← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 110

Sashe 83

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Dan Allah ya yi gangancin barin wani ya shigo maki gidan mana, kin ga ki yiwa kanki yaki kin ji Zahran MAMAH?"
Zahra ta hadiye dan yawu mai wuyar hadiya tana kallon Auntynsu
Aunty luba ta yi murmushi ta miko mata waya samsung mai kyau ta ce" Kin ga, na saka maki layi na kuma buda maki whatsup jiya, gft dina ne kin ga abin ya zo a kuraran lokaci, zan maki gagarumin gft na aurenki idan na koma irin na yayunki kin ji?

Ki kunna wayarki ki saka abin nishadi ki yi idan baki da abin yi mai mahimmanci, mamanki tace kar ki shiga kicin sai kin yi sati, ki ringa wanka kina saka kayan cen na dakinki ki rikita min shi kin ji yar albarka?

Mijinki ne idn baki yi ba wata katuwar zata yi kuma a zunubin harda ke tunda ke kika ki kulawa da shi kin fahimta?"
A sanyaye ta gyada kanta tana ta ayyana abubuwa a zuciyarta
Luba ta yi murmushi ta ce" Yauwa maza taso ga wannan shi zaki ci sannan ki sha wannan, yar albarkar Mamanta "
Tashin ta yi ta je ta zauna, Aunty Luba ta fitar mata da dahuwar da ta yi a kwano madaidaici, dahuwa ce ta kwadayi domin dukkan abinda ya dace baki ya ji yana marari ta zuba mata danma ta cinye tasss, ta mika mata ta dauke kanta sannan ta dauki madarar da ta zuba maganin, magani ne wanda a maganar gaskiya ya fi karfin budurwa, domin magani ne na tayar da sha'awa, magani ne wanda muka yi muka gwada kuma muka ga aikiinsa a bayane, ba maganin budurwa bane, hasalima maganin matan da suke fama da daukewar sha'awa ne , da bushewar gaba, uwa uba na albasar dake dayar goran wanda shine mai matukar saka mace jika, hadadun magungunnanmu da ake iya samu a wajen MAMAN ABDUL KHAIR, ko a nan wajena watau nijar da Nigeria, rikakun magungunnanmu da basu da hadi da cutarwa sai karra lafiya da inganci, sunne Aunty luba ta rika, bata tafia babu su a jakarta, bata jimawa bata dafa na ni'imar nan ta sha ba domin wanke ciki yake yi tassssss mace ta samu lafiyar jikinta da danshi iya danshi, tun jiya ta so zubawa ama ta bari ta ga take takensa, mamansa ba zata gane ba, dole sai an tunkuda keyarsa koda za'a samu abinda ake so, ya riga ya tashi cikin akida tasa ta kansa, sannan ya hadu da macen da ta sake durmiyashi a ciki, ire iren mutanen nan wasun sai dai ka yi hakuri ka tafi da su yadda suke kawai, ita bata son haka, shi yasa take son kwana ukun nan da ya rage ta yi iya yinta dan gannin ta karya alkadarin yayanta
Hankali kwonce ta cinye, ruwan dake cikin galan nema bata ji dadinsa ba domin salaf da shi sai dan gafi gafi, sai kuma madarar, wani ikon Allah tana gama shanye madarar barci ya ringa fuzgarta, barci mai nauyin gaske da kuma wata irin mika
Luba na fuskantar haka ta sakata zuwa ta kwonta ita kuma ta shiga kimts mata gidan duda ba wani dati da ya yi ta saka mata turaran wuta ama bata shiga dakin mijinta ba, ta kuma koma da abincin nan na wajensa dan idan an barima yana iya lalacewa tunda shi ya karya itama kuma ta karya
Bayan sha daya ta hau ta yi mata salama ta sauko ta tafi bayan ta sanar mata code din budewa da rufe kofar baba
Tana tafe ne tana kallon yannayin gidan, har yanzu shiru ya yi yawa kamar ba har rana bace ke neman fitowa kowace ta labe dan an yi mata kishiya, uhum an yi mata kishiya mana wannan ko da docter ya santalo yar budurwa ta masu ciwo haka kuwa?

A nutse ta karasa bangarensu a ranta tana ta tunanin saurin da Furera take yi tana dan waige waige, ko ina zata je ita kadai?

Basarwa ta yi tana shigeqa bangaren MAMAH ta ayyana a ranta kawai ta yiwu kiran wani aka aiketa, dan ko kati ba'a bari yan matan su je siya da kansu, akan ba masu aiki su siyo ne
Tana shiga falon ta ringa murmurshi tana fadin" Masha Allah Mamah wadinnan kuloli fa?

Lalle yar gatan MAMAH aka aurar"
Mama ta yi murmushi ta ce" ni ai na zata zaki ganta a nan ne, kin fa san hali har ce mata ake yi jelata"
Tana murmushi ta zauna ta umarci Auta kan ta je ta kai abincin ZAHRA na rana, tana kallon Aunty Amarya dake cire kunshi ta ce" Uhum ai tana girki na tarda ita mutumen ba dai rashin hakurin yinwa ba"
Mamah ta dan yi tsai, girki kuma?

Kennan dai babu abind....babu........., Sai kuma ta share ta ci gaba da abinda take yi
Aunty Amarya kam wani irin salama a cen kasan zuciyarta da take ji bata san yaya zata misaltashi ba, yanzu haka ance tafiyarta gannin likita jibi ne, zata je ta ga likita bata san lokacin da zata dauka ba, ta tambayi bata da lafiya ne?

Mamah tace sai tace zata gani, kuma gannin likitan nan ance wai da Luba ne zasu tafi kuma da wani, bata san wanin ko wanene ba, ita dai bata da damuwa da hakan, haka take ji a ranta yanzu tana iya tafia ko'ina ma, bata da wani tunanin baya a cen kasan zuciyarta mai hannata motsi, haka tun daga jiya da safe zuwa yanzu bata hadu da wani cin zarafi daga matan Docter ba, kai fitowama basu yi ba bale su wulakantatan, koda yake su dai suka sani in dai neman fitina ne su yi ta yi
Mikewa ta yi ta tafi sama dan wanke lallen, hakan ya saka Luba kasa kasa ta ce" Mamah, yanzu idan aunty ta rikice mana idan ta ga Aban Zahra fa?

Ni du sai nake gannin a zauna da ita a sanar mata da shi a tafiyar"
Mamah ta girgiza kanta ta ce" Ai ba zata ganshi ba, wanda zata gannin daya daga cikin bodyguard din Babangida ne shi Aban ZAHRA ai bama zaku yi jirgi daya ba, shi fa tun gobe zai tafi dan baban likitan ya bukaci fara zaunawa da shi ya sanar masa komai a gaba da gaba bayan na waya da aka sanar masa, shi likitan ai shine yace idan kuka je kema kwana daya kawai zaki yi ki yi tafiyarki, in yaso su sai su amsheta, yace ne kasantuwar Aban ZAHRA a wajen ba yanzu bane zata ganshi, wai sai aikinsu ya yi nisa sosai zasu iya tambayarta in har zata iya yafewa mutumen koda ta ganshi a gabanta?

Kin gane dai, kuma ba nan take zasu nuna mata shi ba dan kar ta ga ko shine yake biya da sauransu ta yi zuciya, dole sai an bi a hankali su nuna sun sa ya zo da sauransu, kuma kin ga a zo a yi a bude a hankali a hankali har a gamsu da samun lafiyarta, dan ko da gangan ta nuna ta huce a lokacin da zata ganshi a gabanta idan wani abu ta dane su zasu fahimta, manyan ma'aikata ne da ake ji da su du duniya, ai kin ji kudin aikin du na wuni guda haka ya biya bawan Allah, ni zuwa yanzu sosai yake bani tausayi, ya yi nadama, ya kuma yi, baban laifinsa raping din da ya yi mata, wannan kuwa kowani bawa da salon kadararsa, kin san da har cewa ya yi idan har ta warke tace zata kai kararsa dan girman Allah a bari ta rufe shi in dai haka zai sa ta idasa yafe masa?
Chapter 83 · 0% Book details