← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 110

Sashe 47

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kace yarinya ce a lokacin sosai, shekaru sun tafi, kai din yanzu ka kusan sittin, ko ba'a fada maka ba ka san shekaru sun ja......., Inaga ka samawa kanka sasauci ya fi, koda karar ka zata kai ka yi kokari ka amsa, ba wai ka je saudiyya ka tare da matarka ka yi kamar baka da wata rayuwa kafin wannan....., Kowani bawa fa na aikata aikin sabo, kowane bawa da ka gani yana da sirri mai tsauri, na wani ya fi na wani ne, rashin dadin al'amarin a yi ta tafia ba tuba, kuma a mace da hakin bayin Allah a kai, ka kuma tuna da ayar nan Kama tudini tadana,ka dan ba kanka sasaucin dacin zuciya........, A yanzu kai babban mutun ne, ka tara, ka dan waiwaya ko zaka dan taimaka mata idan tana raye biensur" Baban gida ya fada yana fuskantar Aban Ahmad da ya zuba masa ido kamar ya ga bako a gabansa
Yana ajiye maganar ya mike ya sake shan shayin nan sannan ya wuce ba tare da ya kuma ce masa uffan ba
Bayanshi ya raka da kallo har ya bacewa ganninsa sannan ya sake juyowa wajen dardumar dake shinfide
Gaskiya tsagwaronta itace ya fada masa, ba boye boye ba kwane kwane
Shi yasa yake matukar son mu'amalarsa da Babangida,ya girme shi nesa ba kusa ba amma idan ta kama ya fuskance shi tsaf zai fuskance shi ya sanar masa abinda yake zuciyarsa koda kuwa hakan zai zamto bacin rai a gareshi
Jiki a mace ya sake duban hanyar, sai kuma ya shiga lalubar matarsa ta whatsapp yana tunanin Allah ya sa bata kwanta ba duba da tazarar awannin biyar dake tsakaninsu da saudiyyya,gashi magrib ta gabato ta yiwu har ta kwata
Allah ya taimake shi tana zaune a lokacin, hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Umman Ahmad"
Tana murmurshi ta amsa shi, sai dai yannayin amon muryarsa ya sakata dan yin jimmmmm,
Ita dai ba yarinya bace, hasalima tana da shekara talatin da biyar ya aureta, sun hadu ne a kan harkar kasuwanci, sun fahimci junna da wuri ya kuma share hawayenta na shekaru da ta kwasa bata samu miji ba ya gwongwajeta ya aureta, hakan ya sa tsakaninsa da ita fahimta ta fi rashin fahimta, a zamansu kuwa zuwa yanzu abinda bata sani nasa ba kauyansa da yake boye mata ya ki sanar mata bayan ya sanar mata waye shi a da, ya ki sanar mata sunnan kauyen dan
Karara ya gane idan har ya sanar mata tana iya zuwa bincikar labarin abinda ke cikin zuciyarsa, idan ku
wa haka ya faru ba zai so ba, bai bar wani abin a zo a gani ba, banda boyayan tarihi marar anfani bai bar komai ba, lalle Docter Ahmad SULAIMANE ya zamo uba a gareshi kuma mafarin shiriyarsa, haka kuma hanyar samun budinsa......, Shine ya sanar masa cewa bawa na iya cenzawa daga mutumen banza zuwa na kirki idan har ya sala kansa, shi ya amshe shi ya kuma bashi damar jin zai iya cenzawar, shine ya bashi jari yake kuma taimaka masa da dukkan abinda ya dace har yau ya zama haka........

Daga haka baya jin zai iya sanar mata kai tsaye sunnan garin dan babu wanda zai gyara abinda ya bata
Muryarsa ce ta yi rauni ainun, a raunane sosai ya ce" Na takura ki ko?

Me kike yi ne?"
Da kula ta ajiye zanen da take yi ta mike ta bar wajen yaran tana fadin" Aban Ahmad lafiya?

Me yake faruwa ne?"
Idannuwansa ya lumshe hawayen idannuwansa suka shiga zarya a saman kuncinsa
A raunane ya ce" Ina gannin, ya dace yanzu na waiwayeta....., Umman docter tunda kina shirin zuwa gaisuwar ABAH ki zo da yara baki daya sannan ki zo min da dukkan wasu takarduna masu mahimmanci, ina gannin zan jima a kasar nan har sai na sameta"
A hankali ta lumshe idannuwanta tana jin wani iri a cen kasan zuciyarta, Allah yana gani zata fi kowa jin dadin gannin damuwar mijinta ta kau a kan wannan lamari, sai dai haka kawai take jin kamar tsoro tsoro, da kuma tunani mai rauni sosai a kan maganar, shin idan ya ganta .....

Ras bata da aure fa?

Idan abinda ya barta da shi yana nan ras ras fa?

Idan har a lokacin ba wai iya sha'awa bace kawai ta kaishi gareta harda so fa?, Idan wani abu na iya kasancewa tsakaninsa da ita fa.....?

Shine baban firgicinta, ba wai kishiya ce damuwarta ba, farin cikin da ta samu, kwonciyar hankalin da take ciki, dan cercle dinsu ita da mijinta da
ansu biyu ne bata so ta ga wani abu da zai iya tarwatsa shi ko ya lalata masa zane komai kankantarsa, shin me haduwarsa da abinda ya tsaye masa a zuciya yake nufi?

Da kyar ta iya rarashinsa, sannan ta sanar masa in sha Allah zata yi ta gama komai ta dawo da wuri da dukkan abinda ya tambaya, ta yi masa Addu
ar samun abinda yake nema idan har alkhairi ne hakan, sannan suka kashe wayar
Sunna kashewa ta samu kanta da zama a waje daya ta dafe gaban goshinta
Tambayoyi ke mata yawo a kwanyar ta
Shin zaman mijinta da hakin nan ya fi mata alkhairi kan son zuciyarta dan tsoron kar a lalata mata farin ciki?

Sannu a hankali ta ringa kawo farin abin da bakinsa har dai ta mike kan abu daya, ko menene ta sani ba zata taba bari ko yin sanyar da wata zata zo mata rayuwa kai tsaye ta wani lalata mata kwanyarta da farin ciki a tsakaninta da mijinta bayan ta dauki lokaci cikin kunci ta kuma dauki lokaci cikin gina haka.......dolema zata matsa kusa da shi da wuri wuri dan ta san me yake ciki ta kuma taya shi nemowar dan ta kasance a wajen a lokacin da abin zai faru ko dan ya gane cewa tana nan, tana kuma tare da shi, ko menene tana hankalce babu wace zata yi mata kwacen mijinta, ko meye shi ita shine mijinta tana son abinta a haka......

Wannan kennan
Washe gari Fatima ta samu Rukaya da maganar Hasan ta sanar mata abinda yake so, sai dai ta kasa sanar mata ita kuma abinda take so kafin a kai ga hakan
Rukaya ta ji dadin haka ainun, harma tace da ita zata sanarwa Mamah da kanta abinda ta yanke sai su yi
Ita kuwa ta bar maganar a ranta cewa koda ya zo an ganshin ta yiwa kanta alkawarin sai ta sanar masa wacece ita, dan babu abinda zai sa ta yi wasa sai magana ta shiga jiki a zo ana tsunguri tsoma
.........................................................

Bayan sati biyu da yin arba'in din DOCTER , ya kama kwanaki hamsin da hudu da rasuwarsa, Yau ranar asabar da karfe goma sha daya na rana
Yana cikin aiki a office kira ya same shi daga gida, da yannayi na tashin hankali daga wajen Mamah, hakan yua saka shi dauko bak'ar rigar swuit dinsa ya fito da dan sauri ya amshi ky din motarsa ya tuka kansa da kansa ya nufi gidan a ransa yana ayyana Allah ya sa lafiya dan yadda ya ji muryar maman ya dan daga masa hankali gaskiya, bata cika yin magana a haka ba in ba abu ya shiga zuciiyarta da karfi ba
Tunfa ya fito ya nufi bangarenta ya ga kannensa a tsaitsaye kowa yannayinsa wani iri ya saka shi sake shiga da saurin da ya fi na dazu cike da tsoron ko wani ba lafiya ne a ciki?

Yana shigowa ya shiga binsu da kallo, Uman Abul a tsaye , Uman furera a zaune a saman kujera, Aunty Amarya a saman cafet kaffafuwanta a lankwashe, Mamah a zaune a saman kujera idannuwanta sun mata ja tana kallon kofar shigowar, tana ganninsa ta sauke ajiyar zuciya hadi da dauke kwalar dake kurmin idannuwanta ta fuskaceshi tana fadin" Bismillah mana Baba karaso ciki"
A hankali ya idasa shigowar yana sake yin salama a tausashe sannan ya ringa bin Maman Abul da kallo gannin ta juyo tana cikin masu amsa masa harma ta zagayo ta zauna a saman kujerar itama tana dauke dubanta a kansa
Rasa me zai fara fada ya yi, idan ya kalli wannan sai ya kalli wancen har sai da aka sanar masa zuwan daidaiku daga cikin samarin gidan magidanta wa'inda suke neman izinin shigowa, hakan ya saka shi farfadowa ya juya da kansa ya leka ya ga ko su waye, dan haka ya basu damar shigowar baki dayansu ciki harda yaren kannanu kaf dinsu har ya zamto falon Na Mamah na neman yi masu kadan dan bai kai na Abah girma ba gaskiya
Du zama kowa ya yi bayan gaishe gaishe da junnansu suka dawo da dubansu kansa shi kuma yana tsaye ne yana binsu da kallo gaba dayansa yana shawarar shin ya tafi ne ko ya tsaya......?

Me zai ce da su idan ya tsaya din?

In wata rigimarsu ce suke yi shi yaya zai yi da su?

A nan dai iyayensa ne sai kuma kannensa, iyayen nasa kamar sunne suke wani halin
A fole dai ya karasa ya zauna saman kujera yana kallon Maman Abul wace ya fi fuskantar ta fi kowa hawa sama a tausashe ya ce" Hajia wani abu ke faruwa ne?"
[11/26, 7:32 PM] MAMAN ASLAM: Kai ta dago ta zuba masa ido, ita gaba daya wani kara bijime mata yake a idannuwanta, kyansa kwarjininsa, tsarin mulkinsa sake cika idannuwanta suke yi, buga mata zuciya yake ko sunnansa bale shi din da kansa, shan kanshinsa shine tak abinda take nema a wajen maza, ta fi so yana shan kanshin nan dan gudun kawo rainin yan matan zamani a duniyarsa, a haka dai da yake a haka ya yi mata dari bisa dari, sai kuma ta lumshe idannuwan nata gannin kamar zai kalleta, muryarta na rawa sosai ta shiga share hawayen karya, shikenan ?

Bakin maganarsu kennan?

Shikenan idan ta tafi kuma sai yaushe?
Chapter 47 · 0% Book details