Sashe 38
Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko aman yada iri ake yi?" Ta fada da dan yannayi na rainin nan, wanda nan take ta saka shi tsareta da ido hankalinsa na neman tashi
Rai bace, muryar Zahra a mace ta dube shi tana magana tana jin kamar ba'a jin maganarta ta ce"
22 D5
Rai bace, muryarta shake , ta budi baki ta fara magana tana jin kamar ba za'a iya jin amon muryar nata ba ta ce" Yaya Bani kwanon na tafi"
Wani murmushi na raini Laraba ta yi tana fadin" Bakya so a yi maganar ne ?
Shi ai wannan da kika gani bayana kansa yake yi ne, idan baki bari aka gani yanzu ba zai bayanar da kansa ne, dama mene Allah na tuba me za'a jira da hujajen kwano?"
Kasa mika mata kayan ya yi, yana kallonsu da mamakinsu da tarin takaicin da ya tsaye masa a zuciya ya ce" Wai me kuke nufi da furucinku ne?, Daga cewa na daukota na kawota zaku sakani a gaba kamar wani sa'anku da wasu magangannu mararsa tsari da dadin ji?
Me kuke nufi da furucinku ne?"
Da tarin rashin kunyar da Laraba ta fi iyawa ta wani dakatar da shi tana ruko idannuwanta ta ce" kai malan ya isheka hakanan!
Ka kuwa san ko ni wacece?
Lalle samun dama, bawan Allah inace sunnanka soja karamin soja direban baban soja uban gidanka ko?
Ka bada amsar tambayar da akai maka kawai ka yi tafiyarka bama son dogon turanci idan ba haka ba hukuncin da zaka amsa daga wajen oganka sai ya gigita tunaninka!
Lalle abubuwa da yawa sai sun cenza a gidan nan Allah dai ya kai damo ga harawa....!"
Mamaki kamar zai kashe shi daga shi har su Furerar da Ita Zahran, abu daya ya hanna shi babala yaren nan rashin sannin sakamakon abinda bala sun zai haifar
Da ba dan wannan ba, yana rantsuwa da wanda ransa yake hannunsa da a cikin gari ne sai ya hau su daya bayan daya tamkar doki ya murza iya murza kafin ya ci masu uwa, har a nunawa soja iya takun iskanci ne?, wadinnan ai da gani ba tarbiya, ama ya yi mamaki a gidan su sir dama akoy irin wadinnan?
Dan bai san waccece Laraba ba, bai san cewar ba yar gidan bace da ita din ya gurji nata bakin
Jiki ba karfi ya mikawa Zahra wace ta so yin tafiyarta a ranta tana ayana' ai sai ka yi tunda kana da lokacin shashanci!'
"Ke dan ubanki.....Au dan uwarki ba zaki bamu amsa ba?" Laraba ta sake fada da haushi haushi, ita fa abinda ya fi dan daga mata hankali jin yace wai daga gidan sir aka ce ya kawota, so take ta san ubanda ta je nema ita daya!
Rai bace idannuwanta na lulumshewa ta juyo tana kallonsu , a dake tace" Aman nan da na yi ne kuke son sanin ba'asi?"
Furera ta yatsine baki ta ce" Eh shi fa, budurwa ba zazabi ba komai a ga kina kelaya amai na menene to?"
Lumsasun idannuwanta masu shige da na yar shaye shaye ta sake lumshe masu a gajiye ainun ta ce" Ciki ne da ni fa, ku shirya sake hada numfashi da dan shege bayan ni!"
A zabure Furera ta rrike baki tana fadin" Lah"
Ita kuma daga haka ta amshe kwanonin ta yi gaba ta barsu gaba dayansu baki sake kamar zasu summe da jin furucin bakinta, dan babu wanda ya yi tsumayin amsa daga gareta irin wannan face kukan da ta saba
Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke yana kallon tashin balagagen iya shege sannan idannuwansa kyam a kanta har ta bacewa ganninsa
A hankali ya juya zai tafi sai kuma ya dan dakata ya ce da su" Ku sani, shi shari da Kuka gani dan aike ne, kuma wannan furuci naku dole na fadawa magabatanku dan a san da maganar da kuka fada baki daya, daga zo kaita ba zaku raina min wayo ba ku min kazafi daga ku din har ita!"
Har ga Allah sai da Furera ta ji kamar zata summa dan tashin hankali da jin furucinsa
Da sauri ta bi shi , sai dai bai tsaya ya saurareta ba ya yi gaba abinsa yana jin inama zai sake gannin Zahra kafin ya tafi?
Inama zai samu ganninta?
Koda yake.......zai nemi hakan.............
hankali tashe furera ta dawo tana kallon LARABA dake tsaye kikam hannayenta harde a kirjinta ta ce" Aunty kin ji me yace?
Idan maganar nan ta fita walahi na shiga uku, innalilahi wa inna ilaihi raj'une sai da Babarmu tace mana mu kiyaye dan Baban yaya ya shiga lamarin yace du wace ta kuma irin haka da shi take ba da kowa ba!"
Laraba ta ja wani tsinanen tsaki ta ce" Ke dakata, ba wannan ya fi damuna ba, yarinyar cen me take nufi?, Daga ina take?, Maganar cikinta da gaske ne?
Uban wa take nufin ya mata?, Dan maganar wancen a banza na dauketa shima ai ba zai yarda a san ya dauko yarinyar ba, kuma idan haukansa ya saka shi fadi zai jama kansa balaki ne dan kuwa sharin da zamu kula masa sai ya dame damuwarsa tsaf ya shanye ya turmuza shi a kabari!, Maganar yarinyar ce nake, wai daga gidan Marshal take, dama tana zuwa ne ita daya?"
Ita dai jikinta du a mace, hankalinta kuma a tashe, dan ta san idan har maganar nan ta fita zata samu sakamakon da ya dace da ita,, jiki a sanyaye ta ce" Gaskiya inaga sai dai ko dalilin kai masa abinci ko wani abin da ya shafi sakon Hajia, dan gaskiya bana tunanin akoy wani abin da zai kaita gidansa daban, ke Baban gida fa ake magana a kai ba wani ba, ke dai kawai Allah ya dora ki kansa ai yayanmu ba dai soyaya da shegiya ba walahi har abada!"
Murmushi ta yi tana sauke ajiyar zuciya sannan ta kama hannunta ta ja tana fadin" Kin ga, zo mu yi mu leka ki gano habibinki na rako ki inada wajen zuwa kafin dare ya yi nake son dawowa tunda ba zai zo ba mu tafi kawai wata rana ma hade"
Da wannan suka fice a gidan ba tare da an hannata fitan ba dan kuwa ta saba raka Larabar dama zuwa gidansu idan ta zo aika
_____________________________________
Yannayin tafiyarta kadai ya isa ya sheda maka halin da take ciki a lokacin da ta yi salama falon Hajia ta ja ta tsaya ta zubawa Auta ido wace ke zaune tana Home work
Amsawa ta yi, lokacin ne kuma Adawiya ta sauko itama daga saman tun hawanta dan gannin ko mamansu ta fito ne?
Ido cikin ido suke kallon junna kafin ta karaso falon ta ajiye kwondon ta juya ta raba gefen Adawiya ta shiga hawa sama tana rike karfen nan dan juwar dake kwasarta
Da kyar ta iya kai kanta dakinta,, tana shiga a nan ta duke ta sada kanta ta fashe da matsanancin kukan dake tuko mata zuciyarta, jikinta na rawa gaba daya na mugun yannayin da take ciki hankalinta tamkar zai bar gangar jikinta
A zabure ta dago jin an dafa kafadarta ta sauke dubanta a kan Adawiya
A boye ta sauke biyayiyar ajiyar zuciya sannan ta ja jikinta ta hade bayanta da jikin gadonta tana kallon Adawiyar da ta harde hannayenta da taron takaici ta ce" Bayan sumar da kika yi dan katon banza ya nuna baya sonki yanzu kuma kukan me kike yi kamar wace mijinta na sunna ya saka ba a cikin hayacinsa ba?"
Dubanta ta dauke tana cije lebenta, bata tunanin in har akoy wanda zai gane halin da take ciki, bata tunanin in ba wanda yake rayuwa irin tata ba zai gane me take ciki a kusa kusan nan ba...........
Ido Adawiya ta lumshe, haka kawai ta ringa jin ba zata iya barinta ita daya ta yi kukan abin nan ba, tunda ta dawo din ta kasa nutsuwa du kuwa irin masifar da ta saka su a yau sai take ji a cen wani bangare na zuciyarta tana cike da damuwar halin da take ciki
A sanyaye ta zauna a daf da ita, ta kamo hannunta tana kallonta
Muryarta a raunane ainun ta ce" Dukama nawa kike ne Zahra?
Yaushema aka haife ki?
Ke ko shekaru kika dauka masu yawan gaske ai komai na Allah ne, yadda ya baka tsarin rayuwarka kuwa haka zaka tafiyar da ita kana so ne ko bala so, ni kam da zaki ji nasihata d kin dauki lamarin wannan bawan Allahn nrml kin share hawayenki kin murje idannuwanki kin rayu daidai kidan da rayuwa zata gabatar maki, Zahra aure kansa na mutuwa a zauna lafiya bale wai soyaya?
"
Jikakun gashin idannuwanta ta dago a hankali ta zubawa fuskar Adawiya ido
Muryarta a sanyaye ta ce" ce min ya yi shine jigona, zai zauna da ni duk rintsi, zai zamo miji a gareni, zai ciyar da ni da gumin fuskarsa, babu ruwansa da wacece ni tunda ba ni na halici kaina ba, yau ko nice na aikata babu abinda ya dame shi koda yaya goma na haifa bale ba nice na aikata ba, yace ya shirya fada da kowa a duniya a kaina, hakan ya sa na ji sanyi a zuciyata, na ji nima ina iya tarban kowa kansa, nake sauraron hirarsa da shauki, nake yarda shi koda kuwa na san hakan ba daidai bane, a kansa na yiwa Mamah karya ya fi a irga dan a tunanina na san cewa daga ita sai shi a duniya masu sona da kaunata wa'inda zasu iya rufa min asiri su rayu da ni a kowani hali nake ciki, na kuma san du soyayar da take min dole zata so ta wankeni ta kaini dakin miji, mijin kuwa shine, aunty Adawiya anya ba an shiga tsakanina da shi bane?
Anya ba da wani abin dake faruwa ba kuwa?
Yaya aka yi su yaya suka kasance a wajen a irin wannan lokacin?
Me yake faruwa ne da Maawiyana?"
"Kina ji?