← Book details Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 110

Sashe 17

Dakika Biyar Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dif ya yi yana dantse lebensa ya juya ya dauki hanyar gidansa dan yana son sake yin wani binciken, a sanninsa a yanzu babu kayan Manal ko daya, dan ya sa sun kwashe, ama kuma ta yiwu ta bar ire iren magungunnan nata na mata
________________________________
Kwonci tashi asarar har Manal ta yi kwana arba'in da rasuwa
A tsakanin kwanakin nan abubuwa da dama sun faru, ciki harda yajin aiki da wasu malamai suka tafi, ama banda wasu daidaiku
A irin wannan ne aka wayi gari yai saura sati hudu a yi saukar su ZAHRAH wace zasu kai hardarta baki daya, gagarumar sauka ce da zata dauki kwanaki ana yi dan har a kafafen yada labaru za'a saketa
Dan sauri take yi da abin amsa amo a kunnenta wanda ta jona da wayarta yar karama tana amsa kiran Ma'awiya tana dan murmushi har ta karaso wajen da zata samu su Furera dan ta sanar masu baba direba fa ya fitar da mota tun dazu su ake jira
Tunda ta karaso gabanta ya yanke ya fadi sakamakon ganninsu da ta yi sunna tare da LARABA sunna hira cikin raha
Sau biyu tana juyawa, sai kuma ta dake ta juyo a sanyaye ta karaso inda suke tsaye ta yi salama cikakiya ta dan dakata tana kallon irin debotan da suke yi sunnaa watsarwa da kallo irin na raini da kaskanci
Sake jan numfashi ta yi a sanyaye ta ce" Asalamu alaikum wa rahamatullah"
"Yau na ga bakin naci da masifa a gidanku Fursy baby, wannan iya yin haka ake maku kennan ba ji ba gani kamar wata tsaftataciya!".

Laraba ta fada ba dar, ba kawar da kai, ba jin kunya bare kiyaye batawa dan Adam
Furera da ta fita halin na rashin da'a ta tare maganar tana fadin" Kema kin ga fi'ili irin na makotan masu kudi ko?, Ana abu kamar an san Allah bayan sai a hankali ne kawai!"
*DA
A BIYAR*
_MALLAKAR_
*SAJIDA NIGER*
*Da sunan Allah mai rahama mai jin
_11_
*Garabasa , garabasa,
, dole na gwongwajemu ai, in sha Allah daga yanzu har zuwa na rufe free page daga bakin page 10 du mai so ya garzayo ya biya dari ukunsa, ta hanyar transfer ko katin MTN, account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank sai ki bani shedar biyan ta wannan number +22793811618, idan kuwa katin ne shima ka turon hoton ta number +22793811618, MUTANENA na NIJAR ga naku, katin Sahelcom ko ta airtel ta dala daro, watau 500 francs, sai ku karkare ku turon hoton ta wannan number da take tawa +22793811618, sai kun zo
Kanta ta sada, zuciyyarta na dokawa da karfin gaske
A hankali ta dan zabura sanadiyar kiran sunnanta da Ma'awiya ke yi da dan karfi dan ya tabata fada ne yan uwanta ke janta da shi dan yana jin komai da suke fadi
A hankali ta ja wani numfashi ta sake dago dubanta tana kallonsu
Aunty Rukaya ce ta juya da nufin tafia , dan ita bata son irin haks, ita bata zagin yarinyar nan, bangarensu daya tare suke kwana sunna tashi, ba ruwanta ne kawai da ita, bayanshi bats zaginta bata wulakantata ko daya
Da sauri Laraba ta kamo hannunta tana karya wuya ta ce" Rukaya ina zaki tafi kuma muna yin managa?"
Rukaya ta ja numfashi tana fuskantarsu ta ce" Aunty Laraba, ni dai kamar yadda na taba fada maki zan maimaita maki, ni kam babu ruwana da wannan rigimar aunty, kin ga yaya Baba tamkar uba yake a wajenmu, ba Sa'an wasanmu bane, babu irin wannan maganar a tsakaninmu da shi, ba zan taba zuwa na nuna masa kina sonsa ba, ko giya nake sha, abu ne dake iya ja min komaima dan haakan raini ne, shi kuma baya so a raina shi, kawai ke ki same shi mana ko ita furerar ta same shi tunda ai itama kanwarsa ce ko?"
Ido Furera ta zarro tana fadin" ke kar ki sakani a halin ha'ula'i bayan ni ba kowa bace, ke idan kika yi duk rintsi yana jin kunyar Mamah "
Rukaya ta tsatsareta da idannuwanta ta ce" Me kike nufi da yana jin kunyar mamah?

Ai kin san Baban gida ba futsarare bane, a gidan nan babu uwar wanda ya raina, sai dai shi a ringa neman gannin tabewarsa, wannan kuwa karyar dan Adam tunda Allah ya rika ya kuma iyayensa biyaya"
Itaama fureran sai ta ga ai kamar zaginta Rukaya ke son yi, a hayayake ta budi baki zata rama Laraba ta tare tana shiga tsakaninsu ta ce" Haba yan kanaina menene wannan abin dan Allah?

Kunna abu a gaban bare salon ta dauke ku ta kaiku gaba ta watsa?

Ku daina irin haka mana ai tataunawa muke yi dan mu samu mafita daya tak wace zata talafa mana mu isar masa da maganar ko?"
Furera ta ja hijabinta da Laraba ta rike tana huci ta kallo wajen da Zahra ke tsaye ta kalli wannan ta kalli wancen ta ce" Ke zaki bar mana nan ko ba zaki bari ba kin tsaya mana a kai kamar aljana kina kwashe mana sirri kamar kin hadu da shegu irinki, ki bace mana a nan tun kafin ranku ya bace !"
Ido ta rintse da karfi tana jin zuciyarta na rinewaa
tana yin wani irin baki kamar zata mutu
Rukaya ce ta bude baki, a daken itama, sai dai ba zagi ta ce" Me kike so?"
Da kyar ta iya bude bakinta bayan ta bude idannuwanta da suka yi jajajir tana kallonta a sanyaye ta ce" Dama makaranta ne zamu tafi "
Rukaya ta dauke dubanta, dan hawayen da suka zubo a saman fuskar Zahrah sai ta ji kamar zasu girgiza mata zuciya , ta ce" Baki san kuma kun shigaa hutun bane?

Bakwa yi sai an biya malamai!"
"Mtsssss aikin banza aikin wofi bata lokacin banza da wofi, ni da nice ke da zuwa zan yi na kama daki a wajen da za'a ringa biyana ina anfanuwa da dan lokacin da nake da shi tunda uwa bata so uba ba'a san waye ba bale in yi tunanin samun yanci irin na kowa!" Furera ta fada tana jijiga, dukkan bacin rai da tashin hankali na bayana a tare da ita, a duniya ta tsani ta budi ido ta ga wannan yarinyar, bata san me ta mata da zafi ba ama ta tsaneta fiye da komai!

Kaffaafuwanta dake rawa ta kai duke a hankali tana jimke hannayenta duka biyu tana neman hanyar da zata jure ta dauki wannan tashin hankalin dake mata yawo a kwonya
Anya kuwa zata aurun?

Gaba daya daidaikun yan matan gidan nan sun tona mata asirin cewa ita shegiya ce
Anya kuwa ba bacin lokacin bane take wani karatu da sauransu zata gama ne ta tashi a tutar babu a banzar bazara
Wani lokaci Saude tace mata ta bi rayuwa a hankali idan aka wayi gari mahaifiyarta ta rasu ko ta bar gidan Docter tata ta kare fa, ta jima tana wannan tunanin daga baya ta watsar, a yanzu kuma sai kawai ya dawo mata a birkice
Kanta ta sake dagowa ta zuba masu ido, bama irin Laraba da Furera, gaba daya baki kirin take kallon gefen da suke tamkar an shafe su an maye su da baki
A zuciyarta suke kwana suke tashi da tsoro da fargabar haduwarta da su a gaban wani bako dan ta san da ta aikata da bata aikata ba sai sun yi sanadiyyar da bakon ya san wacece ita a gidansu cewarsu kar a lalatawa babansu sunna
Da kyar ta iya mikewa tana laluben hanya har ta ji maganar da Ma'awiya ke yi cewar ta bar masu wajen kar ta kula su ya tsinke, hakan na nufin ya katse kiran ne da ya jita shiru
Layi take yi har kamar zata kifa har ta karasa bakin bangaren matar da ta fi kowa jin tsoro a duniya, watau mahaifiyarta
A hankali ta idasa hawa taa shige balbalin dake iya sadata da kofarta ta kama ta murda tana jin hannun wajen murdawar yana da wani irin sanyi, bayan ba sanyi ne da shi ba jikinta ne ya kwashi zafi
Budewar kofar daidai da bugawar zuciyarta da masifafan karfi, ama battaa yi niyar juyawa ba, yau ko me zai faru sai dai yaa faru
A hankali take takawa bata iya yin salama ba tana hangenta a wajen diner tana gyagyara kayan girkinta da ta yi da kanta cikin kwonciyyar hankali sannan cikin shiga ta dogon hijabi har kasa kuma bulememe
" har kun dawo ne?, Kin ga ai har na gama fa ina jejerawa, ajiye min sakon a cen ki dubo min docter ya shigo ne na kai maganinsa" ta fada cikin zazakar muryarta mai fita da sansanyan amo da dan kaza kaza na matar da bata da kiwya
Jin shiru ya sakata juyowa dan ta ji an bude kofar ai da dan sauri dan gannin ko waye, domin mai aikinta ba mace ce mai shiru shiru ba, hasalima shegen surutu ne da ita sosai
Kofin dake hannunta na kwalba ne ya kubuce ya fadi kas, karar fashewarsa da watsuwarsa a ko'ina ya sakata binsa da kallo sannan ta sake dagowa ta zubawa fuskar Zahra ido, sannan ta juya da sauri tana harhade kwanonin du a rikice tama rasa me take yi a hade ta ce" Me ya kawo ki wajena?"
Fatima ta sake zuba mata ido, hawayen saman fuskarta wani na korar wani, a hankali ta budi bakinta dake rawa tana kallonta ta ce" Dan Allah, dan Allah ki taimakeni, ki sanar min wanene mahaifina?

Koda mahaukaci ne, koda makaho ne, ko kuturu ne, ko dan daba ne, ko barawo ne, zan so na sanshi, na ganshi, na je inda yake, ta yiwu shi ya yi min uzuri ya yafe min zuwana rayuwarsa matsayin kadarars........."
"Idan baki fitar min a falo ba na juyo na zo inda kike babu abinda ba zai faru ba da ke, ki fitar min a falo tun kafin wani ya zo ya ganki a wajen nan!" Mahaifiyarta ta fada da karfin da ya sakata sake rintse idannuwanta jikinta na kwasar rawa
Da dan karfi
adan dan ta samu kwarin gwuiwar korar tsorin dake ruhinta ta ce" Tsintata kika yi?

Waye mahaifina ?
Chapter 17 · 0% Book details