zahra ta yi kicin tana ji tamkar zata kifa kirjinta na dokawa cike da tarin tsoro da firgici a cen kasan zuciyarta
Wayar da ya dauka yana dannawa ya ajiye a hankali ya kai dubansa kan ABAN AHMAD wanda tunda ta sauko rankatakaf hankalinsa da dukkan nutsuwarsa ta koma kanta har ta shige kicin ya kasance ya juyar da dubansa zuwa hanyar kicin din gaba daya har ya sha'afa da ba shi kadai bane a wajen
Wayar da ya dauka yana dannawa ya ajiye a hankali ya kai dubansa kan ABAN AHMAD wanda tunda ta sauko rankatakaf hankalinsa da dukkan nutsuwarsa ta koma kanta har ta shige kicin ya kasance ya juyar da dubansa zuwa hanyar kicin din gaba daya har ya sha'afa da ba shi kadai bane a wajen ya manta kwata kwata ya zamto kallon har ya zarta misali
A hankali MARSHAL ya dan kashe girman idannuwansa shima ya bi hanyar kicin din da kallo, sai kuma ya dawo da dubansa kan table din kasa kasa ya yi gyaran murya yana bude abincin a hankali ya furta" Bismillah Freind, mu karya"
A dan birkice ya juyo da dubbansa ya sauke kan Marshal, ya shiga bin hannayensa dake zuba masu abincin da kallo idannuwansa na yi masa wani irin zogi
Bakinsa na rawa rawa ya ce" MARSHAL, wacece ita?"
Tsai ya yi da abinda yake yi na yan sekwani, a hankali ya dago dubansa yana dan dage girarsa daya alamun tambayar wa fa?
Abu Ahmad ya sake waigawa kicin din muryarsa har tana fan hadewa ya ce" Wadda ta shige kicin yanzu, wacece ita dan Allah?"
Tsatsareshi da ido kawai MARSHAL ya yi, haka kawai ya samu kansa da tunanin to me yasa yake son sannin wacece?
Kar dai Abu Ahmad da girmansa da komai zai nuna yana son wannan yar yarinyar?
To in ba wannan ba meye wannan kallon da yake neman wuce misali?
Shi dai ya amincewa Abu Ahmad shiga nan ne dan kafin ya amince masa Abah ya amince masa, kuma shima zai iya cewa ya ga cenji a rayuwar mutumen sosai, bai taba dai ji ko gannin wani batancin ba bayan wanda ya fada da bakinsa cewar ya aikata a da, ama haka kawai sai ya ji kallon bai masa ba gaskiya, kar fa ya ringa sakewa karti a zo a nemi bata masa *y'aya!*
Idannuwansa ya dauke yana saka cokali a hankali ya ce" Y'ar Mamah ce"
"Y'arta ta cikinta?
Yaya aka yi ban santa ba Babangida?" Ya fada shima yana tare numfashinsa
BABANGIDA ya sake kura masa ido ya kasa saka abincinma a bakinsa, yana basarwa ya ce" Ba lalle ka santa ba ai"
Idannuwansa har kamar zasu dauki kwallah, abinda yake ji daga cen kasan zuciyarsa nema yake ya fi karfinsa, wannan abin da yake ji mai karfin gaske ne, a birkice ya bude baki yana kallon MARSHAL ya fara magana da son lalle sai ya san a yaushe ta zama y'ar Mamah bayan a sanninsa ya'yan na Mama daga Auta ba kari kafin Auta kuwa Adawiya ce sai Rukaya?.....ya ambaci ainahin sunnan MARSHAL zai fara yi masa maganar ta fito hannunta dauke da jug din shayin da kofunna na kwalba kannanu masu kyan gaske ta karaso ta ajiye a kusa da baban kwanon abincin sannan ta dan ja baya kadan kanta a kasa, muryarta a sanyaye ainun ta ce" Aban Abah, aunty tace kana kirana?"
Ji ya yi du duniya babu wanda ya raina shi irin yarinyar nan, yanzu maganar turaran da ya mata bata ji ba kennan?, Ta wani zo ta tsayawa mutane ita ga isashiya!
So ya yi ya barta ta yi ta tsayuwa har ya gama sannan ya kama kumatun nan nata ya murde ya mata maganar da babaku ko zata fahimta, ama idannuwan Abu Ahmad sun tsaurara a kallonta, kallon sam bai dace ba gaskiya, hakan ba daidai bane, a dole ya ce" CE MASA KIKA YI AN GAZA SAYA MAKI TURARE DA HODA A GIDANKU NE SHI SIYO YA KAWO MAKI?" Ya fada ne yana dan turo babar ledar da tana ganninta sai da ta ji kamar an wanka mata mari a gefen kuncinta dan firgita da tuna daga wa Ledar ta fito, wannan ai sakon da Hasan ya zo da shi ne jiya suka ki amsa
A rikice ta sake kallon Ledar, sannan ta kalli Babangida, muryarta har tana hadewa ta ce" Aa, jiya ne ya kawo kuma bamu amsa ba, Mamah ta hanna mu amsar sako haka, shi yasa baku amsa bama walahi , ban san kuma daga ina sakon ya zo nan ba"
Sai yanzu ya dan juyo yana kallon fuskarta, hawayen da suka ziraro ta gefe da gefen kumatunta ya bi da kallo, da irin jan da fuskar ke neman dauka lokaci guda, hakan sai ya bashi mamaki, menene ya yi mata shi yanzu ?
Daga tambaya?
Kansa ya dauke a hankali ya ce" Jeki "
Ajiyar zuciya ta sauke ta dan dago ta bi hannunsa da kallo a sanyaye ta ce" Na gode Allah ya saka da alkhairi "
Sake dagowa ya yi da expression din son gane godiyar fa? , Sai kuma ya tsinci bakinsa a hankali da fadin" Go ZAHRAH "
Da sauri ta juya ta nufi sama tana share hawayenta hadi da sauke ajiyar zuciya da godewa Allah da ya kubutar da ita bata amshi bulala ba, dayar zuciyar kuma ta cika da haushin abinda Hasan ya yi, a kan me bayan sun sanar masa Mamah ta hanna su amsar sakon hannunsa zai wani bayar?
Wa ya ba?
Dan tsaki ta ja tana cire hijabinta kasa kasa ta ce" Har ya sa Babangida na tunanin rokarsa na yi?
Gaskiya sai na fada masa kar ya kuma min haka!"
Sai da ta zauna irin kallon bawan Allahn nan ya shiga dawo mata, duda a hali na rikicewa take haka kawai ta ringa tsintar idannuwansa a saman fuskarta, kallon wani iri kamar wani wanda yau ya fara gannin halitar mutun a gabansa?..............., Sharewa ta yi ta shiga hada lalle dan tana son kunsawa ta kuma shafawa gashinta ta kwana biyu bata shafa ba sannan bata kunsa ba, gashi tana da salatif da yawan gaske
"Inaga, ya dace ka bar maganar nan, yarinyar nan fa tana da manemi , bayan wannan inaga ai kamar ka tsufar mata ko menene wannan rikicewa haka?" Marsha ya fada yana harhade girarakinsa dan abin ya ishe shi, su basu ci abincin ba, su basu tashi ba sai abu daya ke kai kawo
Hannayensa ya saka duka biyu yana dafe gaban kansa
Dago fuskarsa ya yi yana kallonsa ya ce" Yanzu a tunaninka kallon soyaya ne zai saka ni kafe yarinyar nan da ido hakaa kamar wani bakon shiga?
MARSHAL abin nan kamar ya fi
arfin soyayar so soyyaya, yarinyar nan ne tana min kama da wace na baka labarinta!"
Haka kawai ya ji wani abu a kasan zuciyarsa har ya dan kure shi da kallo
Dauke dubansa ya yi ya shiga dan taba abincin , ba dan yana jin ainahin tste din abincin ba, dan hankalinsa ya rabu biyu sosai har ya dan ji ya koshi sannan ya zuba shayin ya dan sha kadan kafin ya mike yana fadin" Tashi mu tafi"
Jiki ba kwari ya mike din ba tare da ya ci komai ko ya sha komai ba ya bi bayansa suka fice a falon sula nufi wajen motarsa suka shiga ya shiga tuka su
Sunna tsaka da tafiya ya samu hanya ya gangara ya tsayar da motar yana dubbansa ya ce" Kana neman hade min tunani fa, a wani kauye ne hakan ta faru?, Wannan fa yarinya ce, kuma ka ga itama wace kace abin ya faru a lokacin fa kace yarinya ce karama ai ko ita ina gannin da wahala ka gane kamaninta bale wai wannan yar yarinyar ko menene??????"
"Idanfa, tunanin da nake cewar eh lalle da cikina a jikinta aka koreta bayan na nuna ba nawa bane wannan y'ar itace aka haifa min?, Fuskarta ne take matukar daukan ta wace na sani, haka kuma sai take min shige da Ahmad, kai baka ga kamaninta da ni ba?, Idan fa wannan yarinyar y'ata ce?" Ya fada yana tare numfashin MARSHAL, duda ya san to ama me ya kawota gidansu?